NOVELSUncategorized

SOOTAJ 2

????????????????????????????????????????

              *SOORAJ*


   *Written By*
Phatymasardauna


*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation* 

             *WATTPAD*
       @fatymasardauna


         *CHAPTER 2*

Agaban wani tankamemen gate yayi parking motarsa, fitowa yayi daga cikin motar ya nufi ƴar ƙaraman ƙofar dake jikin gate ɗin, ahankali yatura ƙofar yashiga, Manu mai gadi naganinsa ya kwaso aguje cike da girmamawa yace.
 “Ranka ya daɗe barka da zuwa, Ango, Ango kasha ƙamshi….”  

Kallon da yayiwa Manu mai gadine yasa yaja bakinsa yayi shiru, batare daya ƙarasa maganar dayakeyi ba. 

Direct wani dogon gini dake tsakiyan compound ɗin gidan yanufa. 

Wata ƴar dattijuwar mata ce ke zaune acikin katafaren falon, kayane zube agabanta tare da wasu manyan akwatuna masu kyau da tsada. 
 Da sallama ɗauke abakinsa yashigo cikin falon, amsa masa sallaman matar tayi fuskarta babu yabo ba fallasa. Baidamu da yanayin yanda yaga fuskarta ba, don yasan dalilin daya sanya tayi kicin kicin da fuska damace batason bashi, kuma amma duk da haka baijin zaiƙi furta abundake cikin ranshi.

“Barka da gida Ummu” 
Sooraj yafaɗi haka bayan yayiwa kansa mazauni akan lallausan  carpet ɗin da ya mamaye ƙasan falon. 

“Yauwa sannu” Ummu tafaɗa tana mai ƙoƙarin tattare kayan dake gabanta.  Shirune yashiga tsakaninsu, dama shi haka yake idan yayi magana saiyaja wasu mintuna baisake cewa wani abu ba, bakuma don baida abun cewa ba, a’a haka ya sabarwa kansa.  Ummu kuwa afakaice ta ɗan saci kallonsa, yanda taga fuskarsa ya tabbatar mata da cewa akwai magana abakinsa, itakuwa bazata so taji komai daga bakinsa ba.   Miƙewa tayi daga zaunen da take, wayarta taɗauka kana ta nufi hanyar da zai sadata da ɗakinta.

Ganin da yayi cewa idan yabari tatafi yarasa damansa ne,  yasanyashi   gyara zama haɗe da cewa.  “Ummu dama inaso….” 

“Banason kacemin komai, ya isa haka, munriga da mungaji da halinka SOORAJ, wallahi kaji na rantsema awannan karon kasaki matar da muka aura ma, ranka saiyayi mummunan ɓaci, zakuma kaga fushinmu irin wanda baka taɓa gani ba!” Ummu takatseshi ta hanyar faɗan haka cikin ɓacin rai. 

Jajayen idanunsa yaɗago ya watsawa Ummun, itakuwa ko waiwayosa batayiba ta wuce ɗakinta.

Wani irin tsannin baƙinciki ne yasake kawo masa ziyara, babban abun takaicin shine yanda akaƙi basa dama,  jiyayi kansa na sarawa kamar zai rabe gida biyu,  tashi yayi ya fice daga cikin falon,  ko iya kallon gabansa bayayi haka yakoma motarsa, kafa kansa yayi ajikin steering motar, yana fidda numfashi mai zafi,    “Wannan wace irin rayuwace yakeyi? sai yaushene zai samu sauƙi daga raɗaɗin da yakeji?”  tambayar dayaketa yiwa kansa kenan acikin zuciyarsa.  Ya kusan mintuna 10 a wajen, kafun ya iya tada motarsa yabar unguwartasu gaba ɗaya, kaitsaye gidansa ya nufa.    

Koda ya isa bedroom ɗinsa kayan dake jikinsa ya cire tare da shigewa cikin bathroom,  wanka yayi tare da ɗauro alwala kana yafito,  dogon wando na jeans yasanya tare da wata farar T-shirt, kallon agogo yayi yaga da sauran time kafun aƙira sallan Azahar,   kwanciya yayi akan makeken gadonsa tare da lumshe gajiyayyun idanunsa…..

