TAKUN SAAKA 13

“Ummi dan ALLAH ki barni in fara ci ni dai”.
Komai Ummi bata sake ce mataba. Sai ma miƙewa tai ta shiga takawa a hankali domin zuwa ɗakinta tai salla. Dan har yanzu jikin nata bawai yayi ƙarfi yanda ya kamata bane. Abincin ma Yaya Usman ne ya yisa kafin su wuce tasu Islamiyyar.
Sai da Hibbah taci tai nak da abinci sannan ta shige ɗakinta. Bata fito ba sai wajen 8:30 da tajiyo hayaniyar yayunta. Cike da ɗokin dawowar tasu ta fito. sai dai ganin harda Isma’il ya sata yin turus.
Komai babu wanda ya ce mata a akan yanayin nata. Sai ma tsokanarta faɗa da Ammar ya shigayi. Amma sai bata tayashi sunyi ba. Masifa ma taketa faman yi a ranta na yanda yayun nata suka sakema Isma’il ɗin kai kace ɗan gidan ne. Shi kansa yanda yake komai kansa tsaye sai ka rantse gidansu ne.
Bata wani jimaba tai musu sai da safe ta shige, ta barsu a falon suna kallon ball suna hira da cin abinci. Ummi ma tunda ta leƙo suka gaisa da Isma’il ɗin ta koma ciki abinta. Dan haka Hibbah bata san sanda Isma’il yabar gidan ba.
Washe gari dai an tafi islamiyya babu fushi. Sai dai kuma damuwar ƴan sandan can da ke damunta har yanzu ya sakata komawa wata silent kwana biyun nan. Ko magana ma bata cika sakin jiki tayi ba. Sannan har yanzu bata sake hawa computer ba. Dama wayarta tunda ta dawo take a kashe taƙi ta kunna.
Yau ma suna fara tafiya a kan hanyarsu ta zuwa islamiyya ta fahimci ana binsu a baya. Wani takaici ne ya turnuƙe ta dan tsaf ta gane guy ɗin jiya ne da tun a ƙofar gate ta watsar da lamarinsa. Ba kuma ta sake tunawa da shi ba sai yanzu da taga motarsa. Sam Zahidah da Hafsat su basu lura da shi ba. Hakan yasa Hibbah fuskewa batace komai ba har suka shige cikin islamiyya.
Ƙarfe biyar suka ta shi yau ma tamkar kowane weekend. Da ga nan kuma sai wani satin. Gaba ɗaya ta sake watsar da lamarin wani Shuraim. Amma a mamakinta sai gashi ta sake ganin yana biye da su har gida. Kamar da safe yanzu ma bai yunƙurin fitowa ba. A yanzu kam su Zahidah sun ganshi. Koda sukaima Hibbah magana sai tai musu tsaki ma.
Ƙyaleta sukai ganin shima bai fito a motar ba.
★★
Duk yanda Hibbah taso watsar da lamarin Shuraim sai hakan bai yuwu ba yau. Dan lokaci-lokaci yakan faɗo mata a rai. Sai dai takan ja tsaki da murguɗa baki tamkar tana a gabansa. Har takai abinda takeyi ɗin ya bama Ummi haushi ta balbaleta da faɗa har su Yaya Muhammad suka shigo.
Sune suka bama Ummin haƙuri da fara tambayar Hibbah cikin lallashi ko wani abu ke damunta ne?. Sam batasan wani boye-ɓoye ba. Musamman ma awajen yayunta da suke da matukar shaƙuwa da juna. Kanta tsaye ta shiga basu labarin abinda takema tsakin.
“Woow, ƴar Tanee ɗin Ummi anyi saurayi Congratulations. Yau ɗaya a tarihi dole na rubuta na ajiye na haɗa da shagalin barbaje kolin fati na musamman a gidan nan nayi suriki a matsayina na yaya mai lasisin cin gadon Muhibbat Aliyu Hamza (Tanee)”. Ammar ya faɗa yana tafa hannaye cike da tsokana. Filo Yaya Abubakar ya ɗauka ya jefe sa da shi. Dariya gaba ɗayansu suka kwashe da shi saboda yanda Ammar ya baje a ƙasa da bata fuska alamar yaji zafi..
Hibbah kam dariya sosai take masa harda faɗowa saman kujera. Ta saka yatsun hannunta a kunne tana masa gwalo kamar yanda yara keyi. Filon da aka jefesa da shi ya ɗauka zai jefo mata ta tashi da gudu tai hanyar ɗakinta.
