NOVELSUncategorized

KWARATA 46

???? —— 46


          Tsare Mamy nayi da ido na kasa magana duk saida ta gama buɗemin komai ta ƙare da cewa harma ta gayyato shi zaizo katsina jibi , har ta gama kallonta nakeyi saida takai nunfashinta ƙarshe nayi murmushi amma har yanzu idona akanta yake , kuma banyi magana ba ,


     Mamy taci gaba da cewa tou ya kike ganin za’ayi idan yazo ? Zance gaki ko kuwa ? Shiru nayi na ɗora wayata a saman goshina na rufe idona na dama ina nazari ,

      Kije abunki amma duk abinda zaki kiyi na hankali da tunani ,


        Ni bana zarginki har abadan duniya anma dan Allah karki sake ki bari zuciya da sharrin shaiɗan yasa aimin wasan danbe dake , ni ɗaya tak na isheki bana gajiya kuma bazan taɓa gajiya dake ba har ƙarshen numfashi na,

       Jarumi ɗaya tak akeyi a ƙarni nine jarumin wannan lokaci , Dikko jarumin maza ne kuma ke da kanki zaki faɗa kije ki dawo ina nan ina jiranki….!

      Hawaye ya gangaromin daga cikin ido nace a ina kake jirana inzo ….? Murmushi Mamy tayi tare da cewa soyayya ? Shiru nayi ina hawaye , dariya tayi sosai tace har kin bani tausayi Sultana uban waye ya shiga zuciyarki har kike kuka ?

     Saida nayi shashshekar kuka sannan na kalli Mamy da ido ɗaya nace ni kike tausayi ? Tace Eh ai soyayya babu abinda ke cikinta sai wahala da dana sanin da bashi da amfani , murmushi nayi mai ƙuna nace gara ki tausayimin dan a halin yanzu banma san a babin da nake ba , 

     Yana so na har yanzu ko ya goge ni daga zuciyarshi banma sani ba , dama yace idan bana sansa zai tafi kuma bazai sake dawowa ba , yazo a lokacin da bansan waye shi ba , kuma ya tafi ya barni a dai² lokacin daya koyawa zuciyata soyayyarshi , bazan gaji ba , ba kuma zan daina faɗa ba har kalma na ƙarshe a duniya , ina sanka ׳ Na ƙarasa maganar ina goge hawaye ,

     Tsoki Mamy tayi tare da cewa yanzu kinji abinda na faɗa miki , sai magana na gaba , akwai wani mijin ƙawata yaga wata anan anguwar yana so ya ɓata dare ɗaya tak da ita , tou na biyota bayan nayi bincike sai akacemin matar aure ce , dana faɗa mishi sai yace min dama matar auren yake nema shin zaki iya kawo mishi ita ? Akan wane farashi ? Na tambayi Mamy , tacemin 50k nace kai haba zunubin fa akwai girma , yadai ƙara wani abu… 

     Mamy tace Sultana haka zai baki , kallonta nayi ido cikin ido nace gaskiya ƙarya kikeyi ke kika rage kuɗin da za’a bani , Sultana ni nake ƙarya ? Nace yo wace ce ke da baki ƙarya ? Mamy tace dama naga kin raina ni ko girma na baki bani ? Murmushi nayi da gefen baki na , nace babu wanda ya kawoni bariki ni na shiga da kaina , bana ƙarƙashin kowa ina bisa ƙarƙashin ikon zuciyata ne , banda uwar ɗaki haka kuma banda ubangida , bana nema wurin kowa dan kowa baida abin bani , wannan harkar ra’ayina ne yasa na shiga badan ra’ayin kowa ba , abuna yana jikina naki yana jikinki , tayuwu ke ki bada naki a baki 1k wannan ra’ayinki ne kuma kinji kina iyawa ne , niko babu dalili na buɗewa namijin banza ƙafata ya hauni ya sauka ya bani kuɗin da bazasu kashemin kwarnafi ba ,

     Ban kawo ki bariki ba baki kawoni ba ,baki koyamin ba haka nima ban koya miki ba , a rana tsaka muka haɗu kin gama gogewarki nima idona biyu kika ganni ba bacci nake ba , tuni na bushe fitilar idona , banda Aunty banda Yaya banda Mama haka kuma banda uwar ɗaki a bariki wallahi , ta yuwu ma kila namiji ɗaya ya nemu a tare yana gamawa dake ya jawo ƙafata , wane girma gareki a wurina ? Sana’ar fa iri ɗaya ce , uwar data haifeni ma data ga bata iyawa kayanta ta tattara ta kama gabanta tou bare fa ke banzar bazara kashi a masai , na faɗa kuma zan sake maimaitawa idan bakiji ba kiji , idan kuma kin manta ki sake fahimta ,

     Matar aure bana kawota a dubu 50k wallahi idan dai yana so tou dubu ɗari biyar zai bani nayi miki alƙawari kuma ki mishi albishir a cikin sati ɗaya tak zan kawota babu asiri babu bori , idan haka yayi miki to idan bai miki ba a daina cinikin dan bana san rainin hankali da yawa….

