BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

[8/30, 1:19 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
????
BANBANCIN KABILA
(Short story)
????????????????????????
????

TAMBARI WRITER’S ASSOCIATION

????((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al’umah))

*T.W.A*

https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/

WRITTEN BY ZAYNAB (zeexee)

MARUBUCIYAR

-RAYUWAR HUSNA

  • MAHAKURCI MAWADACI (2020)

1️⃣&2️⃣

Barkan mu da kara haduwa awani littafin, Allah yasa ku ji dadin shi, kuma Allah yasa ya amfane mu duk.
Wannan littafin it's a work of fiction, so in ka/kin ga ya zo similar da rayuwar ki/ka, kasan it's not intensional.

Am dedicating this page to my fam "my Mummy, my Daddy and my brave lil sis Nana Hauwa. I love you all loooooooadssssss.

Bismillah

Zaune suke a balcony, suna hira, sai kanin ta ya taba ta, ya ce “aunty Olamide, yau she zaki koma school ne”? Ya fada yana yatsuna fuska.
“Gaskiya kam aunty, yaushe zaki koma”. Kanwan ta ta tambaye ta, ta na daga gira.
“Mu kam mun gaji da mita ko Farida”. Kanin ta AbdulHakeem ya tambayi Farida.
“Ooooh owk, kun gaji da ni ko, zan bar maku gida nextweek. Amma ku sani, kafun in koma, sai na gasa ku”.
“Otobe! (Baki isa ba) mahaifiyar su ta fada.
“Kawai haka ki dinga takura ma yaya na, nextweek dinnan yayi yazo ki koma, ko yara na zasu ji sakat”.
“Haba Mummy, harda ke yanzu kin gaji da ni”? Ta fadi kaman zatayi kuka.
“Ae sosai ma, addu’a na yanzu Allah ya kawo miji kiyi aure, kinga zamu samu kwanciyan hankali, ba mai mana mita, kije can kiyi da mijin ki”.
“Kai Mummy è ni fe mi ni (baki so na ne)”?
“Of course ina son ki mana, your trouble is just too much”.
“Shikenan, tunda my trouble is too much, bari in bar maku wajan, kuma ba abunda zai kara hada ni daku, in ba gaisuwa ba, da major things, har in koma school”.
“Da mun ji dadi ko Boder (yaya)”?
“Sosai ma”. Abdulhakeem ya amsa.
Afusace ta bar wajan, ta shiga dakin ta tana huci.

*WACECE OLAMIDE*

Kaman yanda kuka sani, Olamide sunan yarbawa ne, although sunan ta Faiza, amma kun san yarbawa da son amfani da sunan yare, shekarun ta ashirin, tana aji uku a jamia, a B.U.K.
Yarinya ce mai hankali, ga son jama’a, ga lada bi da biyayya, tana ba kowa girma, ba babba ba, ba yaro ba. Gashi tana da fara’a sosai, ga wasa, da duk qualities masu kyau dai, amma fa Olamide akwai masifa, ga uban mita.
Mahaifin ta ya rasu tun tana primary school, alokacin shekarun ta shida, toh tun lokacin mahaifiyar su ta zama ko mai nasu da ita da kannan ta.
Sunan mahaifin ta Alhaji Abdullahi, sunan Mahaifiyar ta Alaja(Hajiya) Fausat. Kannan ta biyu, da Abdulhakeem da Farida.
Shi Hakeem, kaman yanda suke kiran shi, shekarun sa sha’takwas, yana aji daya ajamia, a ATBU Bauchi, Ita kuma Farida shekarun ta sha’shida, tana secondary school ne, tana ss2.
Although su yarbawa ne, amma suna zama a arewa, anan ma aka haifi mahaifan su, harda su, in short nan duka Familyn din su suke, kawai dai muna yarbawa ne, dan basuma san hanyar garin yarbawa, although dai sun iya yaran kadan kadan. Suna zama ne a jahar Niger, agarin Suleja, sunma zama yan gari awajan, amma kun san bayarbe da kishin yaran sa.

~Wanan kenan~

Data shiga ciki, su ka fashe da dariya.
“In dai Mide tace, duk abaki take yi, da kan ta zata fara magana da mu”. Mummy ta fada.
“È ma dalon( kar ki damu) mun saba Mummy”. Hakeem ya fada yana dariya.
Ita kuma Farida, tayi shuru, kaman bata wajan.
“A’a goggo Farida, lafiya?
Naga yanzu muka gama dariya, ina magana kuma ki kayi shuru, kaman na tuna maki da wani abu”.Hakeem ya fada.
“Hmmm boder ba zaka gane ba. Kasan baku zaku kwana da aunty Faiza ba, tunan nin masifan da zan sha nake yi”. Ta fada kaman zatayi kuka.
Tana maganan, Mummy da Hakeem suka fashe da dariya. Hakeem na dariya har ya fado daga saman kujeran da yake zaune.
Cikin fushi tace “wallahi boder matsala ta da kai kenan. Kai zaka jawo fada, amma ni zan sha masifa”.
“Toh ni nace ki sa baki ne?
Ai da nake magana, baki ji nace Farida kisa mun baki ba”
“Toh ai kaima ka san bazan iya shuru ba” ta fadi tana goge fake hawaye.
Ita ko Mummy sai kallon ikon Allah take.
“Eya, amebon(gulman) ki ne yayi yawa. Kinga bani ke saki ba kenan. Kuma indai masifa ne, yau zaki sha shi buhu buhu. Amma in baki son ki sha masifa, ki bi Mummy dakin ta, ku kwana tare”. Hakeem ya fadi.
“Toh ai boder Hakeem baka sani ba, nightwear dina na dakin”. Ta kara fada tana yi kaman mai kukan gaske.
Wani sabon dariya Abdulhakeem ya kara yi.
“Wato aunty Mide ta zama doodo agidan nan kenan”.
“Idan ma akwai abun da ya fi haka, toh ta zama shi, ni dai anu è ni tiyo fe won mon gbo( tausayin wanda zai aure ta nake ji).” Farida ta fada.
“Wanda zai aure ta ko ya’yan ta, ai ya’yan ta kam sun shiga uku”. Wannan karon Mummy tayi magana.
“Bari kawai Mummy”.
Haka suka cigaba da hiran su.