“Ummi kanta sai da tai dariya. Cikin dariyar ne ta ce, “ALLAH dai ya shirye ku, kai da Tanee ɗin bansan wanda yafi wani shashanci ba. Ni tashi ka ɗakkomin magunguna na a ɗaki tunda ita ta gudu nasan ba sake dawowa zatai ba kuma”.
Amsawa Ammar yayi da to yana mikewa ya nufi ɗakin Ummin. A dai-dai kuma wanann lokacin Abba da hajiya mama da wasu tsoffin maza biyu suka shigo falon da sallama.
Da ga Ummi har yaranta da mamaki suke kallonsu, musamman ma Abba da basusan ya dawo gidan ba. Tsoffin kuma Ummi ce kawai ta sansu. Da ƙyar ta iya buɗe baki cikin ƙarfin hali ta ce, “Kawu sannunku da zuwa”.
Farin ne kawai yace, “Uhumm”. Ɗaya kam bai tanka ba. Sai dai bin su Yaya Muhammad da yake da kallo tamkar idanunsa zasu faɗo ƙasa.
Yaya Muhammad da ya lura da kallon ƙurullar da kuma yanayin da Ummi ta shiga tamkar na ruɗani ya saka shi fara gaishesu. Haka yasa suma sauran ƙannensa fara gaisuwar.
Amsa musu sukai suna cigaba da kallonsu. Yayinda hajiya mama keta faman ƙyaɓe baki. Abba kam sai wani harare-harare yakeyi.
Ummi tai ƙasa da kai cike da ladabi ta hau gaishesu itama. Basu wani amsa mata da ƙyau ba. Sai ma baƙin tsohon ne a kausashe ya ce, “Uh lallai Asiya an samu guri kam tabbas. Ga manyan sojoji kuma a gefe masu tare miki faɗa. Dama irin wanan ai ake gudu akan auren masu asali irin naki. Saboda shi hali naso yakeyi har jikokin bayan-baya. Gashi ko mun gani yau da idanun mu”.
Idanu Ummi ta lumshe a hankali kanta a ƙasa. Wasu zafafan hawaye suka silalo saman kumatunta. Sai dai cikin dabara ta kai hannu ta share dan kar ƴaƴanta su gani. Cikin dauriya da juriyar da kowa ya santa da shi ta ɗago murmushi a saman fuskarta. “Kawu ina fatan kunzo lafiya?”. Ta faɗa domin son kauda wancam zancen da ya fara.
Sai dai sam bataci nasara ba. Dan kuwa hajiya mama ce ta amshe da faɗin, “Ni ko zan faɗa maka hali naso yake Hannafi, dan kuwa gashi nan a zuri’a ta. Wlhy badan jinin ɗan inna (babansu Hibbah) na yawo jikin waɗan man yaran ba da tuni na daɗe da sallama su, babu wanda ya cuceni sai malam da ya ƙarrafa wannan auren da har na mutu bazan taɓa daina kuka da ALLAH wadai a kansa ba. Wai fa kuga waɗan nan sanƙama-sanƙaman yaran ne babu mai ko neman aure. Kuma uwarsu ta zuba musu ido saboda ita ɗin bata hanyar…….”
“Waɗan nan kuma fa? Da ga ina?”. Cewar Ammar da ya fito da ga ɗakin Ummi yaci karo da abinda bai bari ba. Furucinsa kuma ne ya katse zancen da Hajiya mama ta ɗakko tiryan-tiryan.
Babu wanda ya bashi amsa. Sai zuba masa ido da tsoffin sukai tare da Abba. Baki ya buɗe zai sake magana Ummi ta girgiza masa kanta. Kansa ya ɗauke kawai tare da durƙusawa gabanta ya na ajiye ɗan basket ɗin da magungunan nata ke a ciki. Ɓalla mata ya shigayi yana miƙa mata tare da saka mata ruwa akan baki.
Wani uban salllami farin tsohon nan ya shiga jerawa yana tafa hannaye. “Kai mizan gani haka ni Ballo (Bello????). Wannan wane irin kafurcine kuma haka Hasiya?. Wannan ƙurmisheshen gardin ɗan ke baki ruwa a baki kuma?. A to lallai zancen Hannafi gaskiya ne. Da alama ma ke kinfi uwar taki iya shege”.
A fusace Yaya Umar ya miƙe zai bar falon. Abba ya katsesa a gadarance da faɗin, “To mara mutunci da baiyi gadon arziki ba sai ka tsaya dan zuwan nakune ai”.