*** 
Idan hankalin Ziyada yayi dubu to atashe yake,  domin kuwa tana zuwa injin niƙan tasamu ba’a niƙawa Inna Ma’u niƙan garin kunun tsamiyanta na gobe ba,  hawayene suka cika idanunta, yayinda tashiga haɗa mai injin da Allah akan yaniƙa mata sauri take, da ƙyardai tasamu ya yarda ya niƙa mata.   Tunda ta shawo kwanan ƙofar gidannasu take  hango wata yagalgalalliyar mota, wanda taji tsufa harta gode Allah,  cikin yanayinta na sanyi taƙaraso ƙofar gidannasu. 

Wani dattijone wanda aƙalla shekarunsa zasukai 60 tsaye ajikin wata ragwaɓaɓɓiyar mota dagani motar taci wahala, mutumin irin baƙaƙen tsofinnan ne, sannan kuma ko wani gashi najikinsa yatashi daga baƙi yakoma fari,  kai tsaye zaku iya ƙiransa da tsohon najadu, domin daganin idanunsa zakasan cewa baƙaramin ɗan duniya bane, yanayin yanda yake kallon Ziyada kamar wani tsohon maye ne yasanya tayi ƙasa da kanta,  tashige cikin gida,  Murmushi Tsohon  yayi haɗe da jijjiga kansa, wani irin daɗi yaji aransa alokacin dayaga Ziyada’n.


“La’anatu sai yanzu kikaga daman dawowa? halin asaran dai shine bazaki fasa ba?” Inna Ma’u ta tambayeta.

“Kiyi haƙuri Inna Ma’u, wallahi ba ayi miki niƙan da wuri bane, shine kuma…..”

“Da Allah rufemin baki shine kuma me? waye baisan  fetsarancinki ba, shashasha kawai, yanzu da kika ebo ƙafa kika shigo cikin gida, shin bakiga  Tsoho ɗan dashe  natsaye a waje yana jiranki bane?”

Wani irin bugawa ƙirjin Ziyada yakumayi, a tsorace tace 
   “Tsoho ɗan dashe kuma?”

“Ƙwarai kuwa, zakije kisamesane ko kuwa saina ɓaɓɓallaki yanzu anan wajen!” Inna Ma’u tafaɗi haka a hasale. 

Jikin Ziyada ne yasoma ɓari amma bata da wani zaɓi daya wuce zuwa tasamu tsohon najadun dake tsaye a waje yana zaman jiranta. 

Tana fitowa daga gida Tsoho ɗan dashe yasaki dariya irinta tsofaffin ƴan duniya.  Kallonsa yamayar kan ƙirjinta, saida ya haɗiyi wani yawu,    “Ƙaraso mana Amaryata” yafaɗa yana washe wawagegen bakinsa.   

Kallon tsananin tsana Ziyada tabisa dashi haɗe da soma ƙare masa kallo,  idanunta ta sauƙe akan jajayen haƙoransa dayaketa washewa, gaba ɗaya bakinsa cike yake da tsakin goro, komai nasa dagajaja ba kyaun gani, duk da itama acikin dauɗa da ƙazanta take, sannan kuma bata da wani suturun kirki, amma duk da hakan ƙazancin Tsoho ɗan dashe daban take dana kowa, duk garin babu wanda baisan wanene Tsoho ɗan dashe ba, tsohone da bai riƙe mutumcin kansa ba, bashida wani aiki sai lalata yaran jama’a, matansa huɗu, kuma acikin garinnasu sosai akeji dashi, kasancewar yana da shanaye dakuma dabbobi, saboda tsabar duniyanci irin nasa har mota yake dashi, irin ko ohon motocinnan, nanma ƙaryan raine kawai irin nasa, ko iya tuƙata baiyiba, akwai wani ɗan ƙullinsa Ɗan liti shike tuƙasa yakaisa duk inda zashi, yanzuma tare suke.

Saida tagama ƙare masa kallo kafun ta kawar dakanta gefe, wani sabon tsanarsa taji acikin ranta,  ganin da yayi cewa yarinyar nada taurin kai bazata ƙaraso garesaba yasanyasa soma takowa zuwa inda take, da sauri taja da baya.    

“Wai Amaryata badai tsorona kikeji ba? ai gwamma kisaki jikinki dani domin ina tabbatar miki da cewa mako mai zuwa za’a ɗaura mana aure dake” Tsoho ɗan dashe yafaɗi haka yana mai sake washe ƙaton bakinsa.

