NOVELSUncategorized

RAGGON MIJI 1-5

RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
 *~We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

1
*In the name of Allah the most beneficent the most merciful*
Alhamdulillah ina rokon Allah yabani damar rubuta dede yadda nafara lpy Allah yabani ikon gamawa lpy amin.
Sadaukarwa ga *sis zulaihat rano* alherin Allah ya sameki a duk inda kike, kisani inayinki bazan manta alherin da kikamin ba ina godiya da kulawa
faseelat yarinya ce and she’s not above 21yrs tana da kyau sosai babban jiki ne daita fara ce sosai fuskarta is ready made ko ba tai kwalliya ba batada matsala abinda yafi daukar hankali ajikinta shine kugunta tanada babban kugu da big breast kusan ma sune suka sa ta kiban amma kibar ta me kyau ce saboda bata da tumbi bata da fadi, faseelat kyakkyawa ce de sosai,
Gidansu matsakaita ne ba masu karfi bane kuma ba matalauta ba, mamansu ita kadaice awajen babansu su 5 ne mamansu ta haifa faseelat itace ta biyu kuma ita kadaice mace ta taso cikin gayu tun tana yarinya har girmanta mamanta cikin gyaranta take dayake ita kadai ce mace, yayanta sunanshi omer, se ita se abulkhair se ishak se auta Mubarak,
Babansu meson karatu ne sam be wasa da ilimi ta sauke kur’ani kuma tagama secondry sede mamansu taki yarda tawuce makaranta, wai sanadin lalacewar yawancin yanmata kenan, babanta alhaji maaruf yayi iyakar yinshi amma ummi taki wai sede tabari setayi aure tayi,
Yanzu haka faseelat bata zuwa koina se islamiya shima se weekend duk aikin gidansu itace keyi batada hutu ko kadan, ta kware wurin sanwa sannan kwararra ce wurin gyaran jiki saboda abinda mamanta ke koya mata ne, kullum ummi kamar yar 30yrs take saboda bata wasa da gyara kanta duk abinda ya shafi gyara ko abinci ko kwalliya wannan yasa abbansu yakasa yi mata kishiya dan ko kallon mace bayayi dan yasan inyaje gida tashi tafita.
Har mazan gidan suma basa yawace yawace unlike other houses da namiji se ma ya kwana ba gida ba, su ko duk abunka karfe 10pm acikin gida takemasu.
Faseelat ba mummuna bace bare ace shiyasa batada saurayi kawai Allah ne be kawo ba har yau ba wanda ya taba tunkararta da kalmar so, wannan yana matukar damun umminta saboda ita burinta ta ganta adakin aurenta lami lpya kuma shine gurin kowace uwa akan yarta, shi ko abba be damu ba cewa yayi komi lokaci ne,
itama faseelat abun baya damunta amma tanada buri a soyayya yadda take fara fari takeso, tanada kiba to mijinta ya zama siriri dogo, tana masifar son saje a fuskar namiji, yazama dole mijinta ya zama jarumi me karfin zuciya kuma sannan ya zama yana da rufun asiri da ilimi to shine mijin aurenta kuma shine burinta,
So da dama takan zauna da mamanta su tattauna akan aurenta itade faseelat abun mamaki yake bata gani takeyi mamanta bata yarda da tarbiyyar da ta bata ba ,ko tagaji da ganinta kusa daita,
Yau sungama cin abincin rana itada ummi saboda tare suke cin abinci, ummi ta kalleta tace “faseelat Allah yabaki miji nagari ki tafiyarki ki huta kullum addua ta kenan ba dare ba rana “
faseelat batasan lokacin da hawaye suka zubo mata ba,
Tasa bayan hannunta ta goge ummi na ta kallonta da mamaki,
Faseelat tace “ummi shin akwai ranar da zata zo ta koma baki maganar aure na ba? shin ummi kingaji da nine? Koko nikadaice wadda takai wadannan shekarun a gidan iyayenta,? Ummi tunbana sa komi a raina har nafara zargin ko de baki yarda dani bane? “
Kallon mamaki kawai ummi kebinta dashi tace “haba faseelat burin kowace uwa taga yarta gidan miji nasanki kaf ciki da waje nice mahaifiyarki ni na haifeki nasan halinki bawai inafada bane dan ranki ya baci abinda ke gabana kenan banda Mace se ke duk kanku ina alfahari daku kuma kullum ana yabon yara na dan haka kidena zubar da hawaye kinji diyata? “
tajawo ta akan kafarta hawaye faseelat ta share, ita fa bacin feeling da takeji ai bataki tayita zama gidan suba, to shaawa tayi mata yawa so da dama tana yawan mafarki, kuma dakinta ba toilet aciki tsakanin dakinta dana ummi toilet yake se can farkon shigowa gidan nan dakunansu  ya omer suke suma da toilet tsakiya shi ko abba ciki da falo da toilet ne yakeda, tun asuba take lallabawa tayi wanka inde tayi mafarkin sam batasan ummi tasani ba ,shine ma yasa take kara son aurar daita dan itama ummi haka take da yawan shaawa ,bare faseelat ga girman jiki tunda ko mata suka ganta sede suce tubarkalla dan duk yaddda tayi tafiya kugunta da breast dinta rawa suke .
