UBAYD MALEEK 39

wani irin azababben Nishi dake fitar Mata daqyar.

Gyaran murya jekadi tayi tana kallonta batareda taji tausayinta ko dayaba aranta.

Daqyar cikin tsananin azaba padima ta dago idanuwanta dasuka kumbura suntum dama fuskarta Baki daya 

Dukkaninta tayi jajir koina jininta.

Da hannu jekadi ta nuna Mata abincin data shigo dashi tana cewa”

Ga abinci Nan kici zai taimaka Miki kadan gurin samun karfin iya daukan  dose din anjima.

Wasu siraran hawayen azabane suka silalo Mata ta gefen ido ta bude bakinta daya kunbura batako iya motsashi daqyar can qasa ta iya furta”

Meyasa? Meyasa akemin Haka????

Numfashi jekadi ta sauke ahankali tareda kallon padiman tace”

Da zakiyiwa kanki adalci tun Baki lalace da yawaba da kin Fadi inda Kika samo wannan garin da kanki Amma nasan burinki da gurbataccen tunaninki bazai Bari 

ki zabi hanyaba.,

Wannan shine aikin da kikaje gidan ‘yar uwarki aikatawa akan mijinta kokuma nace akan MALEEK sbd qyashi da hassada sungama cinye zuciyarki gashi kin samu 

kanki acikin abinda tun kafin kizo duniya yake Dan haka batareda wahalarda sauran rayuwarkiba kifadamun inda wannan garin meriz din yafito yashigo hannunki.

Rintse ido tasake Yi cikin wahala wasu siraran hawayen suka sake gangaro Mata tanason fashewa da kuka batada hali sbd batada qarfin iyawa tanaji tana gani 

jekadi ta fice tasake rufeta cikin dakin dakeda tsananin duhu da zafi ta daga hannunta dake rawa ahankali ta wawuro abincin taga flatbread na alkama da 

dafaffuyar madara 

Jikinta na tsananin rawa takai madarar Baki ta shanye tana Gama shanyewa tasaki cup din tana zare idanuwanta dake firfitowa kaman zasu tsinko jikinta ya 

tsananta rawa ta  kife agurin tana ihun da baya fita ko kadan sbd dushewar murya cikin azaba Dan Ashe anxuba meriz din ciki.

Kwanan padima biyu Ana shayar da ita meriz ahankali ahankali Wanda yagama illata dukkanin jini da gangar jikinta tareda fatarta da duk tagama sabewa Takoma 

Kamar wadda aka tsoma cikin tafasasshen ruwa takai takawo ko motsi batayi Wanda yasa hankalin jekadi tashi ta sbd ganin Kamar padiman zata mutu saita dakata 

da Bata saidai dai gabaki daya padima ta sabule tashiga cikin wani irin mawuyacin hali na azaba tanajinta Amma ko motsi Bata iyayi banbancinta da matacci 

numfashin datakeyi ne kawai Wanda shima cikin tsananin azaba takeyinsa,

Tayi kukan zuci Dana ido Wanda baida amfani sbd dukkanin nadamarta Mara amfani ce tunda yau Bata ganin iyayenta bare ‘yar uwarta Susan halinda take ciki 

bare su yafe Mata ko haqqinsune yakamata yasata cikin wannan mummunan qaddarar.,

A da batada fatan datakeyiwa iyayenta da ‘yar uwarta tabasu tsoro Dan tayi amfani dasu saina Kiran mutuwa yau gata zatayi mutuwar bama ta gataba ta 

wulaqanci wadda taso maleek yayi gashi ace itace zatayi.

Hawaye suka gangaro gefen idonta suna sauka kan fatarta dake radadin azaba tace”

 ****************

Direct dakin afia din NURU ta nufa data fito farhat ma ta tashi tana biyeda ita suna shiga dakin ta waiwayo tana kallonsu farhat ta qarasa gurinta da gudu 

cikin tsananin farin ciki me yawa tana cewa”

Yeeee afia.

Rungumeta afia tayi cikin farin cikin ganinta da kewarta datayi kwanakin tace”

My baby I love you I love you.

I love you too afia Kuma nayi kewanki sosai musamman kafin Aunt NURU da daddy sudawo nikadai dasu mum Sarah munata Jin dadinmu.

Rungumeta tasakeyi tana kallon NURU dake kallonsu cikin murmushi ta qaraso tana kallon afia din tace”

Sannu da zuwa.

Murmushin afia tayi tareda sakin farhat taqaraso gaban NURUn suka Dan rungume juna NURU ta bude Baki ahankali tace”

Am sorry afia ban….

