NOVELSUncategorized

SOORAJ 3

????????????????????????????????????????

             *SOORAJ*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*


             *WATTPAD*
       @fatymasardauna

       
           *CHAPTER 3*


Tunda yafita baidawo gidannasa ba har sai ƙarfe goma da rabi na dare, saida yagama daidaita tsayuwar motar tasa, kafun ya cire sit velt ɗin  dake saƙale ajikinsa,    aƙalla yakusan 7 minute acikin motar baifito ba, ahankali ya zuro ƙafafunsa waje cike da isa irin nasa, dama shi gwanine wajen jin kai da kuma miskilanci, baka gane gabansa baka gane bayansa. Sam yamanta da cewa wai yau aka ɗaura masa aure, saboda haka baiyi tunani ko tsammanin samun wata halitta acikin gidan nasa ba, kamar koda yaushe idan yashiga falon gidan direct bedroom ɗinsa yake wucewa, yauma hakance takasance.   Wanka yasoma yi kafun yadawo yayiwa kansa mazauni akan gado, laptop ɗinsa yajawo yasoma latsawa,  long jeans ne ajikinsa sai kuma wata farar riga wacce aka jere aninaye agabanta, saidai bai maƙala  aninayen duka ba, hakan yasanya faffaɗan ƙirjinsa bayyana, kusan koda yaushe irin wannan shigar shine shigansa, duk da kasancewarsa farin mutum amma kuma yanason kalan fari, shiyasa yawancin kayansa suka kasance farare, duk da cewa idanu da nutsuwarsa suna ga abun dayakeyi acikin laptop ɗinsa, amma hakan baihanasa jiyo motsi  a ɗakin dake kusa danasa ba, mamakine yakamasa don baiyi tunanin akwai wani agidan bayan shiba, sai alokacin auren da aka ɗaura nasa yau ya faɗo masa, jiyayi gabansa yafaɗi, yayinda bugun zuciyarsa ta tsananta, da sauri yakawar da ruɗun dayake ƙoƙarin shiga, tare da miƙewa tsaye, ƙirjinsa na bugawa haka yafice daga cikin ɗakin nasa. 

7 minute yaɗauka yana tsaye yayinda yaɗaura hanunsa akan handle ɗin ƙofar, kokonto yake akan shigarsa cikin ɗakin, ganin baida wata mafita da ta wuce ya shiga yasanya yaturo ƙofar ahankali bakinsa ɗauke da sallama. 

Daidai lokacin wata matashiyar budurwa da bazata wuce 21 years ba tafito daga bathroom jikinta duk ruwa da’alama wanka tayi, idanunsu ne yasauƙa acikin na juna, da sauri ya ɗauke kansa daga kallonta, itama akunyace tayi ƙasa da kanta, durƙusawa tayi har ƙasa cikin sanyin murya tace “Ina wuni” shiru yaɗanyi nawasu sakanni kamar bazai amsa mata ba.    “Lafiya” yafaɗa ataƙaice haɗe da juyawa yafice daga cikin ɗakin,   bayansa tabi da kallo tare da lumshe idanunta, wani irin sanyi taji na ratsata, ahankali tace.     “Lallai samun cikakken Namiji mai kyau da aji kamar ka Sooraj babban sa’ane ga kowacce ƴa mace”

Yana fita daga cikin ɗakinnata yaji kansa dake tsananin yi masa ciwo, yayi masa nauyi.  haka yaji gaba ɗaya duniyar na juya masa, ƙirjinsa ne keta luguden duka,  da ƙyar ya iya dafe kansa yakoma ɗakinsa, faɗawa kan gado yayi tare da rumtse idanunsa, shikaɗai yasan abunda yakeji, Ƙunci, Raɗaɗi, sune suka mamaye zuciyarsa, haƙoransa yasanya ya datse laɓɓansa, acikin zuciyarsa yaketa karanto addu’o’i’n samun nutsuwa,,   ahankali kuwa yaji nutsuwa tasoma sauƙar masa,  yayinda yaji ransa nayi masa sanyi, bai tsagaita dayin addu’anba har  bacci ɓarawo ya ɗaukesa.

Ɓangaren amarya kuwa kwalliya ta tsantsara tanajiran dawowan ango, saidai kuma ko motsinsa bata sakejiba, shiru shiru har 12 hakan yasa ta rakuɓe jikinta ajikin gado tasoma kuka, tun tana kukan har bacci itama ya saceta.