    Shiru Mamy tayi tana kallona ni kuma naci gaba da gwada layin Dikko , can kuma tace tou za’a baki rabin kuɗin idan an gama sai a cika miki , ba tare dana kalleta ba nace ni bana da sasshen jikin mutum , Mamy tace kamar ya kuma ? Nace tou kamar yadda zaki bani rabin kuɗi ! Me zan ciro na fara kawo mishi ? Mamy tace Sultana zan baki rabin kuɗi idan aka gama na cika miki , tsoki nayi nace kinga da Allah ki tashi kina ɓatamin magana a banza , kije idan kun shirya ansar mace kuzo da dubu ɗari biyar na gama magana….

     Jakarta ta buɗe ta ɗauko dubu ɗari biyu tace gashi zan cika miki anjima , ai banma da lokacinta bare kuma tayi tunanin naji abinda tace , can kuma tace kin cika kafiya gasu bara na ranta cikin kuɗin ƙawata idan naje banki na cire ita saina bata , da gefen idona na kalli kuɗin , miƙomin tayi na ansa na tusasu fes sun cika , hoton matar ta turamin a wayata tace gata nan kuma bama so sai tazo tayi ta wani noƙe ² nace inki so kije abunki ,

    Har zata fita nace , maganar mai zuwa katsina kuma jibi akwai Hamida akwai yaran gidan Baba ƙarami ki taimakamin suma su shigo sahunmu tafiyar zatamin dai² , Mamy tace baki da damuwa , godiya nayi mata ta wuce abunta , ni kuma naci gaba da nazari akan hanyar da zan fiddo matar aure a kaita wurin mijin da ba nata ba kuma banma taɓa magana da ita ba ina dai ganinta tana wucewa !

     America…

       Mai gida Dikko ne kwance a gefen gado , ya ƙurawa waya ido ko kiftawa bayayi , daga can ƙarshen gado kuma amaryace sanye cikin wata irin tsadajjiyar alkebba , mutum biyar suka kawota kuma kwanansu biyu yau suka juya bayan sun ƙara gyarewa ango amarya suka shiryata cikin shiga ta alfarma da ɗaukar hankali , bayan tafiyar “yan rakiyarta ta dawo ɗakin da take tunanin nan ne ɗakin mijinta ta tsareshi da kallo kamar kwarton namiji yaga wawan zama..

KU DANNA  NAN DON SAMUN KYAUTA

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


      Tafi minti 15 zaune bataji yayi magana ba , dan haka ta tashi tsaye ta zare alkabbar ta ajiye a gefen gado , cikin gogewa da buɗewar ido ta fara tafiya cikin natsuwa ta zagaya inda Dikko yake kwance.

      Kafin ta iso Dikko ya tashi da niyar shiga toilet , da sauri tasha gabanshi tace haba ina ne kuma zakaje ne bayan kayi wanka , kallonta yayi sannan yace zan tsaya kiyi ta kallona ne kamar banda aikin yi ne ? Haba Yayana aiko kaine kake da aikin yi a gabanka , nuna kanta tayi daga sama har ƙasa tace mai wannan zundumemiyar mace inashi ina bacci a daren nan ? Ga kallo kuma ga aiki , kasan yanzu ba’a sake da miji mai mummuna ma ta tattala abinta ina gani mai tsadajjiyar fuska da ƙira mai ɗaukar hankali kamar ka ? Ai banga ta zama ba aiki ya sameni harsai na goge tambarin ɗiyan ɗan caca a zuciyarka…

          Wace ce ɗiyan ɗan caca ? Dikko ya tambayeta yana mata kallo mai nuni da zaici ubanta ! Haba Yaya DK kana tunanin bansan komai ba ? Kaf labarinta a hannuna yake , me zakayi da wannan yarinyar ? Yarinya mara tarbiya , marar asali jahila da bata gane komai sai karuwanci..

