NOVELSTA DALILIN SO

TA DALILIN SO 7&8

🅿️ 7&8

Cigaban labarin….. K’AJEJE na juyowa suka had’a ido da Al-hussain”wanda kebinsa da wani irin banzan kallo hankalinsa kwance”

fisge hannunsa k'ajeje yayi ya juya da nufin ya d'akko addarsa"

Husnah dg ita har salaha kallon mamaki sukebin Al-hussain dashi”yyinda sauran jama’a ke zaton k’ajeje saiya raunata Al-hussain”

meyasa zakayi haka pls?”cewar husnah tana kallonsa”d’auke kansa yayi yana tattare hannun rigarsa”sbd ganin yaran k’ajeje sun nufosa gadan gadan”

K’ajeje kuwa gani yayi ba girmansa bane yana d’an aji hud’u yatsaya danbe da d’an aji3″gara yabar su Alonso su koya masa hankali kawai.

kan kujerarsa yazauna yana bin husnah da wani irin mayen kallon k’asan ido”

saliha kuwa hannun husnah taja”tana cewa kizo muje bansan meyasa masifarki take da yawa ba?

Ina zakije da ita?”cewar k’ajeje yana kallonsu”hakan kuma yayi daidai da isowar su bawo da Alonso gun Al-hussain”

Idan kun isa mazaje ku yadda makamai mana”cewar Al-hussain”yana tab’e baki”

gaba d’aya akayi tsit wajen ana kallon abinda ke faruwa”

saliha kuwa baya tayi ta rabu da husnah sbd gudun kar k’ajeje yasakota a case d’in”

Tsaye husnah tayi gabanta nata fad’uwa”wani wawan punch bawo yakawowa Al-hussain”cikin zafin nama yagoce”wanda Inda yasameshi dole yamasa illah”cikin sa’a Al-hussain yafara basu punchers…

sosai suka fara dukan juna”da yawa student na mamakin Al-hussain”wasu na cewa” k’ilan gwahinsa be karyeba…lolx”

Hankalin k’ajeje yatashi dayaga Al-hussain na suburbud’an yaransa”

Cikin zafin nama yad’auki addarsa”yanufo husnah”

Husnah tasaki k’ara”Al-hussain yadubeta da sauri”

Hankad’a bawo k’asa yayi hancinsa nata jini”yyinda Alonso yabaje awajen”

student suka d’auki ihu da shewa”hakan kuma yayi daidai da isowar wasu malamai tareda security dasu Abdallah da ibbi”

k’ajeje beyi wata wataba yad’aga addar da nufin yasari husnah….. Al-hussain yayi saurin rike addar da hannunsa guda biyu”atake hannunsa na haggu dg tsakkiya ya yanke”jini yafara zuba”hannunsa guda na dama yasaka yakaiwa k’ajeje wani mugun Punch”atake k’ajeje yasaki addar”yana tab’a gefen lips nasa yaji jini….nika fitarma da jini?”yafad’a cikin tsananin b’acin rai”

hakan kuma yayi daidai da shigowar malamai da security agurin”atake aka sakawa k’ajeje ankwa”saurayin aka wuce dashi asibiti”

k’ajeje yasha mummunan alwashi akan husnah da Al-hussain”yanaji yana gani aka nufi station dashi”

gashi abin damuwa daddynsa baya k’asar balle yasaka afito dashi.

Husnah kuwa da sauri itada su Abdallah suka nufi gurin Al-hussain daya rintse idanuwansa sbd zafin da ciwon ke masa….

subahanallahi!sannu muje akaishi asibiti amasa dressing ko?”cewar husnah arud’e tana kallon Al -Hussain”

Abdallah da ibbi dabasu gane kan zancenba”suka bita da kallo”husnah na k’ok’arin sake mgn Al-hussain yabud’e idanuwansa”had’a ido sukayi da ita”,atare gaban kowanan su yabuga”

husnah tayi k’asa da kanta zatayi mgn kenan”saliha tazo ta fisgi hannunta suka bar wajen”

haba saliha ina zakije dani?”kina ganin Hussain yaji ciwo fa kuma duk akaina??”

wlh husnah kishiga taitayinki da mazan skul d’in nan”kinsan kuwa waye K’AJEJE?”

meyasa kika tsoma kanki acikin abinda bbu ruwanki?”kunyi fad’a da Al-hussain shine yanzun ma kika sake jawo wani fad’an??”

