WA ZAI FURTA 3

???? *WA ZAI FURTA?* ????
0⃣3⃣
*TUKUICI NE GA AUNTY RABI ALLAH YA KARA ARZIKI DA RUFIN ASIRI*
*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*
*Domin ki…. blood sister khadija Dahiru wowo miji na gari I pray my besty*
*DAYA TAMKAR DUBU AL’AMEEN ZUBAIRU* TANNY ALLAH YA RAYA MIKI YARON NAN YA KARA MISHI KYAU DA KWARJINI????
*Federal University dutsinma*
Tunda aka dawo bai yarda sun hadu da Bilkisu ba har suyi wata magana. Tana ta kokarin su hadu Amma yaki yarda.
Suna tsaye ita da su favour bakin ajin da zasuyi darasi ta hango Suleiman na taho wa, tun daga nesa suke ma juna dariya saboda Yanzu sun Zama tamkar *Wa da kanwa*, Anwar har yazo ya wuce ta gaban ta bata ganshi ba amma Shi Suleiman man din ya hango shi.
Yana karasowa malamin Shima ya iso haka suka rankaya zuwa aji.
Ko Zama Yanzu kusan tare sukeyi.
Har Yan class din sun Fara lura da shakuwar su.
Ya fakaici idon malamin ya Fara mata magana kasa kasa.
Wai Bilkisu kinsan Hamza Yusuf din say ake nema ajin nan Anwar ne?
Ta zaro ido *Anwar*?
Eh wallahi. Jiya gaba na ya amshi award din first class da Kuma overall award ina kallon sa yayi saurin boyewa ya bar hall din da sauri.
Ta rike baki. Innalillahi, wallahi sai na mishi magana naga wannan semester din ma tunda muka dawo sai wani shareni yakeyi.
Hmmm, ai da yake kece, Amma Anwar inba ke ba waye ke mishi shigar kawara duk makarantar Nan. Kinsan girman kansa, jiji da Kai da kuwa maida kowa banza yasa aka tsane Shi wallahi ya cika gadara……. Duk yaji dashi nikam daga yau wallahi ya shiga uku dani.
Ba abinda nake nema wurin sa inba karatun ba…..ta katse shi.
Hmmm Hana wallahi nayi mamakin *Business finance* din last semester, bana fada maka cikin mintuna da Basu wuce talatin ba ya gama kusan questions 4 kowa na kuka da question one amma Shi duka yayi. *B* fa gareni course din Kuma wallahi C A da 22 na shiga……ohh ni *Balky* ai wallahi ya shiga uku dani.
Suleiman man dai sai dariya yakeyi yace idan kin kwaso wurin sa Kya ringa koya mun….tabbbb tare zamu je kyaleshi ai wallahi sai na fitine Shi ga wannan semester din kurar ta tafi ta aji daya.
Daya ke Anwar din Yana ta gefenta sai kawai ta yi ta kallon sa.
Tun bai lura har ya fahimci tana kallon sa. Ya Dan juyo suka hada ido ta balla mishi harara Shi Kuma sai ya kawar da Kai Yana murmushi kawai. Haka sukayi tayi da sun hada ido sai yayi murmushi ita Kuma ta harareshi.
Yana ta sake sake cikin Rai *Kuma yau me nayi Ni Hamza* bana iyawa rigima da fitinar Yarinyar can. Ya kawar da Kai bai yarda sun Kara hada ido ba har aka gama.
Hankalin ta na kansa yana mikewa itama ta Mike.
Abinka ga namiji kafin ta sunkuya ta dauki jaka har yabar ajin. Da gudu tabi ta kofar baya kawai sai dai ya ganta gaban sa.
Gaban sa yayi mummunan faduwa Amma miskilancin Anwar bai yarda ta gane hakan ko a fuska ba hasali ma sai yayi Yar dariya *Hajia Bilkisu an tashi lafiy?*
Ta rike kugu To yau Allah ya Kama ka, Ashe Kai ne *Hamza Yusuf*…….. Har ga Allah ya Dan razana. Amma a zahiri sai kawai yayi dariya duka kumatunsa suka lo6a ….inji wane makaryacin? Ya fada Yana dan waige waige kada sauran Yan aji masu fitowa suji,
Wallahi Kaine *Hamza Yusuf*…. Ta fada tana hararar sa. Tana matukar bashi dariya saboda ko gida bai taba samun Wanda ke mishi magana Kai tsaye Babu shakka ba irin Bilkisu.
Yadan Sha mur Yana Dan zare mata ido ke ni bani bane ya gitta zai wuce …..Tasha gaban sa da sauri tare da ware hannuwa ba inda zakaje sai ka fada mun wanene jiya aka bashi kyauta ya boye ya gudu?……tuni hankalin mutane ya dawo kansu an Fara fahimtar meke faruwa.
