NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 39 – 40

 *_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
             _(ya dace ya gyara kansa)_
               *_Bilyn Abdull ce????????_*
                   *_[39➖40]_*   
…………..Zuwa yamma lik’is Zazza6i mai zafi yarufe Jiddah saboda ciwon da
taji, hannun harya kumbura, Ummace talura danhaka taje inda Jiddah ke a kwance takamo hannun.
    Y’ar k’ara Jiddah tayi tana rik’e hannun Umma da fad’in “Wayyo Umma akwai zafi”.
       “Yanzu nan ciwo kikaji a hannun Jiddah amma kikayi shiru da bakinki? Yanzu daban kulaba haka zakiyita zama dashi? Ga jikinkinan har zazza6i ya sauka”.
     Hawaye kawai Jiddah keyi takasa magana, tsaki Umma tayi tana mik’ewa, yayinda can k’asan ranta ke k’ara zafafa da lamarin Abba, yau gaba d’aya a cikin 6acin ransa ta yini, kai dukama gidan harsu Balu.
      Waya Umma ta d’auka takira Uncle yahya, yace yaje Jigawa amma gashinan a hanyar dawowa.

           Sai bayan Sallar magriba Uncle yahya yazo damai gyara, sosai Jiddah ta jigata da kukan azaba, ga lalurarta, danma yanzu ALLAH ya sauk’ak’a abun sosai bakamar daba.
     Ana gamawa aka bata maganin zazza6i Tasha ta kwanta sai barcin wahala.
   
         Umma suka zauna da Uncle yahya bayan mai gyara ya tafi, bayani taimasa akan abinda Abba yazo yayi yau, sosai ran Uncle yahya ya6aci, ananma yake shaida Mata shima yaje nemansa a kasuwa akace yaje jigawa shine yayo nan gidan ya zubar musu da tujarar su.
     Umma tarik’e ha6a tana fad’in “Anya kuwa Alhaji yanada isashshiyar lafiya Uncle d’insu?”.
       “Wlhy lafiyarsa lau Maman Nafisa, abinda ya shukane kawai yafara girba, dan hak’in yarannan kawai ya ishesa ishara, yanzu haka d’azun Saudah takirani take shaidamin wai yakira mijinta yabashi bashin miliyan ashirin, dan ALLAH Maman Nafisa kijifa zubarwa kai mutunci”.
         Ran Umma a matuk’ar 6ace tace, “Takirani nima wlhy, rasama mizance Mata nayi, dan ni lamarin mahaifinsu yafara fitamin a kai gaba d’aya, jira nake kawai naga yarananan sunsami matsugunni wlhy nak’ara gaba”.
     “Kiyi hak’uri Maman Nafisa, dan ALLAH kibar wannan tunani, ke kamar uwace agaremu, idan babuke wazamu kalla muji sanyi, dagani sai d’an uwana iyayenmu suka Haifa suka Bari, amma kece kika mayemin gurbinsa, idan kin goce ni dawa kuma Zan zauna?”.
       “Uncle d’insu abunne da ciwo, yaufa soyay yamareni gaban Jiddah, badan ALLAH yakawo su Yaruwaiya ba yakake tunanin za’a k’are? Dan wlhy nak’udiri aniyar ramawa daya mareni”.
      Kasama magana Uncle yahya yayi, in banda tafasa babu abinda zuciyarsa kemasa.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

            A police station dai rufe kalifa akayi yanata kuka, kusan a tare suka Isa da Abba, yayi-yayi iya iyawa abashi belin kalifa a sasanta magana amma uban d’an ya rantse sai kalifa yayi kwanan kanta, wasa-wasa har dare Abba yanacan yana fama, sai kusan sha d’aya yabaro station d’in yadawo gida, hankali tashe Hajia Hindu ta tareshi da zancen kalifa, bayani yaymata yay shigewarsa d’aki yabarta tana kuka harda kururuwa.
    Suma sauran yaran duk sunyi jigum-jigum.
          Washe gari dai dole Abba yaje makarantar su kalifa, amma Sam principal d’in saiyak’i saurarensa, acewarsa yanzu magana tana hannun hukuma, miyasa lokacin da suka buk’aci ganinsa yak’i zuwa?.
       Duk yanda Abba yaso nuna musu kud’i abin ya gagara, ga hajia Hindu Nata musu kuka, dan kasa hak’uri tayi saida ta biyosu.
        Kwasa sukayi zuwa station d’inma, canma Sam ba’a sauraresuba, saida Abba yakashe kud’i sosai kafin aka sasanta magana akan Abba zai biya kud’in asibitin yaron daduk wasu abinda zai buk’ata harya warke, aka kuma yiwa kalifa tsakani da yaron.
      Sunje asibitin suka duba yaron, Ashe sosai kalifa yaji masa ciwo kuwa, sun masa sannu suka taho abinsu.
       Aiko wujiga-wujiga suka dawo gida, hajia Hindu ta rungume kalifa tana kuka, hakama su Hassan duk sun rungumeshi da murnar dawowarsa.
      Kan Abba yai zafi sosai, sannan dagashi har hajia Hindu babu Wanda yayma kalifa fad’a akan lamarin.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