      Murmushi Dikko yayi maicin rai dan duk duniya ya tsani a famo mishi ciwon tunanin An mata , haka kuma ya tsani a soketa , cikin ƙunar rai yace ni na sanki tun baki san kanki ba , haka kuma nasan waye ahalin babanki ciki da waje , idan har zan duba girma da tsatson ahali da tarbiyar iyaye ke ko matsayin mai aikin gida na baki ba , da cancanta aka bimin wurin auren da aka yomin ke kinsan baki kai cikin layin matan da zanbi hanya ɗaya dasu ba , An mata bata sanki ba kuma baki gabanta dan bata san da zuwanki ba , tana can tana rayuwarta bake ba ko ni bata da lokacina bana san munanan kalamai yana fitowa daga bakin ki akanta , ba ƙoƙarin gogeta zakiyi ba domin bata gogowa har abadan duniya a zuciyata , idan dai zaki iya kiyi ƙoƙari ki kafa soyayyarki a zuciyata shine abinda zakiy farko kenan ,

       Sassauta muryarshi yayi sannan yaci gaba da cewa , tana da tarbiyya , nine zan bada wannan shedar , asalinta kuma yana tare da asalina , tabbas bata gane komai sai karuwanci , nine na yanka mata tikitin karuwanci nace ta koyo dan tamin riƙo da bazan taɓa tunani wata mace a duniya ba sai ita , ta shafe kaf illahirin zuciyata , tabi cikin kwalwata da jinin jikina , yarinya ƙarama mai tafiya dai² da irin rayuwar da nake so , zan bata labarin ki , kuma ince kina mata gori itama ta goranta miki tunda dai uba baifi uba , sa’arki ɗaya ma da mamanki ta haɗo da momy ai da ina ganinki sai nayi amai…

    Goge maganar tayi dai tare da nunawa Dikko ya bata haƙƙinta , shareta yayi ya shige toilet, bai daɗe ba ya fito da alama alwallah yayo , itama shiga tayi tayo alwallah ya gabatar da komai kamar yadda yayi a daren farkonsu da Sadiya cikin natsuwa , bayan sun gama suka koma gado anan Dikko ya farke sabuwar amaryarshi kuma ya sameta a cikakkiyar budurwarta ,

      Yayi farin ciki dan a tunaninshi yadda take ta nuna haɗama tana zalama baiyi tunanin zai sameta a cikakkiyar mace ba , komai yaji gaskiya amma Dikko yace gishiri yayi yawwa , { tasha kayan mata sosai } dan shi Allah ya bashi ilimin gane tsurun mace idan ta haɗa da “yan dubaru ya sani , amma wallahi An mata itadai ta dabance…

    Sai kukan kissa matar Dikko keyi , cikin nuna tasha wahala , Dikko kuwa ɗan jirgiwa yayi ya kifar da kanshi saman katifa tunanin yadda darenshi ya kasance da Sultana yakeyi , wallahi ya cuci budurcin An mata daya karɓa ta ƙarfi da yaji , ƙaramar yarinya da ƙananan shekaru ya saki ƙarfinshi ya haɗa da magunguna yaje mata a gigice , bata taɓa gani ba kuma bata taɓa ji ba sai a gareshi , me yasa ….?

Me yasa? Me yasa haka ta faru ? Dole kice bakyasan Dikko saboda Dikko ya zama mugu a wurinki , An mata da kinyi haƙuri kin bani dama a karo na biyu da kinyi alfahari dani , da bazan barki kiyi kuka ba , bazan barki kiyi baƙin ciki ba , shi kenan kin fita a hannuna zaki tafi wurin mai rabo ya ɗaukeki ya dasa wasan sa daga inda na tsaya…

      A hankali ya lumshe kyawawan idonuwanshi a bayyane yace Allah ya sanyaya miki zuciyarki , a tunaninta da ita ake tace amin mijina , har yanzu idonshi a rufe yace kin yafemin kenan ? Ummm ai bakamin komai ba ma , kenan babu zafi ? Umm umm , to me yasa ki key kuka ? Ba komai , sai yanzu ya gane bada Sultana yake maganar ba , buɗe idonshi yayi da sauri ya ganshi kwance akan sabuwar amaryar shi , kuma “yar uwa a gareshi…

        Ko tsakar dare dana farka haka naci gaba da gwada wayar Dikko wanda ya zamarmin kamar hauka dan ƙaranci ban kira wayarshi ba a rana na kirashi sau 200 da wani abu ,

      Ina zaune tsakar daren nan ina ta aikin neman wayar naji maganar Baba ƙasa² daga bayan ɗakina dake daga tagar ɗakin sai a fice zaure a fita ƙofar gida , bana iya jiyo abinda Baba yake cewa saidai naji maganar Amisty cikin shagaba tana cewa nidai Dady don Allah… Ta ƙarasa maganar kamar tana kuka !

