MUSAYAR RUHI 1-2

*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*Page 1 & 2*
*W* ata kyakkaywar matashiyar budurwa yar kimanin 23 yrs zaune cikin makeken Parlour gefanta kuwa qawayentane kowacce tazubamata ido cike da shi’awa sabida yadda tayi masifar yin kyau kasancewar yau saura kwanaki 2 kacal d’aurin auranta suna cikin hidimar biki event suketayi kala kala
amma batare da ango ba sabida shikam bayama qasar se ranar d’aurin auran zaidawo waya takeyi cikin shagwa’ba
” _Haba my D wai ace yau saura 2 days bikin mu amma har yanzu kaqi kadawo gaskiya nafarayin tantamar Soyayya ta gareka kai bakanan amma ko katuromin bro d’in naka tunda babu wanda zaigane bakai bane gashi kasa sefaman jin kunya nikeyi cikin qawayena gaskiya banji dad’i ba ”
Ajiyar zuciya yasauke daga wancan ‘bangaran yace ” am sorry my B kinsan yanayin aykin nawane haka amma ay kinga inadawowa Nigeria ???????? zancigaba dayin ayki anan dole nagama dakomi kafin nadawo sabida inaso muyi rayuwa irin wadda se’anyi kwatancenta rayuwarmu zatazama abin shi’awa gakowa sannan kidenayin tunanin wai Hammat zezo wajan shi’aninku kinsan halin shi indama zanbiye tatashi dabanyi wannan auran yanzuba ki kwantar da hankalin ki kafin lokacin d’aura auran mu nashigo cikin Nigeria in sha Allah nide inaso kiriqe amana my B kinsan ina matuqar son ki please don’t forget me ”
Murmushi tayi tace ” haba my D tayaya kake tunanin zan barka please kabar wannan maganar duk wuya duk rintsi inatare da kai ” ajiyar zuciya yasauke daga ‘bangaran shi yace ” idan hakan takasance zanyi farinciki sosai ”
Sunjima suna waya cikin tsananin Soyayya gaskiya wannan Soyayyar tasu tamusamman ce bayan tagama wata daga cikin qawayen tana tayi murmushi tace ” gaskiya Hamidat wannan Soyayyar taku tana matuqar burgeni sosai Allah yasa nasamu mai sona kamar yadda Hamut yake sonki ” murmushi Hamidat tayi tace ” Amin shiyasa nike mugun alfahari da Hamut sabida yagamayimin komi a rayuwa tunda yabani zuciyar shi ”
Murmushi kowa yasaki cikin tayata murna dede lokacin wata matashiyar budurwa taqaraso wajan sannu tayi musu sannan tadubi Hamidat tace ” Aunty Momcy nakiranki ” miqewa Fadila tayi tabi bayanta wani madedecin Parlour suka shiga sannan suka shiga cikin bedroom d’in Momcy zaune take itada qawayenta da wasu daga cikin qannanta fita qanwar tata tayi gaidasu Hamidat tayi suka amsa cikin sakin fuska zama tayi tace ” Momcy gani ” murmushi Momcy tayi tace ” ay iyayen naki sunada yawa Hajiya Shahuda kekiranki ” duban Hajiya Shahuda tayi Hajiya Shahuda aminiyar Hajiya Salima ce wato Momcy su Fadila tare sukeyin shawara akan komi dazasuyi duban Fadila tayi tace
” Hamidat mahaifiyar ki tasanar dani cewa bakison shan magungunan da’aka had’a miki ko maiyasa kinsan halin maza kuwa? sunason mace tamusamman daga ranar farko samun darajar mace ko rashin samunta zaikasance agun mijin nafiso Hamut yarikice akanki fiye da tunani Hamidat kinsan waye Hamut samun namiji irinshi akwai wahala dan gaskiya baqaramin sa’a kikayiba kina shiga kinzama gimbiya zuwa wani lokacin kad’an zakizama Sarauniya tunda shine maijiran gado ” cikin sanyin murya tace ” su 2 de Momy kokin manta twins ne su Hamut dakuma Hammat kuma kowanne yacancanta yayi sarauta dan duk sunhad’a komi sannan nifa kunsan yanayina keda Momcy inacikin mata masu qarfin shi’awa dan Allah karkusa nayi abin kunya yazama nice nanemeshi bashine yanemeniba kunga idan hakan takasance darajar tawa tazube kenan sabida Hamut zaiga kamar nasaba da yin lamarin dan Allah kubarni haka wanda nashama nikad’e nasan cikin halin dayasakani ” murmushi Hajiya Shahuda tayi tace ” yaro yarone tabbas nasan Hamut da Hammat Twins ne amma ay Hamut shine Hassan ko kinga kenan shine babba shine mai hawan wannan kujerar sarautar sannan wannan yanayin naki cetonshi zamuyi idan baiji kin rikitashiba tayaya zai nace miki har kisamu irin biyan buqatar dakikeso kinsanfa yanadajin kai sosai irinsu koda sunason abu tofa basanunawa dan haka yazama dole kishanye duk wani magani dayake gurinnan kafin jibi maza d’auka kisha kowanne agabana ” babu yadda Hamidat ta’iya dole tasha badan ranta yasoba