             A washe gari Uncle yahya yaje wajen malam Abdul-ra’uff suka tattauna maganar tariyar Jiddah, sosai malam yay farin ciki da matso da maganar, dan sun yanke nanda kwanaki uku kacal.
      Ananma Sheikh Aliyu yazo ya samesu, shima sosai yagamsu dahakan, amma kunya ta hanashi Nuna farincikinsa a gabansu malam. Sai dai shi malam dayasan yanayin d’ansa tuni ya hango farin ciki tattare dashi.

★★★★★

         A ranar da yamma kayan gadon Jiddah suka iso, kayane masu k’yau da tsari dakuma tsada gwargwadon k’arfin Uncle yahya, kowa yagani saiya yaba, saidai idan mak’iyi kuwa.
      Ganinfa abin da gaskene sai jikin Jiddah yakuma sanyi, ga Yaruwaiya tadage sosai take kuma gyarata da tsumata a k’amshi.
       Sheikh Aliyu yana kiran Jiddah su gaisa, yakuma bata hak’uri akan bazai samu sake shigowaba, dan yayi busy da yawa, ga shirin tarewarta ga walimar musabik’ar dataje Saudia wadda malam yace za’a had’a data aurensu.
     Ita hakanma sai yay Mata dad’i, dan dama batason yazo yaga taji ciwonan Na hannunta, sannanma dai tafison su zauna nesa-nesan, shiyyasa jitake inama su Umma zasu yarda a kuma d’aga tariyar. Daka ganta kasan tana tare da damuwa, datasamu ke6ewa ita kad’ai sai kuka, ita kanta Umma dauriya kawai takeyi, su Zarah kam duk sunyi wani sukuku dasu suma, kewar Y’ar uwarsu Na matsuk’ar damunsu.

           Washe gari aunty zulai dasu Aunty Saudah, hannatu suka iso, dan haka aka rankaya gidan Aliyu yoma Jiddah Jere.
     Tarba ta mutunci suka samu dagasu aunty Ruk’ayya da Maimunatu, dan bazama kata6a cewa itace kishiryar Jiddanba, yanda taketa hidima dasu abun gwanin birgewa.
     Dukda gidan Alhaji garba yafi Na Aliyu komai hakan bai hana gidan Aliyu k’ayatar dasuba, dan ba arzik’in bane abin birgewa kawai, zaman kafiya da kwanciyar hankali shine abun buk’ata ga kowacce d’iya mace.
      Tsarin gidan babu ruwan kowa da kowa, dan kowacce kamar 6angarenta daban zamuce, sai dai bawani k’atun k’atunbafa, dan bawani katafaren gida baneba, yanada dai girmansa gwargwadon hali, kuma tsarin yayi, iri d’ayane da sashen Maimuna, babu wani banbanci saina kayan d’aki, komai Na Jiddah pink and White ne, iya gwargwadon iko dolene a yabama Uncle yahya, kayan gadonta d’aki biyun duk aka zuba, kicinma kam Alhamdllh, saidai mak’iyi. Dayake sunada yawa dandanan suka gama, dan zuwa magriba sun dawo gida, sunata zuzuta tsarin gidan, sun nunama Umma video recording d’in da sukayo, itama sosai ta yaba, dad’i kuma ya kamata, dan yanzune hankalinta ya kwanta da auren d’iyarta.
      Koda suka nunama Jiddah k’in kalla tayi, saima ta fashe musu da kuka.
     Aiko dariya suka sanya Mata, ganin da gaske takeyi duk sai jikinsu kuma yay saniyi suka shiga rarrashinta.
          