     Da sauri na haska fitila na duba agogo naga 3:45am cikin sauri na miƙe na sake matsawa da kunnena jikin window naji shin da gaske Amisty ce ko kuwa dai wata ce daban ! Wallahi Amisty ce dan duk duniya babu mai irin wannan muryar sai ita , me suke cewa ? Me ya haɗa Amisty da Babana a wannan salasunan daren ? Me ke tsakanin Amisty da Baba ? Duk wannan tambayar banda ansoshinsu nayi yunƙurin yin wani abu tunani na ya tsaya cak domin kaina ya riga da ya juya…

     Buga kaina nayi da ƙarfin bala’e a jikin bango na kurma wani irin ihu duk wanda ke cikin gidan saida yayo waje saboda ƙarfin ihun da amonshi ni kuma na fito da gudu nayo hanyar fita , babu Amisty domin tuni ta fice , ina ƙoƙarin fita Baba ya riƙeni da ƙarfi yana lafiya ? Fizge ² na farayi na kwace nayi waje , da gudu ya bini ya riƙoni nafi ƙarfin riƙonshi domin na sake zuƙewa daga riƙon da yayimin , cikin tashin hankali zugar gidanmu suka yo kaina dakel suka kaini ƙasa suka daddanne ni na birkice gaba ɗayansu na watse su , na yanki santa , yayuna maza suka taimaka aka kamani aka mayar dani cikin gida ,

      Kowa tambayar abinda ya sameni yakeyi ? Murmushi nayi mai ciwo na kalli Baba nace ina ka ɓoyeta ne ? Cikin rashin fahimta yace wa ? Kafi kowa saninta me takeyi a gidan nan a wannan lokacin me tazo yi me take nema…? Baba yace wai wace ce ? Ga sunan Amisty a zuciyata amma ƙiri² ya gagara na faɗa a baki na , nace ita mana ita wace ce ? Kai ji nan na nunashi da ɗan yatsa nace tana ina karfa ka ɗaukeni mahaukaci nasan abinda nake ina ka ɓoyeta ne ?

Amma Baba sai ya fara tofa min addu’a yana cewa aljannu sun kama uwar masu gida , a taimakamin da addu’a , inaji ina gani Baba yasa aka mayar dani mahaukaciyar ƙarfi da yaji , kowa yayi ta tofamin yawu , banda yanda zanyi dole nayi shiru amma wannan abun bai gogemin daga zuciya ba kuma saina bi salsala na gano abinda ke tsakanin Baba da Amisty , maganar Mamy ta dawo min a kaina kamar yanzu take faɗamin maganar…

     Gaskiya an samu matsala shi kanshi Binna da yasan waye Hafsa a wurinshi daya haɗe zuciya ya mutu ,  itama bata san wayenta ba , shima Baban Hafsa baisan ke wacecen shi ba , kowa iskanci ² gaba ɗayan ahali sun zaman KWARATA…

    Lallai akwai alamar tambaya a wurin nan amma waye zai fiddo maganar daga cikin zuciyata ? Waye ? Waye zai taimakeni ne ? Wai wace ce ni ? Anya kuwa ni mutunce ? Mutane kuwa suna gani na ? Wai meke damun rayuwata ? Me ke damun kwalwata ?  Wannan wane irin masifa ne ? Wace irin rayuwa nakeyi ? Ina mahaifiyata wai me Baba ya ɗaukeni ? Me nene ׳ na ƙarasa maganar ina ɗaga muryata wanda ina tunanin duk mutumin dake anguwar nan yaji irin hayagagar da nakeyi…

       Fashewa nayi da wani irin kuka nace tabbas ko wace ce ni da sanin wace irin rayuwa nakeyi amsar tana wurinki , kuɗin da Mamy ta bani na ɗauko na irga suna nan yadda ta bani su , maidasu nayi na aje , amma a zuciyata nayi alƙawari zan bautata mata tiƙuru kuma zan bata girmanta kamar yadda take so zan nemo matar nan kuma zan kaita zan bawa Mamy kuɗinta kuma zanci gaba da farauto mata duk wanda take so adalci ɗaya zatamin ta warwaremin sirrin rayuwata wannan shine kawai mafita….

