Labarai

Tashin Hankali: Matashi Ya Babbaka Uwarshi Har Lahira A Jihar Neja

Mazauna unguwar Darusalam da ke Minna, Jihar Naija sun tashi cikin kaɗuwa da firgici bayan da wani matashi, mai suna Steven Jiya, ya bankawa mahaifiyarsa, Comfort Jiya wuta.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Steven, wanda ɗan ƙwaya ne, ya dawo da ga garin Suleja a Jihar Naija ɗin dai, inda bayan ya dawo gida ne, sai kawai ta raya masa cewa ya ƙona mahaifiyarsa.

Jaridar ta ce a lokacin Comfort, wacce tsohuwar Shugabar makarantar sakandire ce, tana tsaka da girki a kicin, sai kawai wannan tambaɗaɗɗen ɗa ya zazzaga mata fetur ya kuma cinna mata wuta a gidanta da ke unguwar Darusalam ya kuma tsere.

Nan fa ta fito a waje tana ihu a kawo mata ɗauki, inda kan ka ce kwabo, wutar ta ƙone mata ilahirin jikinta.

Wata majiya a dangin marigayiyar ta ce an garzaya da ita asibiti inda ta ke jiyya.

Sai dai kuma, da misalin ƙarfe 3 na yammacin jiya Juma’a, marigayiya Comfort ta ce ga garin ku nan.

Wata majiyar ta ƙara da cewa dama can Steven fitinanne ne kuma ya yi yunƙurin hallaka uwar tun a baya.

Jaridar ta ce ta tuntuɓi rundunar ƴan sanda ta Naija amma haƙar ta ba ta cimma ruwa ba.

Sai dai kuma, in ji jaridar, tuni dai ƴan sandan Caji-ofis na Minna su ka samu nasarar damƙe Steven kuma har an kai shi babbar kotun Minna inda zai girbe abin da ya shuka.

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button