      Washe garifa dangi suka Fara sauka, zuwa yamma gida yayi taf, dangin Umma danasu Abba, kamar taron farko wannan karonma sai rabuwa sukayi saboda gidan Umma yamusu kad’an.
      A ranar da yamma kuma aka kawo lefen Juddatulkhair daga angonta Sheikh Aliyu maina, suma ammusu tarba ta girma da mutuntawa, kuma kowa ya yaba da lefen Masha ALLAH, dan saidai mak’iyi kam, abin tamkar bana bazawara ba.
        Jiddah dai ko tarinta bakaji a gidan, koda su aunty siyama suka buk’aci ganinta k’in yarda tayi, dole suka hak’ura suna fad’in ai dai gobe iyanzu takusa shiga gidansu.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

         A yayinda ake shagalin tarewar Jiddah kuma shima Alhaji garba yanacan yana shagalin tarewa da sabuwar amaryarsa da aka d’aura aure yau hajia deluwa bata saniba, sai wajen tashin hantsi taga anzo ana kwashe kayan 6angaren Jiddah, dariya tayi sosai tana fad’in “Badole ka kwasheba, da kabarsu su shekara dan itadai tatafi kenan har Abadan”.
      A wajen kwasar kaya masu kwasar sukaci Karo da abinda Hajia deluwa ta sakama Jiddah. Basuyi k’asa a gwiwa ba suka Kira Alhaji garba suka shaida masa..    
       Mamakine ya kamashi, babu jimawa yadawo gida bayan an d’aura aure, kai kawai yake iya jinjinawa saboda takaici, ko tantama bayayi wannan aikin deluwa ne, wato wannan shine yasaka Jiddah haukacewa idan tagansa, shine kuma yasatake masa wari?. Sakasu yayi suka k’ona, itakuma bai Mata maganaba dan yanzu bashida lokacinta, ta amaryarsa yakeyi wadda takasance gogaggiyar Y’ar bariki, dan hajia bariki ma ake kiranta, tafi hajia deluwa komai, idanma kud’ine itama ta Tara, tadad’e tana nunama Alhaji garba so amma yana shareta, hajia deluwa kuwa sosai ta tashi hankalinta lokacin dataji hajia Rahina bariki Na sonsa, dan shige-shigen malamai taitayi dan kar hajia rahina tashiga zuciyar Alhaji garba.
     To a yanzu kuma gashi tashigo batareda ta saniba, ko wane irin zama za’ayi???? kuma?????????.




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

          Jiddah datasha kuka zazza6i ya rufeta ta kwanta, duk hayaniyar ganin lefe da y’an biki sukeyi sama-sama takejinsu saboda barci dake fusgarta, zuwa wani lokaci barcin yay awon gaba da ita gaba d’aya.
      Cikin barci tafara mafarki mai ban tsoro, kafin daga bisani tasamu k’arfi akan Wanda suketa dambe a mafarkin, a fili kuwa tajik’e sharkaf da zufa, ga mazari da jikinta kemata.
       Fannah data shigo domain gwargwad’a Mata lefe da kayan arzik’in da ya sheikh ya zuba ta isketa a wannan hali, jijjiga Jiddah tafarayi tana kiran sunanta, ihunta shine yajawo hankalin mutane sukayo d’akin.
     Da k’yar aka samu Jiddah ta farka, amma saita Fara wani fisge-fisge da gurnani cikin wahaltuwa, numfashima dak’yar take fisgarsa, daga k’arshema saita sank’ame alamar ta suma.
       Ummace ALLAH yabama k’arfin zuciyar d’akko magungunan Jiddah da sheikh Aliyu ke bata har yanzu ta zuba turare a rushi, yayinda Maman Sadiq keta shafama Jiddah ruwan addu’oin a fuska.
      K’ara ta k’walla kafin tafara rawar jiki da zufar dake cigaba da kwararo Mata, bayan kamar mintuna uku saita koma tayi lakwas tamkar ba itaba, saikuma hawaye dake kwarara Mata a fuska. Daga baya kuma barci ya sake kwasheta.
          Uncle yahya da aka Kira a waya ya k’araso, Koda sukai masa bayani sai sukaga ya d’aga hannu sama yana fad’in “Alhamdullahi, ALLAH mungode maka dakabama yarinyarnan lafiya, ALLAH yasa iyakar wahalar kenan”.
     Tambayarsa suka shigayi, nanfa yaymusu bayanin insha ALLAH Jiddah tasamu lafiya daga lalurarta.
     Kowa murna yashigayi, saidai Umma Na mamakin ya akayi haka cikin sauk’i? Kodai Uncle yahya ya d’auki wani matakine basu saniba?. Ganin babu mai bata amsa yasa ta hak’ura, tasan idan komai ya lafa zai Mata bayani.
      Da wannan aka cigaba da shagali.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


         Dukda Busy da Aliyu yayi haka yasamu ya nemi Jiddah a waya saboda duk yau basu gaisaba, amma saima yaji wayar switch up, dole ya hak’ura dan yasan gobe iwar haka insha ALLAHU tana gefensa.