     Gari na waye nayi wanka yau ko inda Babana yake ban kalla ba kuma ban gaishe shi ba , makulin mota ta na buƙata ya bani amma sai yacemin wai anci motar a caca , kallonshi nayi nace ni bansan caca ba mota ta kawai na sani kuma sai ka biyata ,

       Mamana ni kike cewa saina biyaki mota ? Kaine ka siyata ne ? Ai ko ban siya ba naci albarkacin haihuwarki da nayi , ka maidani ciki idan kaji munin maganar  amma sai ka biya wannan motar babu gudu babu ja da baya kuma ba abinda ya dameni na baka daga yanzun nan zuwa bayan sallah isha’e … Ina faɗin haka nayi waje abuna na barshi ta tagumi…

      Ina fita na shiga maƙota na nuna hoton matar da Mamy ta turomin a wayata nace da Allah ina neman gidanta , matar tacemin lafiya dai ko ? Nace lafiya qalau gwamnati tace a taimakawa masu ƙaramin ƙarfi wanda suke shan wahala a gidan aurensu , an ɗauko jaddawalin sunan ko wace macen aure da ƙaramin katin hotonta , sai naga ita kamar tafi kowa shan wahala shine nake so ita a taimaka mata da yawa , mata da kuɗi sai Allah kuma nayi haka dan in rubzata rami itama , ta haka zanji wane irin hali matar take nasan komai nata kafin na isa gidanta , !

      Murmushi matar tayi tare da ɗaukomin kujera na zauna tace amma Sultana kunsan kuna da hanyar taimako shine mu ba’a saka sunanmu ba ? Jakata na zuge na fiddo damen “yan dubu² nace kin gansu nan kowa da sunanshi ai bansan kuna buƙata ba , itama banda tabbacin da zataje ko bazata ba , 

     Tace zuwa kai , muje na rakaki gidan ta amma don Allah nima kisa a rubuta suna na don Allah , nace baki da matsala , saman ƙyaure ta ɗauko hijabinta tana ba yaranta umarni karsuyi mata ɓarna idan Babansu ya shigo ta shiga maƙota baza ta jima ba ,

       Ta gaban gidan Amisty muka wuce gaba ɗayansu suna ƙofar gida hada Asma’u an saka kujeru na roba Amisty kuma tana ta tofi da hayaƙin sigari , yayin da wata tantiriyar “yar iska ke shan shisha tana murza hayaƙin cikin ƙwarewa da gogewa a cikin harkar ,

Har mun wuce naji bana iya haƙuri na dawo da baya , dai² Amisty na tsaya na ciro sigarin daga cikin bakinta na kasheta a saman goshinta , wata irin ƙara tayi saboda zafi ta riƙo hannuna na , da hannun damata na riƙe hannunta saboda dana haggun na kashe mata tabar sannan nace na rantse da Allah duk ranar da hasashena ya zamo gaskiya yadda na murje wannan sigarin a goshinki haka zan murje miki rayuwa..

      Gaba dayan su sukayo kaina suna kee…. Nace heeee ku saurara na kaso daku sannan ku ɗauka domin yanzu babu sauran muradin ɗaukar fansa a zuciyata ina neman rayuwata ne amma idan kuka bari na ɗauki zafi anbaliyar wuta zan fara hattaranku domin ni fetir ce kuma sai cikin wuta nake amaina ! 

      Kallon Amisty nayi nace ki fara addu’ar kuɓuta daga sharrina domin na yanzu ba irin na baya bane , na yanzu maciji zansa ya cinye kwansa { uba ne zai kwanta da “yar sa } ki kiyayi haɗuwa ta da ke domin abin bazai miki kyau ba ,

      Sakinta nayi na kalli matar nace mata muje… Wuce su mukayi muka tunkari gidan matan , da sallama muka shiga , ta amsa mana cikin sakin fuska tare da shinfiɗa tabarma tace ku zauna sannunku da zuwa ,

      Zama mukayi , baiwar Allah ta dama ɗan kokonta da ɗumamen tuwo suna ci ita da yaranta tana ma Allah godiya ,  amma dole tayi haƙuri domin Sultana ta shigo mata rayuwa , mijinta ya fito daga cikin ɗaki muka gaisa dashi ita kuma tabi bayanshi danyi mishi rakiya , wayyo bawan Allah kayi haƙuri Sultana tazo yanzu zan firgita maka iyalinka ka kasa gane gabanta bare bayanta…

    

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button