Ummi ta saki ajiyar zuciya tace “Allah yamaki albarka faseelat duk aikace aikacen gidannan ke kadai keyi kinhanani komi ni har tausayi kike bani “
Abulkhair ne ya shigo agajiye yadawo daga school yana shigowa yaji yadda ummi kesawa faseelat albarka,
Ya zauna tareda fadin “wlh ummi bamu yadda ba kullum faseelat kadai kike sawa albarka muko baruwanki damu, Allah ina tunanin rabon daki samin albarka tun kan ki yayeni “
da faseelat da ummi suka fashe da dariya
ummi tace “abul inayimuku kuma ko ban bayyana ba, kaima Allah yamaka albarka dasu gabadaya “
Yace” amin ummina, ya faseelat mi kika dafa yau? “
tace “aifa new student in university, abinda bakaso akayi danwake da souce “
Yace “nashiga ukku ni abul ummi ya zakuyi dani wlh nakusa karasawa lahira sora kiris inbaku temaka min ba idawa zanyi “
Suka babbake da dariya faseelat tace “katashi katube kashiga kitchen kawai “
Yace “pls pls ya faseelat do help me “
Tace “naki din “
Ya tabe fuska “nide dama nasan yaya bakisona ko kadan “ya mike tsaye.
Ummi dake dariya tace “itako ke sonka tayimaka rice beans se kaci da soese din”
Yasaka hannu biyu a kirji yasauke ajiyar heart huuuuum “yaya Allah yabarminke inasonki kamar rai “
ummi tace “jeka de kaci kahuta tukun “
Yajuya yatafi dasauri itako faseelat ta mike tsaye ummi tace “se ina? “
Tace “wanka zanyi ummi kafin marece infito indora muku dinner”
Ummi tace “bakigajiya da wanka faseelat to zakiga dilka saman windon toilet kidanyi kafin wankan “
Tace “Tom ummi se nafito “
[7/12, 10:57 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
2
Dedicate to *sis zulaihat rano*
A Al’adar gidansu faseelat bayan asuba sukan hadu suyi murajia, bayan isha kuma suyita fira basu cika kallace kallace ba, itada yanuwanta akwai kyakkyawar fahimta,ya omer bayanan yana Niger karatu kuma can ne asalin mahaifiyarta asiya, sun hadu da mahaifinta ne yaje kasuwanci a can kuma ya samu nasarar sace zuciyarta har akamusu aure, sukan je niger amma ummi tafi yawan zuwa,
Bayan kwana biyu
yau tun asuba faseelat ta farka a firgice tasha mafarkai kala da kala
Cikin sauri ta sa hannu ta shafo kasan pant dinta taji shi da lema, ta dafe goshi tareda fadin “oh god”
Babban tashin hankalinta sanyin da ake surarawa gashi dole tayi wanka, ta tsaya tana ta nazari can dasauri ta dira daga kan bed ta jawo towel sauri -sauri ta sabule rigar baccinta tai waje jin shiru dakin ummi tagane bata tashi ba, wuf tashige toilet ta sakarma kanta shower yayinda take cudawa da hannunta sauri kawai take kar ummi ta tashi.
Karar ruwan dake sauka ne ya tayarda ummi daga bacci ta tashi zaune ta buga tagumi tausayinta yakamata ko ita inde zatai wankannan takansa ruwan zafi, kamar tatashi tafita se kuma tafasa dan karta bata kunya,
 seda faseelat tagama wanka tafito tawuce dakinta sannan ummi tafito jikinta a mace tashiga toilet itako faseelat salla ta kabbara,
Ummi se sake sake take bazata manta yadda tasha wahala ba lokacin da take budurwa don har azumin dole takeyi,
Alwala tayi ta kabbara salla tana ta adduar Allah yakawo wa faseelat miji nagari ,bayan faseelat tagama tafito dakin ummi tashiga tazauna sannan ta gaisheta ummi ta amsa tana lazimi har ta tashi ummi takira sunanta “faseelat!”