      Baiwar ALLAH Maimunatu, duk yanda kaso gano halin datake a ciki baka isaba, dan ta danne zuciyarta sosai, yayinda kulawa da tattalin da mijinta ke bata ya danne kaso mai yawan gaske Na damuwarta.
      Harkokinta taketayi, danma laulayi yana takura Mata sosai, batajin dad’in jikinta, dauriya kawai takeyi.
       Yauma gaba d’aya da daddare bayan yadawo nasiha yayta Mata da lallashinta cikin kalamai masu sanyi da saka zuciya nutsuwa. Hakanne yasakata itama bashi dukkan farin ciki batareda ta d’auki fushi Na tunanin gobe iyanzu yana tare da amaryarsa ba.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨.

           Washe gari Jiddah ta tashi garau da ita, wannan Yakuma tabbatarma dasu Umma lallai an dace kam. Yau tunda aka tashi da gyaran jikin Jiddah aka fara, dan sunayin sallar asubahi aka Fara zuba Mata kunshi da kitson Bare-bari d’an asalai (barbarawa????????⛹‍♀), tayi k’yau harta gaji.
             Sai dai daka ganta kasan batada sukuni, magana kad’an za’ai Mata ta6are baki tana kuka.
        Y’an uwama saisuka koma tsokanarta, musamman abokan wasa, saisu Aunty Sauda ne ke kareta.
      
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

           Abba dai duk wannan hidimar da akeyi baya gari, dan tun Randa aka fiddo kalifa daga station suna dawowa yahad’a kaya zuwa Abuja wajen wani Alhaji Sammani Moddibo, abokinsane amma yanzu ya haye dan d’an majalisane a Adamawa, Da Abba yabuga tunaninsa yagama yaga babu wajen mafaka, danya Kira Mijin y’arsa Sauda danya ranta masa kud’i ALLAH ya tak’aita wahala Sauda ta d’aga sannan wayar na agunta, saida yagama fad’ar buk’atarsa sannan tace masa “To Abba ai nice, Ashe dama y’a mace nada amfani da Rana? Ai nazata bazakama ta6a tunamu a cikin y’ay’ankaba balle kabiyo mazajenmu da buk’ata”. Batajira cewarsaba ta yanke wayar taredayin blocking d’insama gaba d’aya, shinefa takira Uncle Yahya da Umma ta sanar musu.
        Wannan Abu da Sauda taimasa ba k’aramin Sosa masa zuciya yayiba, dan haka yashiga tsinarta yana had’a kaya, aranar yawuce Abuja.
      Harkuma yau da Jiddah zata tare bai dawoba, ya iske Alhaji Sammani bayanan, amma saiya zauna jiransa saiya dawo, dan ance tafiayar kwana biyar zaiyi, to aganinsa dayayi wahala biyu bai dawoba ai gara ya zauna ya jirasa kawai, yama huta da bala’oin daya baro a cikin kano.
     Auren Jiddah kuwa yana komawa yabiya Alhaji garba kud’insa saiya tsinkashi, danyayi alk’awarin tunda Yaruwaiya taci zarafinsa gaban y’ay’ansa saiya huce akan Umma, sannan saiya shukama Uncle yahya rashin mutuncin da ko’a hanya bazai sake nunashi a matsayin d’an uwansaba.


????????‍♀Aɮɮa ʍɨҡaҡɛsօռ ʐaʍaռɛ աaɨsɦɨռ?.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


