UBAYD MALEEK 39

dake dakin sai table da kayan adon daki masu kamar zaiba ta juyo tana kokarin komawa ta zauna taji wani irin gumi da zafi zafi me tsanani Yana tasowa daga 

cikin jikinta ta hadiye wani wahalallen yawu sbd bakinta dake gauraya da wani irin mummunan daci ta juyo da sauri tana share gumin fuskarta tana kallon 

jekadi da alamar tashin hankali da azaba tace”

Me Kika bani???

Me kikeson yimin???

Innalillahi wayyo Allah 

Mutuwa zanyi azaba nakeji me tsanani….

Wurgi tayi da dankwalin kanta tana fige rigar jikinta cikin wata mummunar azabar dabata taba Jin makamanciyartaba arayuwarta ta zube qasa tana yagar jikinta 

tako Ina tana cewa”

Dan Allah ki taimakeni

Jikina cikinsa wuta ake hurawa

Dan Allah kibani ruwa 

Zan mutu……

Shure Shure tafara jikinta na rikidewa jajir duk inda ta Sosa Kota fizga saiyayi wani irin kumburi kaman wuta ta koneta a gurin take ta haukace tana Shure 

shuren azaba tana ihun mummunan yanayi Jin takeyi kamar ruwan dalma na sirkuwa cikin jininta da bargonta..

Ihunta yasa jekadi juyawa ta fice daga dakin tareda rufewa ta waje ta cire qaton mukullin ta bar gurin Takoma can kofa daganan ta dauki hanyar zuwa gurin 

Anneti da akaiwa isarwada sakon zuwan jekadi.

Da murmushi Anneti ta kalli jekadi tace”

Barkan jekadi da dawowa lafiya,

Muna fatan anbaro Mana su maleek da mushransa tareda ‘yayansa lafiya?

Da murmushi akan fuskan jekadi cikeda biyayya tace”

Alhmdlh muka barosu Inshallah.

Masha Allah to Yaya bakuwar mushrah?

Da ita kuka dawo dai Ina fata?

Sauke Kai jekadi tayi tace”

Da ita muka dawo saidai tariga ta wuce delah inshallah Bata biyo ta Nanba.

Masha Allah shikenan kije kihuta kin debo gajiyar Kai baquwa da dawowa da ita Dan Haka kije ki huta na tsawon kwanaki shida bakya buqatan fitowa kawo 

gaisuwa nabaki daman hutawa tukuicin Kai baquwar NURU da dawo da ita.

Cikin tsananin farin ciki jekadi tace”

Allah yaqarawa Anneti tsawon Rai da lafiya tareda girma, jekadi godia take sosai da matuka.

Murmushi kawai Anneti tayi tareda gyada kai tana cewa”

Amin.

Tashi jekadi tayi ta fice tana sake miqa godiya.

Tana fita hamdala ta sauke sbd hutunta zaibata ikon rike aikin gabanta da kyau su samu su gano asalin maqiyin maleek da nahaifinsa daya rasu Wanda suka 

shafe shekaru suna bibiya.

Sassanta NURU ta nufa inda takeda babban Palo da daki tareda makeken toilet dinta ware musamman acikin sassan na NURU tareda makeken dakin bayin sassan dake 

gefen nata.

Wanka tayi ta huta taci abinci sai alokacin tasamu ta rintsa dataga tafara aikata aikin kaleeb da maleek wainda zata iya bada ranta akansu.

Washe gari da sassafe ta saci jiki Babu me gani ta nufa gurin padima daukeda abinci cikin kwando tana Isa ta saka mukulli ta bude kofar ahankali tareda 

shigowa ta maida ta rufe ta ajiye kwandon hannunta tana kallon padima da kamanninta suka Gama sauyawa zuwa wani irin yanayi na tsoro da firgici tana fidda 

wani irin azababben Nishi dake fitar Mata daqyar.

Gyaran murya jekadi tayi tana kallonta batareda taji tausayinta ko dayaba aranta.

Daqyar cikin tsananin azaba padima ta dago idanuwanta dasuka kumbura suntum dama fuskarta Baki daya 

Dukkaninta tayi jajir koina jininta.

Da hannu jekadi ta nuna Mata abincin data shigo dashi tana cewa”

Ga abinci Nan kici zai taimaka Miki kadan gurin samun karfin iya daukan  dose din anjima.

Wasu siraran hawayen azabane suka silalo Mata ta gefen ido ta bude bakinta daya kunbura batako iya motsashi daqyar can qasa ta iya furta”

Meyasa? Meyasa akemin Haka????

Numfashi jekadi ta sauke ahankali tareda kallon padiman tace”

Da zakiyiwa kanki adalci tun Baki lalace da yawaba da kin Fadi inda Kika samo wannan garin da kanki Amma nasan burinki da gurbataccen tunaninki bazai Bari 

ki zabi hanyaba.,

Wannan shine aikin da kikaje gidan ‘yar uwarki aikatawa akan mijinta kokuma nace akan MALEEK sbd qyashi da hassada sungama cinye zuciyarki gashi kin samu 

kanki acikin abinda tun kafin kizo duniya yake Dan haka batareda wahalarda sauran rayuwarkiba kifadamun inda wannan garin meriz din yafito yashigo hannunki.

Rintse ido tasake Yi cikin wahala wasu siraran hawayen suka sake gangaro Mata tanason fashewa da kuka batada hali sbd batada qarfin iyawa tanaji tana gani 

jekadi ta fice tasake rufeta cikin dakin dakeda tsananin duhu da zafi ta daga hannunta dake rawa ahankali ta wawuro abincin taga flatbread na alkama da 

dafaffuyar madara 

Jikinta na tsananin rawa takai madarar Baki ta shanye tana Gama shanyewa tasaki cup din tana zare idanuwanta dake firfitowa kaman zasu tsinko jikinta ya 

tsananta rawa ta  kife agurin tana ihun da baya fita ko kadan sbd dushewar murya cikin azaba Dan Ashe anxuba meriz din ciki.

Kwanan padima biyu Ana shayar da ita meriz ahankali ahankali Wanda yagama illata dukkanin jini da gangar jikinta tareda fatarta da duk tagama sabewa Takoma 

Kamar wadda aka tsoma cikin tafasasshen ruwa takai takawo ko motsi batayi Wanda yasa hankalin jekadi tashi ta sbd ganin Kamar padiman zata mutu saita dakata 

da Bata saidai dai gabaki daya padima ta sabule tashiga cikin wani irin mawuyacin hali na azaba tanajinta Amma ko motsi Bata iyayi banbancinta da matacci 

numfashin datakeyi ne kawai Wanda shima cikin tsananin azaba takeyinsa,

Tayi kukan zuci Dana ido Wanda baida amfani sbd dukkanin nadamarta Mara amfani ce tunda yau Bata ganin iyayenta bare ‘yar uwarta Susan halinda take ciki 

bare su yafe Mata ko haqqinsune yakamata yasata cikin wannan mummunan qaddarar.,

A da batada fatan datakeyiwa iyayenta da ‘yar uwarta tabasu tsoro Dan tayi amfani dasu saina Kiran mutuwa yau gata zatayi mutuwar bama ta gataba ta 

wulaqanci wadda taso maleek yayi gashi ace itace zatayi.

Hawaye suka gangaro gefen idonta suna sauka kan fatarta dake radadin azaba tace”

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button