Tace “naam ummi “
ummi tace “dawo kizauna zamuyi magana “
tace “to ” tadawo ta zauna
Ummi tagyara zama tace “faseelat ni ce mahaifiyarki ni na haifeki tambayar ki zanyi kuma inaso ki bani amsa a matsayina na mamanki, dole ne yasa zan miki maganar nan duk da tamin nauyi “
gaban faseelat harbawa ya rika yi sosai da sosai,
Ummi ta cigaba da cewa “ina kula da ke tun kina 18yrs na kula kina yawan yin wanka akai akai kuma nasan dalilin hakan ,amma inaso kifadmin da kanki miye dalili “
Hannu faseelat ta dingi dannawa yana bada sautin kas -das
Ta sunkuyar da kai, kunya duk ta cika ta,
Ummi tace “dama nasan bazaki fadamin ba amma don Allah ina rokon ki faseelat kiyi hakuri da yanayinki ki jure karki gurbata rayuwarki ki rike mutuncinki na roke ki”
Faseelat gabadaya jikinta yayi sanyi tace “ummi  banida wannan tunanin kuma namiki alkawari bazan taba zubda mutuncina ba ki cigaba da yimin addua adduar ki nake so “
Ummi tace “addua munanan munayi faseelat sede mukara akan ta”
shiru ummi tayi sadaf sadaf faseelat tabar wurin, duk ji tayi jikinta ya mutu batareda ta je wurin da suke karatu ba ta wuce daki ta kudundune,
Ummi bayan ta gama  addua tafita bayan Sun gaisa da abba tawuce kitchen taga ba faseelat, ta girgiza kai tafara aiki, tasan dama me wuyacine yau ta saki jikinta.
Suko su abba karatunsu sukayi har xuwa 7am sannan suka tashi me bacci ya kwanta me zuwa school yafara shiko abba shigewa yayi yafara shirin office.
bayan ummi tagama hada breakfast suka yi suka fice gidan yayi tsit kamar ba kowa ciki,
Ummi wanka tayi tashige daki, batareda ta waiwayi faseelat ba, itako faseelat bacci ne ya dauketa,
Can wajen 10am ummi tafara jin sallama tana fitowa taga wata kawarta a aikin hajji suka hadu matar ta girmi ummi nesa ba kusa ba amma jininsu yazo daya saboda a room daya suka zauna lokacin hajji ita kuma ummi tana matukar girmama na gaba daita, wannan yasa suka shaku da maman khalil, ko bayan Sun dawo daga saudiyya suka cigaba da zumunci.
“maraba maraba da maman khalil “
Hjy saratu tana faraa tace “yawwa Hjy asiya “
Ummi tace “shigo ciki mama naga kintsaya waje mushiga ciki “
Maman khalil na murna suka shige ummi tanata nan nan daita takawomata pure water da zobo taajiye sanan ta zauna ,”sannu Hjy ,sannu da zuwa, yasu khalil? “
Hjy saratu tace “lpyarsu lau siyama ma na gaida faseelat”
Ummi tai faraa da cewa “ihhhhn siyama  kenan kullum tana gida kamar ba macen aure ba “
Hjy saratu tace “mijin tasamu me sauki shiyasa “
Ummi tai murmushi
Suka cigaba da fira can Hjy saratu tace “Hjy dama wata muhimmiyar magana nake tafe daita Allah yasa zansamu abinda nazo nema “
Ummi tai shiru tana saurarenta
Hjyar ta cigaba da cewa “kinsan yara na biyu kacal khalil da siyama, siyama de tayi aure gashi harda jikoki na samu, amma khalil shiru yaki ya fiddo mata gashi yanzu har yana batun Shiga shekara 35 kuma bayada niyya na mishi magana baso daya ba ba biyu ba amma shiru, to daga baya na Yanke shawarar zabar masa mata,saboda shi mata basa gabansa kwata kwata.
nayi tunanin ,na duba na hango yarki faseelat ce ta dace dashi, batun yau ba ina fadamiki yaranki na burgeni wannan yasa nakeso inhada Zuria dake, inaso yaro na yazo sugana da faseelat in sun dedeta se ayi buki.