Ki fahimceni mana salaha”cewar husnah tana sanar mata yadda akayi”

Allah ya kyauta”amma idan yadawo kibashi hak’uri”sbd nasan wlh bazai k’yalekuba”

Al-hussain dama beda ruk’o gsky”inda badan shiba kuma wlh abinda K’AJEJE zai miki sai kinyi nadamar shiga huruminsa”

Tab’e baki husnah tayi tace”.be isaba wlh”hak’uri fa kikace?”Eh mana ubansa nada kud’i da iko”wlh nasan zuwa gobe za’a sakesa”

Hmmm to Allah yakaimu lafiya” be isa yamun abinda Allah be munba wlh”

ni zan wuce aji befi 5 minit mushiga lacture ba”cewar husnah”

Dato kawai saliha ta amsa ta wuce warta”

Husnah na isowa aji akamata caaa da ido”duk ta sharesu ta musu banza”

Amma ta lura bbu Al-hussain dasu Abdallah a ajin”

Bayan sun fito gurin k’arfe 1:12 pm”husnah jikinta asanyaye yake”

Tana tunanin ko yaya jikin Al-hussain d’in?”wata zuciyar tace”.kindamu dashi ne?”dole nadamu sbd ta sanadina haka yafaru”tafad’a afili….

Hango Al-hussain da Abdallah da ibbi tayi”ga hannun ammasa dressing”

nufosu tayi fuska cike da tausayi”amamakinta sai taga AL-HUSSAIN yawani had’e girar sama data k’asa yana wani basarwa da shan k’amshi”

wani mugun haushi taji”aranta tace”.nafika miskilanci da aji wlh”

saurin canza hanya tayi ta rab’asu ta wuce bata ko koma kallonsuba”balle su sami arzik’in ta musu mgn”harsu ibbi saida suka waiwayeta sbd mamakin data basu”dan Al’hussain yabasu labarin yadda akayi.

bayan ta wuce tace”.aikin banza kawai”ninace kata remun fad’an ne balle ka d’aga mun kai?”.

Masjeed ta wuce taje tayi sallah”sannan ta shiga cikin gari tayo shopping”

sai kusan3 pm ta iso gidan”saliha bata dawoba”indomie ta dafa taci tayi wanka da sallar la’asar”sannan takoma skul d’in sbd tayi Assignment da aka basu yau….

haka husnah taci gaba da rayuwarta askul d’in”duk abinda ake koya musu tana k’ok’arin maida hankali taga tagane”

Yyinda tun wannan ranar bata koma ganin k’ajeje ba ko jin labarinsa ba”

sannan tunda Al-hussain yamata wannan shan k’amshin”bata koma kulasaba”ko Inda suke bata kallo balle ta musu mgn”

Harkan gabanta kawai takeyi”yyinda y’an gulma abaya suka fara zaton ai Al-hussain sonta yakeyi.

shima anashi b’angaren be kulata yashareta”

Ayau yakama monday”tun 9:am suke aji ana lactures”sai kusan 3pm suka gama lactures”

sosai husnah takwaso gajiya da yunwa”kai tsaye skul shop ta nufa”

Lemo fenta mai sanyi ta siya da cake” da nufin ko sune tafara ci kafin taje taga meye saliha ta dafa musu tunda tare suke komai…

tana k’ok’arin ciro kud’i tabada a hand bag nata taji muryar Al-hussain cikin izzah da gadara yana cewa”ina ruwanki danine?meyasa suwaiba bakida zuciya ne?”d’ago kanta husnah tayi ta kalli direction d’in dasuke tsaye”

Kallo d’aya tayi musu shida yarinyar ta d’auke kanta”ta lura da dressing d’in yarinyar”ta kuma yarda da cewa bbu tarbiyya atare da ita.

kanta ta d’ago ta mik’awa john 1k ta tsaya ta amshi canji”amsa yayi yana kallon Al-hussain daya k’araso”

Chips ,fenta &maltinah zaka samun”yafad’a yana dg tsaye yana satar kallon husnah”wacce ke k’agare john yabata canjinta ta wuce”

Komai john yamik’a masa yana murmushi”amsa Al-hussain yayi yace”.ga wacce ta siyamun nan saita biyaka kud’inka”

husnah taji gabanta yafad’i amma bata ko kallesaba balle ta nuna da ita yake”

John na murmushi yace”.madam kud’insa 1500 ne”yanzun 1,100 zaki ciko kinbar canjin 400 ai ko?”

Husnah…….

  *****************

Aguje hafsat ta shigo cikin parlourn tana k’walawa mamy kira”

mamy ta fito dg kitchen sbd taga lafiya meke faruwa??

Hafsat ta fad’a jikin ta tana kallon k’ofar shigowa”mamy yaya ne wlh!mamy na k’ok’arin mgn AL’HASSAN yashigo parlourn fuskarsa tamkar hadarin gabas bbu annuri ko kad’an”ga belt a hannunsa.

k’ara hafsat tasaki tana rirrik’e mamy”dan Allah mamy kibashi hak’uri”

Kallonsa mamy tayi tace”.karka dukarmun yarinya Al’hassan”

sokakeyi jikinta ya taurare da duka kome?”

Tsaye yayi yana bankowa hafsat harara cikin husky voice yace”.mamy kece kike b’ata yarinyar nan wlh”

yau kusan mutum3 yakawo k’ararta agidan nan”

yanzun k’arfe 4:11pm tun 2 nace taje tayi shirin islamiya”amma shine tak’i ta sulale waje suna fad’a itadasu salima(k’awartace a mak’otan su)

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button