Ita kuma Faiza (Olamide), data shiga daki, taje ta zauna akan gadon ta, don daman kowannan su (ita da Farida) na da gadon sa.
Ta zauna tana ta huci, wai ita ce suke kira mai mita, da masifa, ai zasu ga masifa da mita kuwa, dan yau din nan, sai Faiza tayi kuka, shi kuma Hakeem, sai idon sa ya raina fata, dan zata jijjiga su sosai kafun ta koma. Tana cikin tunani, lokacin sallan magrib ya yi, ta tashi ta shiga toilet din dake hade da daki, ta yi alwala, sannan ta fito tayi sallah.

Suma acan waje, suna jin kiran sallah, ko wannan su ya tashi. Mummy ta wuce dakin ta, shima Hakeem ya shiga dakin shi, yayi alwala, sannan ya wuce masjid. Ita ko Farida, tana bakin kofa, ta kasa shiga daki. Tasan indai ta shiga dakin nan, toh akwai problem, dan yau mai ceton ta sai Allah, ko in Mummy ta nuna mata bacin rai.
Sanda taga Olamide ta fara Sallah, kafun tayi sanda ta shiga dakin, ta dauki hijjabin ta, ta fita da sauri, ta wuce dakin Mummy. Nan ma ta samu Mummy ta fara sallah, sai ta shiga toilet din Mummy, ta yo alawala, kafun ta fara sallah.

Olamide na idar da sallah, tayi addu’a, ta nike Hijjab, da sallayan data yi amfani da shi, ta sa kowannan su a mazaunin sa. Data gama, ta zauna saman gado, ta fara dariyan mugunta. Ta ce “zaki gane ai yarinya, bani ba”?

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

“Umma ta, yau fa naji jiki sosai, ji nake kaman ban taba aiki ba arayuwa na” Wan saurayi ya fadi. Kana ganin shi, kasan wanan bafulatani ne, ga shi dogo, amma fa ba sosai ba, dan normal dinan, shiba siriri ba, kuma ba shi da kiba, normal size din nan ne. Ga kyau mashaAllah ba’a magana, gashi fari ga dogon hancin nan kaman pencil, ga idanuwan sa manya manya, yayi fitting din shi sosai.
“Yau aka fara?
Ai kaidaman ba ranan da bazaka dawo daga aiki bakayi complain ba, kuma kullum aikin ke maka wuya”. Matar da ya kira Umma ta amsa mai. Itama matan, ba’a magana, tana da kyau sosai mashaAllah, gata ita ba fara ba, kuma ba baka ba.
“A’a Hajiya, bana son kina ma auta na haka fa”.wani dattijo ya fada. Toh kana ganin dattijon nan, ka ga saurayin, saboda suna kama sosai, har ya baci. Amma babancin shine, shi wanan ya fara tsufa, shi kuma wanan saurayi ne.
“A’a Abba, kasan wanan yaron is very lazy, abu kadan sai yace ya gaji, yana abu ne kaman mace. Ina ji ma matar ka, saboda ita zata dinga aikin na miji agidan ku”. Yayan saurayin ya fada, shi wanan yana kama ne da Umma sak.
“Abba na ka kyale su kawai”. Ya na fada, ya tashi yana mika, sanan ya wuce dakin shi.
“Lazy woman kawa” yayan shi ya fada.
“Subhanallah, auta na ba woman ba ne, man ne, kuma a very strong man”.
“A’a Alhaji adai fadi gaskiya. Ai wanan ya ma fi woman lazy”. Tana fadan haka, yayan shi ya fashe da dariya.
Da ya shiga daki, ya cire tie din dake wuyan shi, ya na yi yana hamma.
“Gaskiya I need to get married, atleast in ina da aure, irin yau dana dawo agajiye, ita zata cire mun tie, ta fara tarba na tun daga bakin kofa, ta amsa briefcase dina, ta hada mun ruwan wanka, kafun in gama shafa mai, ta kawo mun abinci. Gaskiya aure kam akwai jin dadi, no wonder Yaya Sudais na kiba, amma I wonder why almost everyday yana gida, instead ya bari nima in mori su Umma, amma sai yazo suna hada hannu da Umma suna tsokana na”. Ya fadi yana murguda baki kaman mace.
Daya gama cire kaya, ya shiga toilet, yayi wanka, yana gama wanka, yayi gab da an kira sallah, kawai yayi alwala kafun ya fita, ya yi dressing, ya fesa turaruka, ya fita parlor, nan suka hada hanya da Abba, saboda by that time Yaya Sudais ya tafi gidan sa.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Leave a Reply

Back to top button