*_11:00pm_*

        Harabar makarantar su Jiddah tagama cika taf, bakajin komai sai k’ira’ar alkur’ani mai girma, tarone daya tara manyan bak’i daga yankunan arewaci da kudanci.
    Dan taron an shiryashine da manufa biyu, Na murnar nasara da Nageria tayi a gasar diniya, dakuma murnar taya hazik’in malami Sheikh Aliyu da Amaryarsa Jiddah tauraruwa a daular musulinci.
        Jiddah na sanye cikin k’yak’yk’yawar sutura, ko ina Nata a rufe ruf, ko tafin hannunta da k’afa baka gani, fuskarta kam tamkar kullum tana lullu6e da nik’ab, sai sirrin k’amshi mai sanyi take fitarwa.
      Madina ce a kusa da ita sai sauran d’aliban ajinsu.
        Ahakanma hawaye taketayi, dukda ayau tanajinta wani sakayau tamkar an sauke Mata kaya, ko kad’an batajin komai game da maza………
        Sassanyar muryarsa data farajan k’ira’ar alkur’ani cikin suratul Bak’ara ce ta katse tunaninta, cikin fad’uwar gaba da bugawar zuciyarta sauri-sauri ta d’ago ta kalli saitin inda muryar ke fitowa.
        Zaune yake a cikin kujera 1Seat, hannunsa rik’eda microphone, yana cikin shadda wagambari kalar sararin samaniya (skyblue) harda babbar riga, hularsa da takalmansa ma duk kalar shaddar saidai su masu duhune, babu abinda ke fita tattare dashi sai wani annuri Na kwanciyar hankali, yayi wani fresh dashi alamun komai yana tafiya masa dai-dai. Yau shine Rana tafarko data samu zarafin masa kallon tsaf, Masha ALLAH gwargwado Sheikh Aliyu maina yanada k’yansa, Abu mafi k’awata taswurar kamilalliyar fuskarta shine tambarin salla dan6arere dake a goshinsa, sai sajensa zuwa gemu daya kuma fidda sirrin nagartarsa da cikar kamala musamman dayasha gyaran fuska da aski a yau. Harya gama karatun yafara Addu’a Jiddah batasan anayiba, saida aka kirayi sunanta sannan Madina ta zungureta ganin batai ko motsiba.
      Babu shiri tadawo hayyacinta kafin tamik’e bisa taimakon Madina. Itace taimata rakkiya har inda ake buk’atar ganinta.
     Tunda aka Fara shelanta sunanta yake baza Ido yaga ta ina zata 6ullo ne? Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke daya ganta tamkar yanda yay fata, danshi mutumne shi mai kishi sosai, dan taronnan da farko k’ok’arin hanata zuwa wajen yayi, kasancewarsa komansa yakan nema shawarar malam kafin ya aiwatar saiyaje ya sanar masa. Malamne ya lallashesa akan yabarta taje yaudai d’aya, kodan manyan mutane dazasu halarci taron, dan kowa zaiso ganin wannan gwana data samo mana nasara. Da wannan malam yaci k’arfin sheikh Aliy………
      Bai ankaraba yajiyo zazzak’ar muryarta na jawo ayoyi cikin kwarewar larabci da takatsantsan. Lumshe idanunsa yayi bugun zuciyarsa Na k’aruwa. Wajen yayi tsitt bakajin komai sai ajiyar zuciyar jama’a.
      Tuni muryar Jiddah ta karye alamun kuka takeyi, wad’anda sukasan hali su malam Abdul’ra’uff dama sunsan za’a rina, tuni ta karya zuciyar jama’ar wajen, wasu sai sharce yawaye sukeyi.
            Saida takai har k’arshen suratul Al-Anbiyaa kafin a dakatar da ita. Wajen zamanta takoma itada madina, dad’i yasaka Umma share hawayen da suka wanke fuskarta, itakam kullu yaumin tana alfahari da haihuwar y’ay’a Mata, babu abinda zatacema Ubangiji saidai godiya.
       An fara gudanar da abinda ya tara mutane, Wanda dukkan manya sun yabama Jiddah dajan Addu’ar fatan alkairi dazaman lafiya nahar abada itada gwarzon mijinta tauraron duniyar musulunci, duk kuma k’yautar data samu shike zuwa ya kar6a Mata. Mutane sai k’usk’us suke akan hakan, yayinda y’ammata irinsu Tawan (Miss Xoxo????????) suketa k’yasawa, jisuke inama sune sukeda wannan Hafizin masani a gidauniyar addinin islama.
      Sak’on jawabi daya kamata Jiddah tayi Na godiya shine yakar6a microphone yayi a maimakonta. Dan yayi alk’awarin babu mai sake jimasa muryar mata gaskiya, karatunma datayi jiyay tamkar yaje ya hanata, da k’yar ya iya tausar zuciyarsa harta gama, shiyyasa yaturama malam mustafa massage akan karsu sake kiran Jiddar, duk abinda ake buk’atar tayi akirashi a maimaikonta.
      Murmushi malam mustafa yayi, dan yasan wanene Aliyu akan kishi. Dan haka yabi dokarsa, komai za’a buk’aci ganin Jiddah saiya Kira Aliyun.
        Bayan andawo salar zuhur malamai suka fara gudanar da lecture mai taken *_GIDAN AURENMU_*, wadda dai anyitane ta musamman domin ango da amarya.
     Jiddah dai Tasha kuka acikin Nik’ab harma kanta namata ciwo.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button