Ummi hamdala kawai take cikin ranta Allah ya amshi adduarta,
ta danyi shiru sannan tace “……….
[7/12, 10:57 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
*Writing by MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
3
*Dedicated to SIS ZULAIHAT RANO*
Sannan tace “naji dadin wannan maganar Hjy kuma inafatan zasu fuskanci juna Allah ya tabbatar mana da abinda yafi zama alheri *
Hjy saratu tace “amin amin Insha Allah gobe zezo su gaisa daita din saboda baniso a dau lokaci”
Ummi tai murmushi “tom madalla zansamu faseelat da maganar”
Hjy saratu tace “ni tunda nashigo bangantaba nade san su Mubarak ana school”
Ummi tace” inajin bacci takeyi, bari natado miki ita “
Hjy tace “aa barta bari na tashi nawuce gida “
Ummi tace “tom nagode kigaida gida “
Suka fito ummi tayo mata rakiya suna fitowa tsakar gida sega faseelat ta fito zata shiga toilet wanka tana daure da towel ,tana ganinsu ta sunkuya ta gaida Hjy saratu dasauri tashige toilet, Hjy saratu ta bita da kallon birgewa sannan tawuce,
Ummi wasai ta nufi kitchen ita kuma faseelat tai wanka tai brush sannan tafito neman abinci, tana shiga kitchen ta tarda ummi na aiki batareda tace komiba ta debi kunun tsamin daakayi tafita shaf shaf ta shanye ta dawo tace ummi ta bata tayi aikin, ummi tace “a,a barshi zan dan tayaki se muyi tare “
Faseelat tace “a, a ummi kibari nayi “

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());

Ummi tace “to” tasamu wuri tazauna tace “miko min albasa da latas din na yanka miki “
Faseelat ta mikomata  ummi nayanka take magana, “faseelat! “
Faseelat ta juyo “naam ummi “
Ummi ta cigaba da cewa “Hjy saratu ce tazo da maganar tanason danta khalil ya aure ki shine ta zo neman izini zezo kugaisa kufahimci juna”
Faseelat tai kasak’e can zuwa tace “to ummi “
Ummi tace “gobe yana nan zuwa seki shirya sannan inaso Dan Allah badanniba ki saurareshi “
Faseelat takara cewa “to ummi “
Ummi ta cigaba da cewa “Hjy saratu mutunniyar arziki ce tun bayan dawowarmu daga saudiyya ta daukeni kamar kanwa tana sona da zuria ta baki daya, gashi hartanason hada jini dani, Allah ina rokonka kasawa abinnan albarka”
shiru faseelat tai ta cigaba da tsintar waken dake gabanta.
itama Hjy saratu tana komawa gida tafadawa mijinta yanda Sukai yace Allah yasa haka shine mafi alheri .
se 2pm khalil yashigo gidan dakin Hjyar ya wuce yafada kan kujera “I’m very tired hjy “
Ta harareshi “se kace wanda yayi dako “
yace “Allah Hjy barci ne a idona sosai bari na tashi naje naci abinci na kwanta “
Har ya mike Hjy saratu tace “kai dawo kazauna”
Yace “to “yaxauna yana jiran mi zatace
“dazunnan naje munyi magana da wata kawata zakaje kaga diyarta intamaka shikenan, tunda kai kakasa fiddowa da kanka gwara ni na zabarma, kashirya gobe kaje kaganta inka tashi kamin magana zanbaka address inafatan kagane? “
Tunda tafara magana yake kallonta “amma Hjy kinaganin ba matsala ni da kinkara min lokaci banfa isa aure ba gaskiya “
Hjy ta watsa mashi harara “tashi kaban wuri “
Ya tashi har ya kai kofa ya juyo “amma Hjy kinaganin ita yarinyar zata amince? “
Hjy saratu takara watsa masa harara
Abinda yasashi juyawa kenan ya fita dakin yanajin duk ta takura masa aishi be tashi aure ba gaskiya shi ko kallon mata bayayi bare soyayya,kusanma tsoron matan yake ranar kwana yayi beyi bacci ba ya nata saka da warwara Karon farko da ze tunkari mace me zece mata?  Mi zasu tattauna shine tunaninshi kawai.