Ya zaro ido….. Ke ni bani bane….. Wallahi Kaine.
Naji nine yanzu meye kike so? Ya fada Yana Yan waige waige kamar marar gaskiya. Zaka ringa koya mun karatu wallahi don bazan kyaleka ba….shine damuwar? Ya fada cikin kosawa, shikenan duk lokacin da kika shirya Zan nuna Miki. Ya wuce da sauri ya barta tsaye.
Suleiman ya karaso kin dai gani ko?
Kyaleshi ai wallahi na daina wahala daga yau addabar sa zanyi.
Nan wuri ya rikice da surutai kowa na mamaki.
Tun daga lokacin kimar Anwar ta Kara karuwa duk masu Jin haushin sa suka daina. Matsala daya ce Babu Mai iya tunkarar sa da maganar koyo duk ana Jin tsoro da shakkar sa.
Tun daga lokacin Bilkisu ta dami Anwar ya rasa yanda zaiyi da ita ba abinda takeyi mishi sai terere kowa Yanzu yasan wanene Shi , ya rasa dalilin da baya son mata wulakanci kamar yanda yake ma kowa.
Ko lecture za ayi Mafi yawan lokuta sai ta zauna kusa da Shi sai dai yayi ta dariya.
Na kusa dashi mamaki kawai sukeyi yanda baya hantarar Bilkisu ko kadan don ko su din lallabashi sukeyi.
Satin da ya kasance daga Shi sai na yin first C.A sun fito lecture seven to nine ( 7-9 ), Yana tsaye ta fito da sauri don kada ya gudu sakamakon daya ce kawai garesu a Ranar.
Anwar muje ka koya mun *Math for Economic* din nan ban gane komai ba gashi jibi yace Shi zaiyi nashi test din.
Duk Wanda ke wurin sai da ya kalli Bilkisu cike da mamaki yanda take mishi magana Kai tsaye haka, Sam bashi ma take kallo ba ko lokacin da takeyin maganar hankalin ta naga jakarta tana saka littafin da suka gama, yayi Dan murmushi ba dai Yanzu ba ko? Saboda ko break banyi ba yunwa…… Ta dago Kai da sauri Nima banyi ba ai idan mun gama duk ma tafi muje muyi.
Ta nuna mishi hanya wuce muje wallahi yau ba inda zaka je……bai San lokacin da ya kwashe da dariya ba Yana ganin karfin halin yarinyar nan sosai, zai Kara magana ta rike kugu tare da tafa hannu kasan Allah ba inda zakaje…… Wuce kawai.
Naji muje yayi gaba ita Kuma tabi Shi a baya. Duk illahirin wurin binsa akayi da kallo ana wani irin mamaki.
Shi ya Fara Zama kafin ta zauna.
Yawwa ko Kai fa….ai ka gama shiga uku dani watan Kaine Mai kokarin aji shine ka mayar damu samnoni ko?
Dariya kawai yakeyi, tana surutai tana fiddo littafi da calculator. Ta Mika mishi biro da doguwar takarda ..ungo Fara daga farko…..
Dariya yakeyi sosai …..daga farko Kuma? Ki dai fadi abinda baki gane ba.
Ni ban gane komai ba.
Ban yarda ba Allah nasan kina son wahalar Dani ne kawai gashi yunwa nake ji walhi.
Ko me kakeji yau muna Nan sai ka koya mun kawai Fara.
Ya bude littafin to bari mu gani ko na iya.
Ta bishi da harara
Yayi murmushi yace seriously.
A hankali ya Fara mata solving dalla dalla. Dayake Bilkisu na da kokari da saurin fahimta hakan yasa bai wahala ba nan da Nan ya fahimci lallai tana da basira saboda da yawa idan Yana koya ma wasu sai su kusan awa hudu bisa example biyu. Akasarin Bilkisu da Mafi yawan formulas din ma ta haddace su idan yanayi da ka take kawo mishi su.
Ya kalleta hajiyar dai ashe guruwa ce ko? Ya ajiye biro gaskiya na gaji wallahi duk kin iya kina son bani wahala ne kawai ko Bilkisu?
Ta Dan sunkuyar da Kai haka kawai taji Yar kunya ….wallahi a’a ban iya ba.
Yabi fuskar ta da kallo Yana Kara kallon yarintar da ke cike da kyakkyawar fuskar tata.
Ke ni yunwa nake ji gaskiya ya fada Yana rufe littafi.
Dan Allah ka taimaka saura fa biyu da mun gama sai mu tafi Zan siya maka break idan mun fita waje.
Au Zaki biyani ne?
Ta zaro ido wallahi a’a naga hostel zaka koma gashi har Sha daya ta kusa, Kuma yaushe kaje ka nemi abinci?
Ke Kuma fa?
Ni indomie zanci dana koma daki.
