HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 19

 

Halin Girma      19

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

**************

Ta cikin ido Moh ya kalli Mama da ya lura kamar tsaiwar na neman gagarar ta tunda aka fara daukar hotunan, gashi sai dauka ake an ki dainawa itama a cikin yanayi take da saura kad’an ta zube a wajen idan aka cigaba da daukar hotunan. Sai da ya tabbatar da tayi masifar kaiwa karshe har tana neman fito da abinda yake zuciyar ta ne sannan yace ya isa haka, tayi saurin fadawa daki babu ko magana, hannun Iman din ya kama a gaban kowa, suka juya suka bar part din yana jin a kalla Mama zata yi hankali, a kalla zata san rayuwa da yadda take juya wa bawa.

    Tafiya sukayi bayan sun yi sallama akan zuwa magriba za’a zo a dauki Iman din. Sake chanja kaya tayi zuwa wasu kayan na daban, suka zauna cikin yan mata da sauran yayan da aka ma aure a family aka dinga hira cikin farin ciki. Bata saka musu baki sai dai tayi murmushi musamamn da ya zama kusan rabin maganar akan zaman aure ne wanda take jin kamar wasu maganganun sun girmi kanta.

   Gabatowar la’asar ya sake saka Iman din a cikin yanayi fargaba, irin wanda ake ji idan za’a rabu da gida. Tashi tayi ta ja Khadija suka fita zuwa shashen su, tana son ganin Zeenat sannan tana son daukar wasu abubuwan a dakin su.

   Shigowar su ya saka kowa na falon bin su da kallo, kai tsaye dakin Mama ta wuce Khadija na binta a babu yadda zatayi. Kusan zabura mama tayi ganin ta, ta tamke fuska tamau tana jin haushin shigo mata da tayi a halin da take ciki. Har kasa ta duk’a, ta gaida Maman sannan ta gaida su Aunty Maimuna. Duk sun amsa banda Maman da tayi kamar bata ji ba, tashi tayi bayan nan ba tare da wata magana ba ta wuce zuwa dakin su. Tayi mugun mamakin ganin Zeenat din, sai taji tausayin ta ya kama ta, ta durkusa a gabanta tana tuna lokacin da ta taimaka mata da bata jin dadi.

“Zeenat?” 

Ta kira sunan ta, sai a lokacin ta san sun shigo dakin ma. Da ido tabi Iman din kamar taga sabuwar halitta, 

“Iman?”

“Na’am, baki da lafiya ne? Kin ganki kuwa Zeenat?”

“Bani da lafiya Iman, bana jin dadin komai, wallahi bana son auren nan gashi an riga an daura, tsoro ma nake ji kar naje na aikata wani abu mara kyau.”

” Me ya faru? Me yasa bakya so?”

” Bashir karya yayi min, babu gaskiya a maganar sa, bashi da komai fakiri ne wallahi.”

Shiru Iman din tayi dan bata san me zata ce ba, tunanin yadda akayi hakan ta faru take, sai dai bata san yadda zata dauki maganar ta kuma ajiye ta ba. Kuka Zeenat din ta sake fashewa dah, kuka dacin da take jin sa a chunkushe a makoshin ta. Baki Iman din ta dinga bata, ta samu da k’yar tana maida numfashi. Tashi Iman din tayi ta duba wajen da ta ajiye jakar islamiyyar ta, ta dauka sannan ta sauki abubuwan da tasan zata bukata ba kaya ba. Khadija ta bawa ta tafi kai mata wajen Mamma sannan ta dawo ta cigaba da kwantar wa da Zeenat din hankali.

   Kamar ba Zeenat ba da take taka Iman din tayi mata duk wulakancin da ta ga dama, tayi laushi sosai,har tana dora kanta a kafar Iman din. 

   Wayar hannun ta ce tayi k’ara,  Moh ne yake kira, dagawa tayi tana tashi daga gaban Zeenat din 

“Amaryata.” 

“Umm.” Ta turo baki, dariya yayi sosai kafin yace

“Ki cigaba da turo bakin nan, babu ruwana aka samu matsala wallahi”

Murmushi ta samu kanta da yi, ta jujjuya kanta tace

“Kaiko?”

“Me nayi?”

“Ba komai.”

“Sharri kawai zaki min dan kin ganni bawan Allah.”