Itama faseelat batai bacci ba will he be like her dream guy? gaskiya bazata taba yin aure ba harse tasamu muradin ta idan ya mata fine inbe mata ba bazata aureshi ba ko,
Haka ta kwana sake sake,
Washe gari
Bayan tagama aikace aikacenta na yau da kullum sannan ta shirya tasa ka riga da sket ta yafa gyalenta ta zauna jiran tsammani dan ummi sunyi waya da hjyar tace karfe 11 zezo,
agogo ta kalla taga karfe 11 saura ta zare gyalen tana tsoki ta kwanta kan bed baccin da bataiba ya dauketa 11 dede ya iso kofar gidan wata yarinya yasamu yace ta kira masa faseelat, gabanshi nata dukan goma -goma.
Yarinyar nashiga ummi tace kice gatanan zuwa, tashiga dakin faseelat ta tadata”kitashi kigyara
fuskarki maza “
shaf -shaf ta sauka daga gadon ta kara kallon madibi bata tsaya kara shafa komiba tafita she’s eager to see him.
tana fita kofar gidan ta diba hannunta na haggu taga roba -roba  fa ke ,cikin ranta tace oh God ko yar honda bedaita mtssssw.
Tayi sauri ta juya hannunta na dama, se gashi tsaye yanata son ganin fuskarta tana waigowa ya zuba mata ido itama shi take kallo daga saman sa zuwa kasa.
baki ne amma not that black idanuwansa a bit tiny hancinsa gajere with medium mouth kayan jikinsa kaftani ya taso hula gaba har kan goshi daf da ido tsawon shi takalla dogo sosai shantaly kenan ????????zufar dole ce tashiga keto mata,
*da akwai matsala fa*????
in next page zamuji ya firarsuzata kasance.
Inaganin best wishes da adduoinku Nagode Allah yabar kauna
[7/12, 10:58 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
Writing by *MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
4
*dedicated to sis ZULAIHAT RANO*
*All praise be to Allah*
Shi ko kallonta yake saboda ta tafi da hankalinsa tabbas faseelat mace ce da inka kalleta seka kara kallonta, kallon kallo suke wa juna and ita nata kallon tanayi ne kawai amma hankalinta baya tare daita magana ma take da zuciyarta ga abinda take cewa “allahumma ajirni fii musibaty wa aklifly khairan minha, to musiba mana gabadaya tunaninta ya Kare akan mamakin tsawon sa dama duniya a kuma Katsina akwai masu irin wanga tsawo haka? Ta cigaba da cewa ya Allah kaceceni mu rabu da bawannnan naka lpya.
Shiko tashi zuciyar tuni ta kamu da kaunar faseelat  ,
Can zuwa ya tattaro natsuwarsa bakinsa na dan kyarma yace “Assalamu alaikum”
firgigit ta dawo hayyacinta still zufa na karyo mata se kace mejin kashi,
Tana mazurai tace “sannu da zuwa shigo ciki”
Wani iri yaji jin muryarta yayi tsaye itakuma tashiga cikin zauren gidan ya bita zalalo zalalo kamar rakumi da akala.
Har cikin zauren babban zaure ne dan already har an ajiye sit din roba biyu tai tsaye ta juyo sannan yakaraso tana nuna masa kujera tace” bismilla “
Ya haye ita kuma tasa gefen gyalenta ta share wata zufa data tsiyayomata ganin kafafunsa Sun dan baud’e kadan,
jiki sanyaye taja kujera ta zauna ta dukar da kai sam bata kaunar ganinsa, beyi mata ba, mi zatayi da baki?dogo kamar ba samude sam baze yiwuba.
Tunanin ta yakatse ne da yafara magana voice dinsa na vibrate saboda yadda yake jin tsoro yace “sannu malama faseelat, Da farko de sunana khalil shekaruna 35 ina teaching a all brighters academic, Hjy ta ta umarce ni nazo naganki mu dedeta ina fatan zamu fahimci juna ni da ke “
wata iriyar murya ce dashi gatanan de, ita kuma faseelat tana son miji me siririyar murya shi ko gata de, kamar wadda aka mara tashiga jijjiga kai, shiru ne ya biyo baya can ta tuna bata kawo masa drinks ba, ta tashi ta kawo masa dudu milk ta tsiyaya a cup ta mika masa, yayi kurba daya ya ajiye shiru beda abin fadi kanta na kasa amma duk dagowar da zatayi seta ga ita yake kallo,
Can zuwa yayi karfin halin cewa “kibani no din wayarki “
Faseelat gabanta na faduwa tana inda inda tace “ni banda waya”
yayi shiru can yace” ba damuwa inafatan nasamu karbuwa? “
tai shiru can zuwa ta daga kai
Yace “Alhamdullilah se na sake dawowa ko? “
Haushi ya kashe faseelat se tambaya yake kamar tsohon makaho ta dago tace “ihhhhhh”
Aiko yayi shiru ya tashi tsaye”ni nawuce “
Afili tace “tow agaida Hjy, a Zuci tace agayas “
yajuya yafita daga zauren takara bin bayanshi da kallo kuttt se yanzu ta lura rigarshi ta wuce gwiwa tsabar tsawo
Ta kai minty 5 zaune sannn ta tashi tai cikin gida,
Shiko Karon farko da yafara fira da mace dadi kawai yakeji yanda ya sameta ya tada babur dinshi yayi gida.
