Ya amshi kudin ne da sunan zai siya dabbobin da za a yi yanka da su don bakaken aljanu su yi musu aiki, bayan ba shi kudin ya nemi shi ya rasa.
Ganin haka ne Adamu ya kai kara wurin ‘yan sanda daga nan aka kama mutumin da ya hada shi da bokan, Ado Mohammed, don ya bayyana inda bokan yake Jihar Adamawa.
Ana zargin wani boka, Alhaji Bala da damafarar wani dan kasuwa, Salisu Adamu, Naira Miliyan 1.3, kamar yadda The Punch ta ruwaito.
An samu bayanai akan yadda wani Ado Mohammed na Sabon Layi da ke anguwar Gombi a karamar hukumar Gombi da ke Jihar Adamawa ya hada Adamu da bokan.
Bala ya yi wa Adamu alkawarin buga masa N500m bayan ya amshi N1.3m a hannun sa don a samu nasarar yin tsafin cikin gaggawa, kuma ciki za a siya dabbobin da za a yi wa aljanun da za su yi aiki yanka.
Bayan wani lokaci, Adamu ya ji shiru daga wurin bokan wanda ya sa ya fara zargin akwai lauje cikin nadi hakan yasa ya samu Mohammed don su tattauna, rahoton The Punch.
Tare suka je gidan bokan da Mohammed
Bayan shi da Mohammed sun nufi gidan bokan da ke kan titin barikin sojoji a Jimeta suka ga ya yi layar zana.
Daga bisani Adamu ya kai korafi sashin binciken sirri, SIB na ofishin rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa.
‘Yan sandan sun kama Mohammed don su yi masa tambayoyi. Kuma yanzu haka an gurfanar da shi kotun majistare ta Yola akan zarginsa da hada kai da kuma damfara wanda ya ci karo da sashi na 60 da 317 na dokar Penal Code, inda yace taimaka wa Adamu ya so yi.
Kamar yadda ya ce:
“Mun hadu da Adamu ne a kasuwar Gombi inda yace ya sanar da ni burinsa na zama mai kudi.
Bayan hakan ne na hada shi da Alhaji Bala, boka akan cewa zai buga mishi kudaden bogi.”
An garkame Mohammed a gidan yari.
Ya ci gaba da cewa:
“Mun shirya zuwa gidan bokan da ke kan titin barikin sojoji inda muka bukaci ya buga masa kudin bogin. Bayan Alhaji Bala ya amince, ya nuna mana wata ganga cike da kudade N1000 dayawa, hakan yasa ya bukaci Adamu ya ba shi N1.3m.
“Bayan lokacin da ya diba mana ya cika, inda muka neme shi muka rasa Adamu ya shiga damuwa hakan yasa ya kai korafi ofishin binciken sirri.”
Bayan nan an garkame shi a gidan gyaran hali inda aka gurfanar da shi a kotu mai daraja ta daya ta majistare ranar Juma’a, wacce alkali Munammad Digil ya yi shari’ar.
Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Maris na 2022.
Yayin tattaunawa da wakilin The Punch, Adamu ya bayyana yadda ya fara ba bokan N300,000 don ya buga masa N40m wadanda zai bunkasa sana’arsa da su.
Sai dai a cewarsa, Alhaji Salisu ya bukaci karin kudi don bakaken aljanunsa su yi aiki da kyau, wadanda ya ba shi duk kudaden da ya bukata kafin ya yi layar zana.
Daga Hausa Legit
[ad_2]