*** Kamar koda yaushe kuma kamar kowacce rana, ƙiran sallan asuban fari akan kunnuwanta, duk da cewa bacci bai isheta ba amma kuma tashi yazame mata dole, kodan aikin gida dake kanta, tashi tayi daga kan ƴar tabarmar da take kwana akai ta zauna, hanunta takai kan wuyanta tashiga sosawa, daren jiya saurayene sukayi lugude ajikinta, suncijeta son ransu, dama ɗakinnata bawani wadataccen rufi yake dashi ba, gashi ko ƙofa babu, labulene kawai da aka sakaya ajikin ƙofar, ako wani dare sauro cizonta suke sosai, tun bata saba da cizon nasuba harta saba, kuma sosai cizon dasukeyi mata ke illatata, saboda kusan kullum fama take da zazzaɓi da kuma ciwon kai, amma dayake bata da wani gata haka take yawo cikin ciwo, saidai idan wahala tayi wahala tasamu ruwa akofi ta tofa Fatiha ƙafa uku tasha, da yardan Allah shike yaye mata ciwon kai.

Ruwa ta samu tayi alwala haɗe da kabbara salla tana idarwa kuwa ta ɗauki tulu tawuce rafin da suke ebo ruwa. Sanyi ake busawa sosai amma haka take tafiya babu ko mayafin kirki ajikinta, tunda tafito daga gida harta isa rafi bata haɗu da kowa ba, kowa nagida yana bacci banda ita wahalalliya marar gata. Zama tayi agaban wawakeken kogin haɗe da ƙurawa ruwan dake gudana acikin kogin idanu, wasu hawayene masu ɗumi suka gangaro daga cikin idanunta. akullum kuma ako da yaushe, addu’a take Allah yakawo mata ɗauki,   tana buƙatar farinciki acikin rayuwarta,  Kwantar da kanta tayi akan guiwowinta, hawaye nacigaba da tsiyaya daga cikin idanunta.   Tajima sosai tana zubda ƙwalla kafun daga bisani ta  ɗauki ruwan da ta iba tabar wajen, lokacin har gari yasomayin haske.    Gaba ɗaya ayyukan gidan ita tayisu tundaga kan shara da wanke wanke harzuwa ɗumamen tuwo, tana tsugune agaban murhu tana ta kiciniyar iza wutan murhu,  Inna Ma’u tafito daga ɗaki hanunta ɗauke da tulin kayan wanki,   watsawa Ziyada kayan tayi, ayatsine tace.

 “Nanda mintuna 20 nakeson nagansu awanke”

Idan da sabo Ziyada ta saba da wannan wahalan, saboda haka bataji komaiba taɗauki kayan tasomawa wankewa.

***  

Yafi mintuna 20 yana juya biron dake riƙe ahanunsa, gabansa kuwa wata ƴar ƙaramar farar takarda ne aje,  so yake ya rubuta abun da shine mafita agaresa amma kuma yana fargaban abun da zaije yadawo,  maganganun Mahaifiyarsa ne suka shiga yi masa yawon acikin kunnuwansa, inda take cewa…..  “Wallahi kaji na rantse ma awannan karon kasaki matar da muka aurama, ranka saiyayi mummunan ɓaci, zakuma kaga fushinmu irin wanda baka taɓa gani ba!”  
Tun ɗazu kalamannata keyawo acikin kansa, lumshe idanunsa da suka soma sauya kala daga farare zuwa jajaye yayi, tare da sanya haƙoransa ya datse lips ɗinsa,    tsikar jikinsa ne yasoma tashi yayinda gashin jikinsa suka soma mimmiƙewa tsaye, jiyayi kansa yasoma juyawa, yayinda  tunanin wasu abubuwa ke son hautsina masa ƙwaƙwlwa, da sauri yaɗaura alƙalami akan farar yakardan yasoma rubutu, bawani rubutu mai tsayi yayi ajikin takardan ba, ya nannaɗeta tare da sanya ta acikin wani envelop. 
Tashi yayi daga zaunen dayake yashige cikin bathroom. Wanka yayi kana yafito sanye da rigan wanka ajikinsa.   

Kayan training ɗinsa da sukeyi masa matuƙar kyau yasanya, tare da ɗaukan wata ƴar doguwar jaka,  ɗaukan takardan dayayi rubutu acikinta ɗazu yayi haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin.

Yana murɗa ƙofar ɗakin ta buɗe hakan yasa ya kutsa kansa ciki. 

Tanaganinsa tatashi zaune daga kwancen da take, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke idanunsa akanta,  a kuma wannan kallon dayayi matane ya gane cewa taci kuka ta ƙoshi.

Cikin takunsa na isa yaƙaraso har wajen da take zaune. 

Miƙa mata takardan hanunnasa yayi batare dayace da ita komai ba.   
Karɓan takardan tayi tana mai kafesa da idanunta,   juyawa yayi yanufi hanyar fita daga ɗakin, har yakai bakin ƙofa saikuma ya tsaya cak, murya ashaƙe yace.

 “Kada kiga laifina, haka tawa ƙaddaran take” 
yana gama faɗin haka yafice daga ɗakin, ko waiwayowa gareta baiyiba.

