BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Wannan kalma ta daki Walyn a lokacin da bata shirya ba,

Zurbat ta mike daga zaunen da take inda wayar dake saman cinyarta da jakarta suka fadi saman fari kal din careau din wajen,

 A lokaci daya gaba daya jikinta ya dauki rawa, ba inda baya rawa a jikinta,

Bakinra ta kara budewa da bila adadin dan yin magana sai dai kawai hakoranta suke hadedewa bakin na rawa lebunanta na marmarmar,

Juyawa ta yi da karfi wajen da Agaishat take, 

Kafarta ta daga da niyar karasawa wajen Agaishat din idan ya so idan ta isa sai ta aikata mata abinda ya samu koma menene, 

Sai dai me, idannuwanta ne suka rufe ruf,

Bata gani sannan a hankali lumfashinta ya yi sama ya dauke dif, inda ta aniya zubewa a wajen,

Du hankalin mutanen wajen ya yo kanta inda du aka mimike hankali tashe, domin bata karasa kasa ba ya tarota jikinsa ta sume a jikinsa,

Tsai ya yi ya kurawa fuskarta ido, a sumen abin sha.awa da ita, ta yi fayau ta nuna fuskar innoscent,

Dan mayafin da ta yiwa wayo ne yake faman sabulewa inda Alhinayett ke tsugune inda suke hankalinta tashe ta shiga magana kamar haka” War, mu je asibiti, ta suma fa, bata motsi, Wardugu mu kaita asibiti,

Dubansa ya dago a hankali inda take , 

Murmushi ya sakar mata yana dubanta , muryarsa ya rage sosai domin ana faman zagaye su du kuwa da irin tsaron da sojawan ke faman bayarwa da tsare du wani wanda zai yi gigin karasawa inda suke sai wa.inda aka tabatar da kusancinsa da wardugu mai girma ne ake bari ya karasa inda suke, hakan bai hana mutanen dake wajen zaman amaren karasawa da sauri suna tambayar wai lafia? A hanzarta kaita asibiti mana?

Wardugu ya ce da Alhinayett, ” Alhi, bafa wani abu na yi mata ba, ke ai kin san ina hakuri da ita ko? Gaskiya ce kawai na fada mata fa,

Alhinayett ta ce” menene ma.anar Orronur?

Wardugu ya lunshe idannuwansa ya kai dubansa inda Agaishat ke tsaye tana so a barta ta karasa wajensu aman an hanata dan gurin faman cakulewa yake sai kacaniya ke tashi kowa na faman a barshi ya karasa ya ga kwakwaf,

Ya dawo da dubansa wajen Alhinayett ya lumshe idannuwansa yana dan shafa gaban goshin Walyn dake kan kirjinsa sume kafin ya ce” *ORRONUR* na nufin *RAINA* 

idannuwa Alhinayett ta zaro cike da tsoro ta kai dubanta da sauri kan Walyn, Balaki! Shi ne kalmar da ta fito daga bakinta, ai kuwa da sauri ta mike tana fadawa mijinta a saki hanya a kai Walyn asibiti, domin tana adu.ar Allah ya sa lamarin ya tsaya a iya sumar kawai, kar ta samu mutuwar barin jiki na bugawar zuciya,

A yanda Walyn ta baiwa kishi madaukakiyar daraja a rayuwarta, a yanda walyn ta dauki lamarin soyayar mijinta a zuciyarya da son kai mai girman gaske, a yanda Walyn ke taka tafiarta na rayuwa da izgili da fariwa da neman magana? A yanzu, wardugu , ya ce kau bani gu, Wardugu a yau zata iya kiransa da Masifafe, ohk so yayi ta daga bali, ta jawa kanta ya daki banza, tabas suma ta zama wajibi a rayuwar Walyn a yau, domin da wannan lamari bai razanata ta suma ba, zata tafka haukan da Wardugu zai sumar da ita, ya salam, ya salam, haka kai tsaye? Tabas tana hangen Wardugu zai zama jarumi wajen fadawa Walyn wannan lamarin a duk lokacin ta sani ya bayana, aman bata taba tunanin kai tsaye haka ba? Mata? Me ke yawo da kusoshin kanmu ne? Gashi dai, da darajarta , da girmanta, da dan shakunta da yake ji ta bale ta saka lokaci daya ya janye du wani laka na jikinta! Ribar me ta ci? Ana kishi, kishi halal ne, kowace mace na kishin mijinta, aman kishima ai taku ne, ????‍♀,

Da sauri aka bude wajen aka shigo da mota, du wannan tsare tsare haka mijin alhinayet ya take da mota har kusan matatakalar , aka bude motar ,