To Nima ita zanci. Ya fada Yana ci gaba da rubutu,
Ba damuwa Zan siya maka wurin Abdul Mai shayi na Nan waje ai nasan mutumun ka ne…….da sauri ya kalleta waye ya fada Miki?
Tayi Yar dariya ai Ina wuce ku ta wurin Mafi yawan lokuta.
Ya Dan harareta ke kin samun ido ko?
Ta kyalkyace da dariya Wai ma…..
Eh Mana.
Rabi labari haka suka gama duk idanun sa sunyi ja….Nan da Nan ta fahimci lallai baya da jimirin yunwa yanda har ya Fara galabaita.
Tare suka jera suna tafiya, baka da jimirin yunwa ta fada tana Yar dariya.
Ya danyi murmushi yunwa nada sabo ne?
Eh Mana Amma ga jaruman maza.
Dariya yayi sosai kafin yace naji ni ba jarumi bane ba.
Eh, ta fada tana murmushi
Ke ni sai anjima ya fada tare da yafito Dan mashin.
Ta zaro ido Ina zakaje?
Hostel…..
Indomie din fa?
Na gode….
Wallahi baka Isa ba , Dan mashin din na zuwa tace malam tafi…..ta kalleshi Allah sai na siya maka break kafin ka tafi ko muyi rigima.
Yau ni naga ta kaina….ya fada cikin zuciya.
Ya kalleta, kiyi hakuri da wasa nakeyi na gode,
Ni ban gode ba kawai muje ta nuna mishi hanya.
Dariya ma ya kamayi.
Haka suka je indomie din akwai layi tace kaga kada mu jira zo muje…. Yace to.
Bin ta kawai yakeyi yana kallon ikon Allah sai sauri takeyi suka zagaya babban restaurant din wurin duk yafi ko Ina kyau da tsada, tayi mishi take-away na chips and eggs aka Sanya mishi salad da sos din hanta sannan ta siya mishi gasasshiyar kaza daya da maltina biyu da Madara. Yana tsaye bakin kofar Daman ita kadai ta shiga. Ta fito da sauri tana ta wurga ido kafin ta hango shi can jikin bango…….barkan ka wallahi na dauka tafiya kayi yau da kaga tsiya.
Kallonta kawai yakeyi Yana Yar dariya.
Muje ka hau mashin din zaka shigo anjima school da karfe 4? Ina son ka koya mun *Human resources* ya danyi jimmm….. To bani tunani Amma Ina ga Zan shigo.
Ta fiddo waya samun no. Ka in kiraka kada ka shanya ni kamar last time. Yayi murmushi duk jikin sa yayi sanyi ya ce okay rubuta….. Yana fada mata Yana kallon fuskarta.
Yana Gama fada yace Shi Suleiman bazai koya Miki ba?
Eh bazai koya ba idan ya iya zance Kaine?
Ta hayayyako mishi. Ya kyalkyace da dariya Allah ya bada hakuri. Daidai lokacin da ya tare Dan mashin. Sai da ya hau sannan ta Mika mishi ledojin sannan ta Mika wa Dan mashin din naira dari tace hostel zaka kaishi. Duk meye kika ciko mun anan?
Malam ku tafi kaji…ta kalleshi tana Yar dariya na gode kwarai Allah ya Kara basira sai mun hadu anjima…….kirjinshi ya halba da karfi Shima ya bita da murmushi kawai. Sai kawai ta daga mishi hannu. Hakan Shima ya mayar mata Yana Jin wani masoki na sukar sa………..shi kadai yasan yanda yakeji a zuciyar sa, tana tafiya tana tunani da surutai a zuciya, a gaskiya yau ta Kara tabbatar wa da kanta Anwar na ganin mutuncin ta da kima saboda cikin karfin hali tayi attacking din sa tayi tunanin zai ki yarda kamar yanda yake ma kowa wulakanci.
Shi kuwa Yana zuwa hostel ya baje abincin dakin a cike Yan zaman jiransa kowa ya bude baki Yana mamaki lokacin da yake fada musu Bilkisu ta siya mishi. Bashir ya ce Wai Kai oga anya tsoron yarinyar nan kakeyi ne naga ba Wanda ke maka shigar kawara irin ta kana mata biyayya, dariya yayi kafin yace *ya na iya da Bilkisu*? Wallahi bana iya wa rigimarta ko baku lura ita Sam Bata tsoro na ba?
To ka dai bi a hankali domin Dr Dan Musa da alama Yana ciki wallahi ya gane kana kusa da ita haka zaka. ……mtsew bai iya mun komai wallahi. Ina ga Suleiman ya kamata ku ja ma kunne ba nima ba domin Shi ke binta Ni Kuma tana Bina …..ya lunkuma nama baki ya kallesu ..hope Kun gane karatun..