“Nima ai baiwar Allah ce.”

” Na yarda kuwa, are you ready?”

” Mefa?”

” Shigowa fadar Moh.”

” Ummm.”

” Get ready kinji? Yanzu zasu zo, kwana biyu zuwa uku zamuyi anan sai mu wuce adamawa.”

” Adamawa?” Tace tana zaro ido

” Calm down, zan miki bayanin komai.”

” Shikenan.” Tace a sanyaye

” That’s my wife, Allah yayi miki albarka.”

” Amin.” Ta amsa tana sakin murmushi a hankali.

Kashe kiran yayi, Zeenat ta bita da kallon sha’awa, tana hango tsantsar dacewar da Iman din tayi, gashi ita ta tashi a tutar babu.

“Zeenat bari na tafi, zamuyi waya in sha Allah, kiyi hakuri dan Allah ki kwantar da hankalin ki.”

Jumbur ta mike, ta rik’e jikin rigar ta tana goge kwallar da ta zubo mata

” Dan Allah Iman karki tafi ki barni, wallahi ba zan iya zama da Bashir ba.”

” Me yasa? Bakya son sa ne wai dama?”

” Wallahi bana son shi, ko kad’an wallahi laifin Mama ne.”

” Iman!” Taji muryar Mamma a kofar dakin tana kiran ta, juyawa tayi ta fita tana kallon Zeenat din cikin tausayawa

” Ke kuma daga zuwa daukar abu sai ki zauna? Kinga ai lokaci yayi ko?”.

Bata ce komai ba sai kawai tabi Mamman suka bar bangaren, ranta babu dadi ko kad’an.

   Wanka mamma ta sake sata tayi, kayan da zata chanja ta tarar a dakin, an turara mata su da turarurruka masu dadin kamshi. Tana shiryawa tana tunanin halin da Zeenat din take ciki, yadda ta firgice ta shiga tashin hankali zaka gane akwai wani abun a k’asa, ba wai kawai dan Bashir din bashi da hali bane kamar yadda ya Maryam ta bata labari.

   Duk shirin da tayi da taimakon su Harira, aka kuma kawo wata sabuwar alkyabbar aka dora mata, tayi kyau ainun, babu make-up babu komai amma yadda fuskar ta take sheki kadai zaka gane ba karamin gyara tasha ba.

  

   La’asar likis sai ga jama’ar gidan su Bashir, motoci goma ne gaba daya har data amarya , yadda za’a samu kowa ya je har mutanen unguwa, a lokacin babu irin kiran da be yiwa Zeenat din ba akan gasu nan amma bata dagawa, shiyasa kawai ya kyale ta domin shi a yanzu ba ta ita yake ba, yadda zasu kwashe da hajiyar ce kadai matsalar sa, labari ya riga ya kai mata ya kuma san gamon su bazai taba yin kyau ba, gashi akwai wasu kudade da ya ta bashi da nufin zai mata wani aiki ya bi ta kansu.

   Hankalin Mama ne ya kara tashi sanda suka iso, ta tabbatar da gaske Zeenat dai sai ta tare gidan Bashir, kiran Abba tayi, kafin ma ta fadi komai yace

“Ina falon Yaya idan kun gama ki turo min Zeenatun.”

Daga haka ya kashe kiran, cikin sanyin jiki Mama ta nufi dakin su Zeenat din, ta tarar da Aunty Maimuna na ta fama da ita akan ta tashi ta shirya, ganin shigowar Mama ta saka ta saurin tashi ta nufi wajen Maman.

“Jeki shirya Zeenat, kiyi sauri Mahaifin ku yana kiranki.”

“Mama?” 

“Ya zanyi? Ya zanyi? Aure an riga an daura ba kuma zan je na chakumi wuyan Bashir nace lallai sai ya sake ki ba, tunda kuma an daura ai dole ki tafi, dole ki bishi shine mijinki, ya zanyi.”

Fashewa tayi da kuka, tayi saurin fadawa toilet din ta rufo kofar, danne zuciyar ta sosai Mama tayi, ta juya ta bar Aunty Maimuna a dakin ta kuma jaddada mata kar su bata lokaci. Mamaki sosai Aunty Maimuna tayi da yadda Maman ta dake, amma kuma ta hango tsantsar tashin hankali a tattare da ita.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button