It’s ok yawuce Dan nice yakamata na Baki hakuri akan abinda mum Dina ta…

No afia yawuce kaman yanda kikece abar maganar.

Zamewa sukayi NURU na gyara tsayuwa tace”

Bari natayaki jejjera kayanki a dakin kafin agama breakfast muci.

Tayata bubbude kayan tayi suka jere suna fira anan NURU ke sanarwa afia din gobe zata fara zuwa Court Inshallah ita dayake tafara zuwa asibitin kafin wannan 

rigimar ta dakata sai itama tace gobe zataci gaba da zuwa kada tun wuri rashin bada himma yashiga cikin aikin.

Suna gamawa NURU ta fito ta nufi dakinta tayo brush ta sauyo Kaya ta cire na baccin dake jikinta wainda takejin nauyinsu tun dazun agaban afia.

Afia dasuka zauna cin abinci Bata wani samu damar sakewa taci sosaiba sbd tunanukan dasukai yawa akanta musamman na mum dinta da batasan meyake faruwaba a 

gizah din ga dad dinta har lokacin wayarsa Bata Shiga gashi takasa tambayar NURUn dad saidai ta tambayi farhat tafada Mata yayi tafiya baya Nan.

Sosai NURU ke kokarin janta da fira sbd su samu duk su dukan su sake dan sukoma kaman yanda suke wannan sabon yanayin nasu bayayiwa kowaccensu Dadi 

Da Haka dai gurin firar suka fara sakewa suna danne komai tareda qoqarin mantawa kawai ahaka dai har dare yayi suka kwanta washe gari kowannensu ya tashi 

kan lokaci sbd Shirin fara fita zuwa gurin ayyukansu 

Sukai breakfast suka fito NURUn na sanye da white long sleeves da White pencil trauser sai black kimono har qasa sai brawn and white scarf dake kanta da 

takalmi wedges na _Le labo_ sai handbag da Jakarta rigarta 

Afia kuwa cikin jeans da shirt take sai white coat dake jikinta ta likitocin asibiti suka fada mota Edward ya fita dasu aka fara aje afia kafin aka wuce aka 

Kai NURU.

*************

Ranarda jekadi suka iso gizah tundaga shigowarsu padima ta ‘dan kalli jekadi tana gyara zama cikin motar da aka daukosu daga airport tace

Saqona na NURU datace za’a bani ko za’a banishi tun ayau inason hada kayana guri dayane idan ba damuwa.

Waiwayowa jekadi tayi ta kalleta tareda sakin murmushin manya tace”

Babu matsala saqonki a Daren yau Zaki fara karban abinki basai kin damu kanki da tambayawarbama za’a Baki komai dukkanin abinda Kika cancanta.

Murmushi padima tayi tana dauke Kai tareda cewa”

Yawwa dai Ngd Sosai.

Suna Isa har kofar dazata sadasu da sassan Matar maleek ma’ana sassan NURU anan akai parking suka fito Kai tsaye suka shige hanyar suka wuce sassan NURU 

sukabi wata hanya sukai tafiya me tsayi datasaka padima fara waiwaye tana son yin mgna Amma tana dannewa sbd tasamu tafara riqe abinda za’a Bata din tukuna.

Sassan maleek suka nufa suka kusa can baya sosai inda wani boyayyan gurin sirrinsa yake jekadi ta waiwayo tareda kallon padima tana bude kofar tace”

Bismillah shigo daga ciki.

Ba wani tsoro padima ta qaraso tana leqawa ta shige sbd ganin kamar dakin ajiyar dukiyane ta qarasa ciki tana dube dube tanajin matsuwar abata abinda za’a 

Bata ta bar gurin sbd kaman tsoro da fargaban gurin na neman shigarta.

Mintuna biyar ba’ayi ba da shigarta saiga jekadi dauke da ruwa da drinks masu sanyi a tray ta qaraso tana ajiyewa kan table dake dakin tana cewa”

Bismillah.

Dagowa padima tayi ta kalli tray din kafin ta kalli jekadi tace”

Anan ne saqon yake?

Wannan karon jekadi Bata kalletaba tace”

Eh saqon ne za’a Baki idan kinyi hkr Yana isowane.

Shiru padima tayi cikin qaguwa da gagfawarta ta saqon yashigo hannunta tasaki guntun tsaki cikin ranta tareda Kai hannu ta dauki lemun takai bakinta tafara 

kurba ahankali tana kallon kofa tana Jin matsuwarta na qaruwa harta shanye lemun ta dauki ruwama Tasha kadan ta ajiye tareda Miqewa dagakan kujera daya tal 

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button