( Shin Wai wanene Anwar wacece Bilkisu? )
*********************
*KADUNA RIGASA*
Yaran duk sunyi barci.
Tayi ma falon kallon ta natsu …..lallai akwai aiki haka ya hada mata aljannah duniya?
Ya kalli ko wace kafin ya tsaida ido ga Amira ya Fara magana a hankali.
Alhamdulillah dukkan godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya kawo mu wannan lokaci, kasancewa dare ya Fara yi Zan muku bayani Kai tsaye abinda ya tara mu a Nan.
Amira kece babba dake Zan Fara ga Ummi, kiji tsoron Allah ga dukkan al’amuran ki akanta ki dauketa tamkar kanwarki Salma, ki sani cewa kema Ummi Amana ce a wurinki kamar yanda dukanku kuke Amana a gareni. Babu wacce tafi wata a wurina sai wacce ta fi mun biyayya da tsare dokokina, tabbas ko wacece cikin ku zata fi Power ban baku a boye ba, Zan yi kokarin adalci a gareku Ina rokon dukkan ku duk wacce taga za a tauye mata hakki ko nayi kuskure ko akasin haka na baku damar nuna mun hanya domin ko wane Dan Adam ajizi kuma wasu a wurin da sukeyin kokarin yin dai dai suke ba dai daiba.
Bana son gulma , bana son Jaye Jaye abokai da yawan fita yawo marar amfani.
Ke Kuma Ummi ga Amira Nan, ki bata girma kamar sailuba bana son raini, rashin kunya da tsageranci. Tabbas na zauna da Amira nasan halinta don haka ki bita a sannu ku zauna lafiya. Duk abinda ya shige Miki na gidan nan ita Zaki tambaya tunda ni ba mazauni bane.
Da ita Zaki zauna kiji dadi ba ni ba saboda tafiya Zan ringa yi ina barin ku.
Ina da Yara, ko da wasa kada ki zagesu domin ba a zagi a gidan nan, idan sun Miki laifi kiyi musu duk hukunci amma banda zagi.
Amira dai tunda ta sunkuyar da Kai bata dago ba tana ta karanta addu’o’i a zuciya, Ummi din ma ce ke ta Yan wurge wurge.
Sai maganar kwana, a musulunce zanyi kwanakin da aka halatta a dakin Ummi a matsayin ta na budurwa daga Nan ko wace Zan ringa kwana biyu biyu hakan ya muku ?
Duk sukayi shiru…….Amira ya muku?
Ta dago Kai umm hakan yayi ko Ummi?
Ta Dan yatsina fuska ..um.
Da kyau!
Maganar abinci Kuma duk Mai aiki ita zatayi abinci, Ummi tsarina a gidan Nan ko Ina Nan ko bana Nan karfe Sha biyun Rana ya zamanto kin Gama abinci saboda Yara da masu gadi da Kuma sauran mutanen gidan.
Bana son kwauron abinci a ringa dafawa a wadace, tun daga safe har dare.
Amira zata Miki bayanin quantity din idan Kun zauna.
Ba wacce zanbi dakin ta lokacin kwananta duk ranar aikinki Zaki sameni sashena ban yarda da raba kwana ba Koda munyi fadan soke soken wuka…..
Ya kalli Ummi wannan shine tsarina. Duk wacce nayi ma laifi kafin ta tsiri yin fushi dani ta Fara sanar Dani idan har nayi bisa kuskure Zan bata hakuri, idan Kuma akasin haka Zan Fadi dalilina.
Duk Mai bukatar abu ta tambayeni Kai tsaye domin nine mijinku, idan anzo muku da magana akaina ku Fara sanar dani da Kuma Wanda ya kawo maganar ku fadan wanene.
Idan cikin ku wata keson haddasa fitina ta kawo muku gulmar daya to ku tsaidata ku kirawo wacce ake maganar kusanya ta maimaita a gabanta zakuyi maganin munafukai.
Ina fatan duk kun gane?
Wacce keda magana tayi…..duk sukayi shiru.
Ya Mike Ummi jeki Ina zuwa……kamar jira takeyi ta Mike.
Ya Mika wa Amira leda uwargida ga taki kazar…….wayar say tayi Kara ya ganka a kunne hello……..na’am hajiya…..Nan ta fahimci mahaifiyarsa ce. Ya yahuto ta da hannu alamar tazo ta rufe kofa zai fita Yana ci gaba da tafiya.
Yana fita ya Sha kwana ya latse wayar daman fakaitar idon ta yayi ya latso wakar saboda Shi baisan yanda zai mata bankwana ba. ( Namiji?…..)
Tana rufe kofar ta duke a wurin tafara kuka na ban tausayi….( Kishi kumallon mata…..)
Ina bada hakuri Dan Allah…….
*zainab wowo ku muku fatan alkhairi*……✍????????????