Mikewa Wardugu ya yi da ita a jikinsa ya samu ya sauka a hankali ya sakata cikin motar,

Bai shiga ba, ya dawo bayan ya cire rigarsa ta saman wato kaki din mai dogon hannu sai bakar body ta ciki ta bayana mai dan gaheran hannu sannan ta tantanke jikinsa baki daya, hakama ya sakata cikin wandonsa ya yi zanzaro da ita a ciki,

Hular kansa ma cirera ya yi, ya koma wajen da Alhinayett ke tsaye ya dubeta ya ce” ki zo mu je,

Da sauri ta juya dan dauko jakar Walyn da wayarta,  har ta bude ta saka cikin motar ta ji muryarsa ya ce” ita fa?

Ba sai ta tambaya ba , ta san wace yake nufi , dan haka ta karasa kusan Agaishat ta damko hannunta kawai ta janyota suka nufi motar inda shi ya shiga gaba su kuwa suka shiga baya suka zazauna,

Gudu yake da motar, baka jin komai sai kuryar Agaishat tana ta tamabayar abinda ya samu Walyn, me ke damunta? Me ya sameta ? Bata da lafia ne? Ko gurdewa ta yi? Alhinayett ki bani amsa mana? Dibi fa ta suma fa, 

Uta dai Alhinayett ta yi wani zuru tana kallonta, to me zata ce da ita? Ita bata ma san abinda ke faruwa ba, bata taba kawowa ranta haka ba, hasashenta bai taba hasaso mata haka ba, ita yanzu fatanta a karasa lafia kar ta farka ta ganta kusa da ita ta kashe su a motar nan, kai rana tsoron zafin kishin Walyn, macen da ta salwantar da gudan jinninta dan kar ta haihu da wuri a fara yi mata irgen abinda ya rage a mata kishiya idan hakan ta kama? Ina ga yanzu hakan na kokarin kamawar? Taf

A haka suka karasa clinik, wato asibitin kudi, 

Nan da nan aka gungura gadon mararsa lafia aka dora Walyn aka shiga da ita, inda du suka fito suke zazaune a harabar wajen mai cike da shukoki masu fulawa masu kyau sosai, 

Mutane na kai kawo masu zaman jinya, sai likitoci, sai motar sojoji biyu fa ra biyo su suka dan rarabu suka zagaye asibitin kowane ka dube shi ba alamar ya san kalmar dariya ,

Agaishat dake zaune kusa da Alhinayett ta yi zaman yan makaranta , ta dafe kuncinta da hannunta na dama ta zubawa gazon din wajen ido tana kallo aman fal tunani ne cikin ranta da sumar da Walyn ta yi, har ga Allah hankalinta a tashe yake, me ya samu Walyn din?

Wayar Walyn ce ta dauki tsuwa , Alhinayett ta mike ta mikawa Wardugu tana kule da yanda mijinta ke binta da wani kallon da ba zata iya gane fasararsa ba, aman kallon na bata tsoro itafa tsoronsa take ji, domin a daren jiya ba abinda ya yi mata bacinsu suka sha sosai ko hannunta mai taba ba, amab a yau sai wani kallon gididiga yake binta da shi!

Mahaifiyarta ce ke kiranta, hakan ya sa ya daga ya fada mata suna likita da sunnan GAZOBI sannan ya kashe

Agaishat dake dan satar kallonsa tana mamakin yanda ya amsawa sarakuwarsa, wani a dakile kuma kalmomin basu fi a kirga ba,

Taf, hakan na cikin hukunce hukuncen da zata gindayawa wanda zata aura, walahi au ya girmama iyayenta tamkar nasa au a hakura da auren koma waye, yo ita ina zata iya zama da irin halin wardugu?  Namiji ne da ya fito mata na faman wawura kansu da kafarsu? Ina sam bata son namiji mai kyau da cika ko mai kudin da zai kasance ita kulun hankalinta a tashe yake, namiji ne da dan isar sa mace ko wacece baya duka mata? Du kuwa da irin son da yake mata? So dai ai bai kai wanda yake yiwa Walyn ba, aman ko ita sai ya dankari banza idan hakan ta kama? Anya wardugu na wasa da matarsa irin yanda annabi ya yi? Anya Wardugu nada lokacin sauraron matarsa? Kai ita zata so ta samu namiji irin wa.inda ba ruwansu, wa.inda zasu baka incinka su baka damarka su baka darajarka, 

Ajiyar zuciya ta sauke a lokacin fa ta bude ido ta kale shi ta ga sun yi ido hudu, harare ya watso mata wanda ya bata mamaki da tsoro, me kuma na yi? Shi ne tambayar da ta yiwa kanta.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button