Kallon mamaki tabisa dashi 
“Kenan miye maganganunsa suke nufi?”   tatambayi kanta tambayar da babu amsa.   Buɗe envelop ɗin daya bata tayi tare da zaro ƴar ƙaramar takardan dake ciki.

Wani irin bugawa zuciyarta tayi yayinda gaba ɗaya jikinta yaɗauki rawa,  sake waro idanunta tayi tana karanta abun dake rubuce ajikin takardan.  Kukane yaƙwace mata, lokaci guda ta shiga Jijjiga kanta, azabure tatashi daga kan gadon tafice daga cikin ɗakin.

Tana ƙarasawa compound ɗin gidan shikuma motarsa na ƙarisa ficewa daga cikin gidan.  Wani irin ƙara tasaka haɗe da zubewa aƙasa tashiga rera kuka, ganin kukan bazai mata maganin komaiba yasa ta koma cikin gida, mayafinta kawai taɗauka saikuma envelop ɗin dake riƙe ahanunta.
  
Tazo fita daga gidan maigadi yatsareta da tambayar lafiya take kuka.  Ko kallonsa batayiba tafice tana ƙara volume ɗin kukanta..

Shikuwa Tanimu mai gadi komawa yayi kan benci ya zauna, aransa kuwa yana tsananin mamakin hali irin na SOORAJ, ko tantama bayayi abun da yafaru da sauran matanne itama yafaru da ita,  shiyasa tatafi tana kuka… 


Yana tsaye agaban madubi, wani ɗan madaidaicin towel ne riƙe ahanunsa, yana goge gumin dake tsastsafowa ta goshinsa, kasancewar yanzu gama training ɗinsa.   

Wayarsace  tasoma ƙara alaman shigowan ƙira,    saida yaji gabansa yafaɗi alokacin dayaga sunan dake yawo akan screen ɗin wayartasa, maganganun Ummu ne suka shiga dawowa kunnuwansa filla filla.   Jiki a sanyaye ya ɗauki wayar tasa ya kara akan kunnensa.

Ko sallaman da Sooraj ɗin keyi masa bai amsa ba, cike da ɓacin rai yasoma cewa…..   ” Yau katabbatarmin da cewa kacika ishashshe Sooraj, yau kuma kaƙara tabbatar min da cewa kai mutumin banza ne, wanda baida tunani, ashe har abada bazaka daina kunyatamu ba? shikenan kaci gaba duniyace, ita kuma yarinyar da kayiwa saki har uku kasani wallahi Allah bazai barkaba, sai ya saka mata, Shashasha kawai!!!”  

Jikin Sooraj ne yaɗauki rawa cikin inda inda yace “Dan Allah Abba ka sau…..” 

“Bazan taɓa sauraranka ba Sooraj, wallahi ko ganinka banasonyi,  gargaɗi na ƙarshe kada kasake ka zomin gida, tunda haka kazaɓa kaci gaba, mukam munzare hannuwan mu daga cikin al’amuranka!!!”

Abba yafaɗa murya a kausashe.

Baibawa Sooraj damar sake cewa komaiba yakatse wayar. 

Zamewa Sooraj yayi daga tsayen da yake yazauna daɓas, hannayensa duka yasanya ya tallafi kansa, idanunsa ne suka kaɗa sukai jajur, take jijiyoyin dake kwance akan goshinsa suka fito raɗa raɗa,  saurin rumtse idanunsa yayi, domin idan yace zai barsu a buɗe, to tabbas ruwan hawayene zasu fito daga cikinsu…


*ZIYADA*

Tun safe take ta faman jibgan aiki kamar wata jaka, har zuwa yanzu kuwa bata huta ba. Shigowarta gidan kenan tasamu Inna’ Ma’u tsaye sai rangaɗa guɗa take, hanunta riƙe da kuɗaɗe masu yawa, gefenta kuwa Malam Garba ne zaune yayi jigum, shidai baida tacewa, komai Inna Ma’u ne keyi, tamaidashi kamar wani yaronta, shikuwa biyayya yakeyi mata kamar raƙumi da akala duk hanyar da ta jasa nan yake bi.  

Harara Inna Ma’u ta aikawa Ziyada da ta tsaya tana kallonta.

“Mayyar banza miye kika tsaya kina kallona?” 

Da sauri Ziyada tayi ƙasa da kanta,  sumu sumu ta wuce cikin ɗakinta, hakanan taji gabanta na faɗuwa, jitake ajikinta kamar wani babban al’amari na kusantota, wanda kuma da dukkan alama ba abubane mai daɗi.     


        *15/March/2020*


*✔️OTE ME ON WATTPAD*
         @fatymasardauna


#Love
#Romance

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button