Faseelat nashiga cikin gida da sallama ummi ta amsa, zuwa tai zata wuce ummi tashiga daki ta kwanta ko ta samu ta dawo dede,
ummi tana kallonta tace “zo nan faseelat”
Tana daga kafa daya kan daya kamar wadda kafar taiwa dayi tazo gun ummi ta zauna,
Ummi tace “ya kukayi”
Faseelat ta sosa kai tare da cewa “naam”
ummi ta harareta tace “eh “
Sosa kai faseelat ta fara labbanta na kyarma tace “ummi beyi kama da mijin da nikeson aure ba “
ummi tarika jifanta da mugun kallo can tace “dan ubanki har wani kalar mijin da kikeso kika tsara? wallahi faseelat ki shiga hankalinki tom,”
Faseelat ta zumburo baki gaba “wlh ummi bani sanshi baki ganshiba beda kyau ko kadan “
ummi ta rike haba “faseelat? Dan kina ganinki fara shine zaki ce haka, ke kekikayi kanki haka hala? To kamar yadda kike haka fara shima haka Allah yayishi baki kuma haka yakeson ganinshi “
faseelat ta matso hawaye “Allah ummi ni banisonshi “
ummi tace “rufemin baki kar in mazgeki, dan kinsamu ze temakamiki ma wa yataba cewa yanasonki? Dankawai ze rufa miki asiri? To barikiji wlh inkinga baayi aurennan ba to abbanku ya binciko wani mummunan hali atare dashi ne ko in Allah ya kaddara
Ke ba matarshi bace amma ina tabbatarmiki se anyi bikinnan “
Faseelat ta dora hannu akai “nashiga ukkuna ummi dan Allah ki temakamin “
Ummi tace “temakon da zanmiki knan in aurar dake “
Faseelat tafasa kara tana kuka sosai ummi ko tatashi tabata wuri tace “ai seki tayi “
“wayyo Allah na ni wlh bansonshi “
Hardasu majina saboda kuka sallamar abbansu ne yasa ta gudu wurinshi ta rungume “abba dan Allah banisonshi karku auraminshi “
cikin mamaki yace “share hawayenki diyata “
Tasa hannu ta goge still wasu na biyowa yace “bawanda ze miki auren dole kinaji ki wuce kije ki kwanta “
Faseelat ta wuce sundum sundum ummi tafito daga kitchen “amma de alhaji kasan bazanji kunya nai magana biyu ba nariga na amsa musu yanzu mi kakeso nacema uwarsa ince bata sonshi? “
Abba cikin sanyin murya yace “haba asiya kibi komi sannu mana, wai ma duka Nawa faseelat din take ne? Duka fa yanzu shaekararta biyu da graduate, kibari komi asannu akebinshi ai yau suka fara haduwa may be su dedeta zuwa gaba”
Faseelat dake labe tace “wlh aa banisonshi bazan so sa ba harabada “sede  bawanda yajita dayake ta Shiga daki
Ummi tace “hmmmm”
Tashige kitchen
Shiko abba ya shige daki yana girgiza kai, yarasa daliin ummi da ta kagara ta aurar da faseelat.
faseelat kan gado ta mike tanata sharar kwalla har bacci ya kwasheta.