Jin ya ambaci kalmar aure yasanya taƙara ja da baya, ganin da tayi kamar baya cikin hayyacinsa ne yasanya ta juya ta koma gida yana ƙiranta amma ko waiwayosa batayiba, ashe Inna Ma’u na laɓe tanajinsu, Ziyada nashigowa cikin gida Inna Ma’u ta ɗauketa da wani irin faskareren mari, cike da takaici tace.   “Amma kedai anyi yarinyar banza, ke inbanda hauka har Tsoho ɗan dashe zaizo miki da maganan aure kinemi wulaƙantasa, to kijini da kyau, ninan nabada aurenki ga Ɗan dashe, ko kinaso ko bakyaso, munafuka kawai, mai baƙar zuciya da aniya!” 

Kai Ziyada tashiga jijjigawa lokaci guda kuka ya ƙwace mata, durƙushewa tayi aƙasa haɗe da kama ƙafan Inna Ma’u cikin muryan kuka tace.  

 “Dan Allah Inna Ma’u kimin rai, karki haɗani da Tsoho ɗan dashe, kowa dake garinnan yasan halinsa ɗan iska ne, kuma ba tsohon kirki bane dan Allah kiyi haƙuri !!”

Ƙafa Inna Ma’u tasanya ta shure Ziyada cike da tsanarta tace “Idan kinga baki auri Ɗan dashe ba to saidai in mutuwa kikayi, ke ko mutuwa kikayi sai ankai masa gawarki” tanafaɗin haka tazari mayafinta da koyaushe ke akan igiya ta fita zuwa waje. 

Kuka Ziyada tasanya haɗe da tashi ta nufi ɗan ƙaramin ɗakinta.  Zama tayi akan tabarma tare da cusa kanta tsakankanun cinyoyinta kuka tashiga rerawa mai taɓa zuciya, tasan tunda Inna Ma’u tafaɗi haka to sai ta aikata. 

Inna Ma’u kuwa koda taje tasamu  tsoho ɗan dashe sosai suka tattauna akan Ziyada, inda yatada hankalinsa akan cewa shi lallai bayason aja lokacin auren, idan da ta sonsa ne ma shi koda yau abasa ita, idan yaso daga baya sai a ɗaura auren sosai yarinyar tashiga ransa, musamman daya lura cewa komai nata ɗanyene shakaf, da’alama zai kwashi garaɓasa mai romo,  kuɗi sosai ya dumbulawa Inna Ma’u ita kuwa sai washe baki take da haka sukayi sallama.. 

Saida tayi kuka mai isarta kafun ta fito daga cikin ɗakin takama aikace aikacenta daya zame mata  dole.   

Sallaman Babanta da tajine yasanya taji gabanta ya tsananta bugawa,  muryarta na rawa ta amsa sallaman nasa.

“Baba Sannu da dawowa!” tafaɗa murya a sanyaye.

“Daban dawoba ai da bazaki ganni ba!”  Fari kyakkyawan dattijon da taƙira da sunan Baba yafaɗi haka ahasale. 

Cikin sanyi ta sunkuyar da kanta ƙasa, wannan halin shi kullum Babanta ke nuna mata, tun tana ƙarama harkawo yanzu bata taɓa sanin ya soyayyar mahaifi yake ba, babanta ko kusa dashi bayaso tazo, tsanar dayake nuna mata haryafi wanda Inna Ma’u ke nuna mata, cigaba tayi da aikinta, shikuma kai tsaye ya wuce ɗakin Inna Ma’u jikinsa na rawa, gudun kada ta leƙo ta fara zazzaga masa masifa, don kamar yaron cikinta haka tamaida shi.

*** 
Bayan yadawo daga sallan Azahar bacci mai nauyine ya ɗaukesa, kusan awa uku ya share yana bacci, kasancewar yau weekend babu aiki.  Ahankali yake buɗe kyawawan idanunsa masu ɗauke da zara zaran gashi asamansu (Eye lashes)   akan agogon dake saƙale jikin bangon ɗakin ya sauƙe idanunsa.  3:00 pm daidai yagani, cikin nutsuwa ya zuro ƙafafunsa ƙasa daga kan gadon,   bathroom yashiga yakumayin wanka tare da ɗauro alwala.

