NOVELSUncategorized

NIDA AMARYATA 7-8

7⃣-8⃣

____ gadan gadan ta nufi Alhajin yayin da Hajiya Hafsa ta tsaya kallon ikon Allah,ganin da gaske take yasa Alhaji Sani fadin “Dakata!,baza’ai wannan rashin mutuncin Dani ba,nawa ne kudin marinta da nayi?”


Dakatawa tayi tare da sakin ajiyar zuciya ta furta,” ka nemawa kanka sauki,kudin dai mari da kayi duk da ban San adadin su ba,zaka biya Dubu dari biyar,sannan kudin kukan da kasata tayi,shima ka bada dari biyar din,duka miliyan Daya kenan”.

Batare da yakara cewa uffan ba ya mike Yana tangadi ya haura saman,babu Bata lokaci sai gashi dauke da check da biro,Yana shirin fara rubutawa,Nihila tace “Aunty hama Kinga fa bai fito da kudin ba sai takarda,”a wulakance Aunty hama ta kalleshi tare da fadin,

“Ya Naga haka?,maimakon kudi sai takardu Kuma?

Dagowa yayi da rinannun idanuwansa,Wanda tsananin bacin Rai da ciwon kan dayake ji yasa suka Kara kankancewa tare da rinewa zuwa jajaye,kawai Dan a halin dayake ciki ne yanzu,baya bukatar hayaniya amma zaiyi maganinsu gaba,Dan haka cikin murya kasa-kasa ya furta,” Zan rubuta Miki check ne kije banki ki cire,”

“Tab wallahi Aunty kada ki yadda,daganinshi tsinannen wayo gareshi,inba haka ba Ina yaga bankin dazai Tara har miliyan Daya a ciki,inagama irin fa nakin nanne da kike Tara kudi a ciki,in zakimin dinki sai ki fasa,to ya dauko ya kawo Mana Mana da kanshi,salon mu dauka da kanmu,yayi Mana sharri yace munmai Sata,to dai mun gano wayonka,” lol….

“Tabbas ko kinyi gaskiya,so yake ya kifar dani,to yanzu ma Ina bankin dazai wani dauki miliyan Daya,kaga kawai bani a hannuna”.

Bai ce dasu kala ba,Dan shi a halin yanzu Bai bukatar surutu,Dan haka ya mike ya haye saman,yadan jima,sai gashi ya dawo dauke da kudin,cikin leda ya Mika musu,Hajiya dake zaune,wadda ta nemawa kanta wurin Zama Dan ganin ikon Allah,yasa ta Kara gyara Zama,tana murmushi Dan taga abinda yafi karfinta.

Yana Mika Mata ta warce,tare da kunce gyalen datayi damara dashi,ta yafa saita nufi hanyar fita,Nihila ce ta shiga kwala Mata Kira Amma taga ko waiwaye Dan haka ta daura damarar binta.Tana Isa bakin kofar sukayi kacibis da ita,ta dawo tare da rangada sallama.
Babu Wanda ya samu zarafin amsawa,da murmushinta ta karaso falon,tare da rike hannun Nihila ta shiga shafa kanta tana murmushi,ita kanta nihilar kallon mamaki take bin Aunty’n tata dashi ganin ta shigo da wani yanayi,sabanin Wanda ta fita dashi yanzu.

“Ah ah! Kaga amarya a gidan Alhaji Sani,na kwana da kewarki sosai ‘yar Anty,shine fa na kasa hakuri na biyo ki da sassafe,dan in ganki,Ah ah Alhaji Kuna Nan Ashe,ai ban lura ba Sam,ganin hantar ‘ya’ya ya makantar Dani,hajiya sannu da hutawa”.

Daga hajiya har Alhajin kallon ikon Allah suka tsaya Yi,inda Basu Gama mamaki ba suka ga taja hannun Nihila tare da fadin,”muje dakinki Inga muhallinki,daga Nan inji kanun labarai,”duka da ido suka bita har suka bacewarsu,yayin da kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa.
   Hajiya mikewa tayi batare da tace dashi tasa Kai ta shige daki,ko ta kanta be bi ba,ya mike ya haura zuwa dakinsa,cike da takaicin wanna aure da yayi,Wanda yake ganin zai more,domin duk auren da yayi babu Wanda ya kashe kudi kamar wannan,gashi Babu nasara,domin duk inda yayi tsammanin samun amaryar tasa,ya dauka yadda take da kyau da Kuma yadda jikinta yake,zai same ta yadda yayi zato,ga wayewa ga ilimi,ga Kuma iya soyayya,to amma duk bako Daya,to dawa yake waya kenan a da can kafin aurensu? Tabbas dai itace a hoton da Alhaji Kabir ya Nuna Masa,shiyasa Koda ya Bai ganta ba yasan ya taki sa’a,duk da Basu hadu ba sai a gurin dinner dinsu ta farko,kallonta kawai da yayi da farko Saida yayi tunanin ba mutum bace Dan tsananin kyanta Daya gani,da kuwa ya tabbatar ita din mallakinsa ce,Saiya tabbatar da yafi kowa sa’a Kuma yanzu yayi aure.

Haka ya karasa dakin zuciyarsa fall da tunani,Yana shiga magani ya nema yasha na ciwon Kai ya kwanta Yana rufe ido Dan so yakeyi yayi bacci Dan bakinsa,Daya kumbura zuwa yanzu,ga Kuma kansa dayakejin yayi Masa nauyi dundurum,ya jima kafin bacci ya kwashe shi.

***
Su kuwa su Nihila suna shiga dakin Aunty hama tace,”maza cire kayanki inyi Miki wanka,ke haka akeyi banace kina tashi da sassafe kiyi wanka kiyi kwalliya kisa kayan da farida ta Baki ba jiya”,

“To ai nayi wanka Aunty”

“A hakan? Ke ban son shashanci maza muje inyi miki,”.

Ba musu kuwa Nihila ta tube Aunty ta Fara Mata wanka,dukansu ba alamun damuwa a tattare dasu,sosai ta dirjeta Koda suka fito kwalliya me kyau ta tsantsara Mata,sannan ta shiga tambayar ta abinda ya faru tsakanin ta da Alhajin,ba abinda Nihila ta rage Mata duk Saida tayi mata bayani,inda bayan ta Gama Aunty hama ta kalleta tare da fadin,”ke wace irin shashasha ce,bana fada Miki abinda yakamata kiyi ba,kice shirme Kika tsaya yi agaban kishiyar taki?

Cuno Baki Nihila tayi,tare da fadin,”bake kikace in ya yimin abu in dinga yaba Masa ba,shine fa na Fara yabonsa ya tsinka min mari.

“Dan gidanku ba dole ya mareki ba,kin Kama yin sakarci,daga ke sai shi nace ki dinga yaba Masa inyayi Miki Abu,Kuma komai yace kiyi nace Miki Banda musu”.

“To shikenan na daina,amma Aunty kudin da Kika karba fa dazu,me zakiyi dasu?

Hmmm “kema ai kinsan inda zasu tafi,kudin da har yanzu ko kwata bamu hada ba na abinda ake bukata,Kinga kedai kawai kiyi abinda nace kinji,ta fada da fuskar tausayi”.

Duk da Nihila yarinya ce,Amma ta fuskanci Aunty’n nata tana cikin damuwa,

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button