Wata katafariyar masarautace wadda tahad’a abubuwa dayawa akwai karamci da mutunci ga tausayi da sanin yakamata ammafa akwai izza wajan hukunta duk Wanda yayi badede koda kuwa d’an gidanne Sarki Jabir shine kekan kujerar mulkin garin akwai masarautu dayawa a qasanshi sarki Jabir matan shi 4 amma abin mamaki bashida yawan yara yaran shi biyar 5 hassan da Hussein sune banya kuma sune yaran uwar gidan shi wato Hamut da hammat se Ansar qanin su me shekaru 20 kafin haihuwar Ansar sarki Jabir yayi aure aure har 3 bayan Hajiya Kilishi wato mahaifiyar su Hamut amma duk su biyun babu wadda tayi koda bari se amaryar shi mai yara 2 mace da namiji Fadila da Fadil duk sa’oin Ansar ne hakan yasa sarki Jabir yakejin tsunanin son yaran shi duka hajiya mariya da hajiya hajara sunyi masifar tsanar yaran duk itako hajiya Fulani wato mahaifiyar su Fadil da Fadila rayuwarta tana cikin tsananin kunci sabida rabantada sarki Jabir wajan biyan buqatarta ta aure tun bayan haihuwar Fadila sekaru 18 kenan sabida tsakanin Fadil da ita tazarar 2 yrs ne tarasa wane matsayi sarki ya ajeta
Itako hajiya Kilishi matada wata matsala agun sarki Jabir se gun hajiya hajara da hajiya Mariya musamman agun yaran dasuke riqo hajiya Mariya tana riqon yara har 3 Kumsat da Amir da Jamil itako hajiya hajara yara 2 Haisam da Amina hajiya Kilishi natason ‘ya mace sosai hakan yasa taroqi sarki akan tanason riqe marainiya bayan tahaifi Ansar da 3 yrs babu wani tantama ya amince inda taje gidan marayu ta amso Hanan tana cikin tsumman goyo wato tana jaririya kasancewar tagama shayer da Ansar da 1 year yasa batasamu damar shayer da Hanan ba sede akabata madara sosai hajiya Kilishi takejin tsananin son Hanan har yanzu Hanan batasan ba hajiya Kilishi bace ta haifeta sabida taroqi sarki Jabir akan bataso Hanan tasan haka yakuma jama sauran matan nashi kunne Ansar da Fadil da Fadila har cikin zuciyar su sund’auka Hanan jininsu ce sabida lokacin da’aka kawota basuda wayo Hanan yarinyace kyakkyawa sosai tanada haquri sosai tanada mugun zurfin ciki tanafama da Asma tayimata kamu sosai da’alama da’ita akahaifeta sabida tun da hajiya Kilishi tad’akkota sukefaman yin magani amma ina gashi har ta girma amma Asman tananan sunyi masifar shaquwa da Ansar da Hamut amma Hammat ina yatsani Hanan sosai tunda Hajiya Kilishi tad’akko Hanan yaji tsanarta cikin zuciyar shi hakan yasa Hanan takejin tsoran Hammat sosai
Hamut yanada sanyi sosai da haquri da kauda kai akan abu yanada kunya sosai amma kas yanada rauni akan duk wani abunda yakeso dan kuwa bai’iya miqa zuciyar shi akan abinda yakesoba miqata yakeyi duka yanada masifar biyayya agun iyayenshi duk abinda sukeso koda bayaso haka zehaqura koda zai cutu shid’in pilot ne shiyasa baya samun zama yanason Hamidat sosai kamar ranshi duk irin kunyar shi amma baya iya ‘boye soyayyar Hamidat cikin zuciyar shi tun tana ‘yar 12 yrs yake tsananin sonta tun daga lokacin duk wata hidimarta shine yakeyimata duk da kuwa gidansu akwai mazan kud’i hatta hidimar skul d’inta shine mahaifin su Hamut da mahaifin su Hamidat wah da qanine dangantakace tajini sosai Sarki Jabir shine babba akwai fahimta tsakaninsu sosai mahaifiyar su tanada rai sunayimata biyayya sosai mahaifin su yajima darasuwa mahaifiyar su tanacikin masautar tanada masifar sosai batada wasa ko kad’an hakan yasa kaf matan sarki Jabir suke jin shakkarta sabida idan tace hakatakeso ayi tofa babu makawa se’anyi tanaji da Hamut sosai samada Hammat sabida sauqin kanshi batashiri da Hammat sabida halin shi