shi ko malan mudi da farin ciki ya isa gida,
Bayan ya shigar da babur dinshi yawuce dasauri dakin Hjyarsu Hjyar na tsefe gashinta da rabi yafara zama furfura ya shiga, Hjy saratu ta dago tana kallon fuskar shi tagane yana cikin farin ciki,
Ya zauna tare da cewa “Hjy kiniya zabe wlh tayi komi yayi dede, gata da kyau ga iya wanka “
Hjyar tai dariya” marar kunya kawai, aibaka isa aure ba “
Yayi shiru yana dariya “toya ita faseelat yanayinta ta amince? “
yace “eh Hjy “
“to yaushe Zaka koma? Kukara ganawa, kafin atura su kawu “
yace “gobennan Hjy “
Hjy tace “hmmmm Allah ya kaimu, sede dan Allah ka natsu kuma ka rika yimata kyautuka saboda takara sonka sannan kuma ka san maganar da zakurika yi “
Yace “to “
Yakagara gobe tayi
*nace da akwai matsala kufa? ????*
[7/12, 10:58 PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
Writing by *MAMAN MAMY*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION????????????~*
*~We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
5
*Dedicated to SIS ZULAIHAT RANO*
Ya kagara gobe tayi ko yakara ganin kyakkyawar fuskarta.
Wasa -wasa har dare faseelat taki tafito waje, ummi de ta share ta su abulkhair suna ta tambayarta sede ummi tace bacci take ,
Har abba ya dawo gida  bayan ishai ummi da abba suna daki suna fira while ishak abul da Mubarak na tasu firar, dan auta ya kasa hakura da rashin ganin ta ya leka dakinta tayi rubda ciki amma ba bacci take ba, abin duniya ne kawai ya sha mata kai, ganin idonta rufe yasa yaja mata kofar,
Dakin abba ya shiga ya samu ummi ya zauna gefenta “ummi kode ya faseelat bata lpy? Naga tundazu da rana bata fito ba yanzu naje dakinta na ganta kwance har yanzu “
Ummi tace “to bana ce maka bacci take ba? Ka tashi kaba mutane wuri “
Yace “to ummi kode a tado ta ni wlh gidan ba dadi da babu ita “
Ummi tace “kai kasani ai “
Abba yace “wai tun dazu bata fito ba? Kuma kika kyaleta haba Hjy kinsan fa ulcer na iya kamata “
“to ya kake so na mata? Ko so Kake naje na rarraso ta tunda na mata laifi “
Abba yace “yaro dan rarrashi ne in kika lallabata se ki shawo kanta amma bata haka ba, kinsan faseelat na da saukin kai ai “
“Alhaji kabarta kawai in yunwa ta kusa kasheta zata fito, nifa duk abinda nakeyi saboda ita ne yarinyar nanfa da kake gani kusan kullum se tayi mafarki, taya kake tunanin hankalina ze kwanta tana zaune gidannan gwara ai mata auren tun kan ai abun kunya “
Abba yayi shiru yana nazari,yace”eh ki de bita a sannu, wa ma ta gado inbake ba da jarabar tsiya in baayi miki 3 rounds ba baki koshi “ya ida yana dariya
Tace “eh naji din ai kai ma shine da har kake iya yin ukkun “
Suka sa dariya Mubarak fa yadade da barin wurin tunda aka korashi.
Ummi nata zuba ido faseelat zata fito cin abinci amma bata fito ba, se kuma tafara shiga damuwa.
Itako faseelat muguwar yunwa takeji ga, zazzabi da ya rufeta kwance kawai take tanata tunanin yadda zatayi rayuwa da khalil.
Can 12am samarin duk sunyi bacci ummi tafito daga dakin abba har zata wuce se kuma ta shiga dakin faseelat,
Tana kwance rubda ciki still ummi ta matsa “ke bana hanaki kwanciya haka ba?”
faseelat ta birkita ba tare da ta dago ba
Ummi tace “wai dani faseelat zaki fushi ?dan kawai ina fadamiki gaskiya? Ya kikeso nayi ne? So kike nabarki na zuba miki ido? Bayan ga hanya Allah ya kawo, haba faseelat wlh kinbani mamaki da har zaki bijirewa magana ta shi dake namiji ya amince da umarnin mahaifiyarsa, amma ke kinkasa “.
faseelat ta fashe da kuka tana sheshsheka ummi tace “aa kidena kuka faseelat bazan takura miki ba tunda bazaki iya aurenshiba shikenan gobennan zankira uwarshi in fadamata bakisonshi tunda burinki ki kunyatar dani, ni wlh daace kinada wanda kikeso da baabinda zesa na matsa miki amma keda bakida kowa ihhhhm? Dama ace ke lafiyayya ce amma kinada larura ki duba fa yanayinki faseelat, shikenan anfasa auren ki tashi kije kici abinci “
Ummi ta juya zata fita faseelat na kuka ta kira sunanta “ummi “!