Tsab yagama shirya kansa cikin riga da wando na jeans masu kyaun gaske,  ya feshe jikinsa da turarukansa masu ƙamshi da kama jiki, combat shoe yasanya aƙafarsa haɗe da ɗaura agogon Apple a hanunsa na dama, sosai yayi kyau,  ɗago kyawawan idanunsa yayi ya kalli kansa acikin madubi, shikansa yasan cewa shi cikakken kyakkyawan Namiji  ne mai aji dakuma ɗaukar hankali, amma kuma saidai yana da tarin matsaloli.   SOORAJ  namijine kyakkyawa, komai nasa abun burgewa ne,  Yana da cikar halitta sosai, jikinsa amurɗe yake kasancewarsa ma’abocin yin gym,  farine shi tas banda lallausan sajen dake kwance akan ƙuncinsa babu wani abu dayake ɓaƙi ajikinsa. Yana da wasu irin idanuwa  ƴan madaidaita masu kyaun gaske, kamar yanda gashin idanunsa suke zara-zara haka gashin giransa ma suke, yana da dogon hanci, dakuma ɗan ƙaramin baki mai ɗauke da pink colour lips.      

 Ya ɗauki sama da 3 minute yana ƙarewa kyakkyawan fuska da jikinsa kallo,  ahankali ya  sauƙe idanunsa ƙasa cike da raunin zuciya,   yasani ahaka idan kowa ya kallesa zaiyi masa kallon Cikakken Namiji Mai lafiya da kuma jin daɗi, amma shiyafi kowa sanin kansa yana da RAUNI sosai.       Wayarsa ƙirar Galaxy S20 ne tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, ko kallon wayan baiyiba yasakai yafice daga cikin ɗakin, yayarda da abun da zuciyarsa tagama yanke masa, bazai bari awannan karon yasake faɗawa cikin irin halin daya faɗa abaya ba, ɗaukar ƙaddara yazame masa dole, don hakane ya yankewa kansa hukuncin nesantar duk wata ƴa mace, mahaifiyarsa ce  kawai bazai iya nesanta kansa da’ita ba, amma sauran mata kam hakan yazame masa dole, kodan rufewar sirrinsa.

*** 

“Nagama yanke shawara Aure zamuyiwa Ziyada”   Inna Ma’u tafaɗi haka ga Malam Garba bayan takai loman tuwo bakinta.

Malam Garba dake zaune akan ƴar tabarma ya ɗago kansa ya kalleta, cikin murya mai sanyi, yace…   “Aure kuma Ma’u?”

“Ƙwarai kuwa Aure, ko so kake muzaba mata idanu tacigaba da yawon bin maza? to idan kuwa haka kakeso wallahi saina cire hanuna akan lamuranku!” Inna Ma’u tafaɗi haka cikin ɓacin rai.

“A’a bawai nace bazatayi aure bane Ma’u, duk hukuncin da kika yanke akan Ziyada aini bazance a’a ba, amma kinsan banda kuɗin aurenta a yanzu!”  ya ƙare maganar cike da tsoron Inna Ma’un.

“Kai dai kawai kazubamin ido, domin nariga dana gama yanke shawara, gobe   Tsoho ɗan dashe yace zai kawo kuɗin aurenta, kuma kadai san yanda tsoho ɗan dashe yake, idan yace zai auri yarinya, to baya buƙatar komai daga wajen iyayenta, hakanan zamu kaita mu wurgar “

Da sauri Malam Garba yasake ɗagowa ya kalli Inna Ma’u bakinsa na rawa yace 
 “Tsoho ɗan dashe kuma? ɗansa zaki aurawa Ziyada’n?” 

Harara Inna Ma’u ta watsa masa cike da takaici tace  “Atunaninka akwai wani matashin saurayin da zai jajiɓawa kansa wannan maƴyar ƴartaka? Ɗan dashe ne ke nemanta kuma nariga dana basa, ko kana da maganane?”

Kansa yagirgiza alamar “A’a” amma kuma har acikin zuciyarsa baiji daɗin hakan ba,  kowa yasan Tsoho ɗan dashe ba mutumin kirki bane, tsohon banzane dabai riƙe mutumcin kansa ba, sannan kuma sam baisan darajan aure ba, ya auri mata sama da 15, daya auri mace tana samun ciki, zai koreta tare da takardan sakinta.  To amma mai zaice, shi awajensa komai Inna Ma’u tayi dai dai ne…

*(A wannan littafin zan buga muku wasa mai zafi, kudai kucigaba da bina, sannan kada ku manta comment ɗinku shizai ƙaramin ƙarfin guiwa)*


          *14/March/2020*
    


*✅OTE ME ON WATTPAD*
         @fatymasardauna

#Love
#Romance…..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button