Matashin ya ce yadda tsohuwar take kula da shi ya sa yace kawai yana sonta kuma yana son aurenta.
Tsohuwar nada ‘yaya takwas, jikoki ashirin kuma suna zama a gidansa da Muyiwa da abokansa ke zama.
Duk da banbancin shekaru 60 dake tsakaninsu, wani matashi dan shekara 25 ya shiga rumbun soyayya da wata tsohuwa yar shekara 85 mai suna Thereza.
Thereza da Muyiwa na shirin auren juna duk da ‘yayan masoyiyarsa da abokinsa sun nuna rashin amincewarsu.
Yadda Muyiwa ya hadu da Therez
Muyiwa ya bayyanawa Afrimax a wata hira cewa ya bar kasarsa Congo ne don karatu a jami’a.
Sai ya kama gidan haya hannun Thereza tare da abokinsa. Muyiwa yace a baya ya yi soyayya da yan mata bai ji da dadi ba, amma Thereza daban take kuma yana tsoron kada ta mutu da wuri.
Yace:
“Na tuna ranar wata Juma’a lokacin da abokin zama na baya nan, ina jin yunwa kuma ba mu da abinci. Na jigatu.
Kwatsam sai tsohuwar ta kawo min abinci.” “Yadda ta kula da ni yasa na fara son ta. Duk da cewa tsohuwa ce kuma ta kai shekarun kakata, amma ina sonta.”
Muyiwa ya yi kira ga masu zaginsa su rabu da shi, abinda yake so kenan.
“Wannan ne zabi na, kuma shine farin ciki na.”
Sun kusa shiga daga ciki
Thereza ta bayyana cewa tana son Muyiwa sosai kamar yadda yake sonta ta ce shirye take su shiga da ciki.
Tace: “Shekaru na 85. Inada yara 8 da jikoki 20. Idan aka lura da shekarun saurayina, kusan sa’in jikana na biyar ne. Yana so na kuma ina son sa. Shirye nike in aure sa.”
Ga bidiyon ku kalla
https://www.youtube.com/watch?v=SGp29PsKfHU
daga Hausa Legit
[ad_2]