Ummi ta waiwayo ta cigaba da cewa “Dan Allah ki hakuri baniso ranki ya baci karki fushi dani “
“bazanyi fushi da keba faseelat sede ki sani zaki sani cikin zullumi da tunani dan wlh inde ban aurar dake ba banida kwanciyar hankali “
Faseelat daga kwancen de take magana cikin rashin tunani tace “na yadda ummi zan aure shi inde zakiji dadi “
Ummi tace “dako kinfaranta min rai dan inada tabbacin bazaki kuka ba in Allah yaso”
faseelat tace “na amince ummi kuma kiyi hakuri da bata miki rai da nayi “
ummi tace “bakomi Allah ya miki albarka ki tashi kici abinci karkijawa kanki ciwo”
Faseelat tace “bazan iyaba ummi masassara nake tun dazu “
ummi tace “subhanallahi “tana hawa kan gadon ta fara tattabata gabadaya jikinta rau yake har kafafunta, ummi tace “sannu kinji bari na kawo miki magani “
Ta tashi ta fita wani kuka ne yazowa faseelat ita kanta tasan ta amsa ne kawai amma tasan haka zatai ta rayuwar hakuri harabada, tasa hannu ta share hawayenta yanzu de koba komi ta farantawa mahaifiyarta rai da tun tasowarta tana ganin yadda take fifita ta akan yanuwanta.
Motsin da taji yasa ta  kara goge fuskarta ummi tashigo dauke da tray ta ajiye ta bude flask ta debo taliyar hausar da ta dafa da daddare ta dora kan bed ta debi ruwa ta ajiye sannan ta zauna bakin gadon tace “tashi ga abincin diyata “
Faseelat na ciza baki ta yunkura ummi taida tadata zaunen jikinta har kyarma yake saboda yunwa,
Ummi  tafara bata abincin a baki da yake tana jin yunwa taci abincin sosai sannan ta bata magani ta koma ta kwanta se sannu ummi ke mata sede ta daga kai, tashi ummi tayi taja mata kofa tana mata seda safe.
ko bayan fitar ummi faseelat kuka ta rikayi ga bacci ya kaura cewa idanunta,
Ba abinda take tunani se fuskarshi da jikinshi tana tunanin yadda zasuyi rayuwa tare wuri daya gida daya daki daya gado daya.
Se asuba bacci ya dauketa, ummi na Gama azkhar taje ta gaida abba yake tambayarta jikin faseelat da yake wurinshi ta amso maganin tace dasauki ta fita dubota, tana shiga ta tada ta faseelat bude ido kawai tayi ummi tace “ya jikin “tana tabata faseelat tace “dasauki “
Ummi tace “naji haryanzu da fever din kitashi ki salla inje in hado miki tea kisha kisha magani “
Faseelat tace “I’m off”
Ummi tace “kinada pads ne? “
Faseelat tace “eh amma beda yawa “
“OK anjima zanba Mubarak yasiyo miki wata tashi kije ki kimtsa ko kinji dadin jikin “
faseelat tace “to “ta mike ummi taga har tangadi take ummi tace “zakiiya wankan kuwa “
Faseelat tace “eh “tafara bin bango ummi takamata ta kaita toilet sannan tai kitchen,
Da dai daya yanuwanta suka rika shigowa suna mata ya jiki kafin su bar gidan, shi ko Mubarak harda hawaye danba karamar shakuwa sukai ba daita.
Bayan tasha tea din da magani ta koma ta kwanta,
Can wajen 12pm ummi nata aikace aikacenta wani yaro yazo yace ana kiran faseelat .
Ummi ta danyi jimmm sannan tace “gatanan zuwa “
Yaro yaje ya kai sako
itako ummi tashiga dakin faseelat har lokacin tana bacci ummi tafara tapping dinta tana kiran sunanta faseelat ta bude ido, tana kallon ummin.
Ummi tace “ki daure kitashi ki dan kimtsa ga khalil can yazo “
Faseelat gabanta ya bada dudum, tasan datace bata iyawa ran ummi ze baci dan dole ta mike tsaye ummi tace “zade kiiya ko? “
Faseelat tace “eh ta jawo hijab har kasa ta saka ai gwara tajema ta kara ganinshi maybe jiya batai masa kallon tsaf ba.
Tana saka hijab din tafita ummi ta girgixa kai tana kallon yadda take tafiya a kasalance.
Faseelat na fita taganshi  a…..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button