Noor Albi

NOOR ALBI 14

Washe gari gidan da wata irin hidima aka tashi Duk da kusan fiyeda Rabin hidimar a gidan umma Jamila ake yinta Dan ba qaramin Jin auren Nan takeyiba cikin tsakiyar ranta sbd dukkanin burikanta da mafarkantane zasu cika
Duk arzikin dasuke dashi batajin kammaluwar zuciya Kamar yanda take Shirin jinta daga lokacinda ta zama sirika ga AB TURAKI Dan Kamar itace uwa ga momyn kanta bare Sa’adah Dan Haka Bata dauki wannan auren da wasaba ko kadan
Danma anrage musu armashin komai dasu Anne suka nema aure a sirrance kawai batareda anyi hayaniyaba da Allah kadai yasan irin shiri da dukiyar dasuka so bajewa su zubar dan sunsan wannan yanzu ba matsala bane tunda sunsan inda ‘yarsu zataje.

Tunda safe Aka fito da Sa’adah tsakar gidan aka Kuma darje koina jikinta da lalle tareda wasu ruwan qamshi kafin aka Bata ruwa tashiga wanka a toilet din dakinta tana fitowa tasaka Laylah tashiga tayo wanka da sauran ruwan lallen.

Koda qarfe goma ta safiya tayi angama shirya Sa’adah din cikin Alfarma ta manyan kayan mutunci dasukaji asalin dukiya Wanda Anne ce ta Aiko dasu da safiyar tace abawa Sa’adah din tasaka
Dan haka taci adonta tana daukan ido tamkar a ace aurentane za’a daura
Ga mamakinsu Umma Jamila da farin cikinsu ba kamar yanda sukaga tana walwala da farin ciki dauke a fuskarta hakan na musu nunin auren dai ta karba hannu bibbiyu itama Dan Haka suka sake sakin jiki Ana hidima.

Momy kuwa sai bin “yarta take da kallo cikin farin ciki tana qarawa
Fuskarta daukeda murmushi Dan tama kasa gane irin kewar ‘yarta da zatai idan ta tafi itama gashi gobe da ita din za’a tafi da Abban qasar Germany.

Kamar yanda ake cewa Rabo sai mai shi hakama Matar mutum kabarinsa
Andaura Auren MUHAMMAD ABUTURAB TURAKI da ZAINAB MAHMOUD LAYLAH Akan sadaki naira dubu dari cif Wanda Kawu ne ya karba laqadan ba ajalan ba
Hakama babbar Sa’ar da Kawun yasamu akan qudiri da niyarsa na hanawa dangin Zainab sanin komai kamar yanda suka so cin Amana
Kafin su Alhaji Atikun su qaraso yasa aka daura auren batareda anjirasuba Dan dama a masallaci ne Kuma ba wani babban masallaci bane daga shi sai Abdullahi sune dangin Laylah sai Turakin da amintaccen yaronsa A Abdoul sai jamaar Dake masallacin wainda basusan waye angonba bare Amaryar Dan kuwa ko labarin duniya basabi bare su shaida Turakin Dan Haka aure dai andaura yakuma samu jama’a daidai gwargwado dasuka ringa bi da adduar Allah ya sanyawa aure Albarka
Dan Haka Koda su Alhaji Atiku dasu Alhaji Qarami suka iso da manyan motocinsu
Suna fakin Ana Gama shafa addu’ar daurin auren saidai Suka ringa bi da Amin na adduoin da jama’a keyi suna ficewa,

Ransu yayi mummunan baci da hukuncin Kawun na daurin batareda anjirasu ba Amma Turaki agurin sai Basu bayyanarba harda qarin sanin Kar abar Turakin da zaman jira yasa aka daura auren ba Kira badan hakan ba da Kawun sai sun nuna Masa rashin mutunta su day yayi
Dan hakan Kamar tazartawane agaresu.

Washe bakuna Suka hau Yi suna gaggaisawa da Turaki Ana Masa adduar Allah ya sanyawa aure Albarka manyan shaddodinsu sai daukan ido sukeyi Dan kuwa ba laifi kowannensu yanada nasa abun duniyar Amma dogon buri da kwadayi yasa Babu abinda suke gani da hange sai Tarin girma da matsayin Turakin Wanda su connection suke dubawa kafin dukiyar tasa.

Daga gurin daurin auren Kai tsaye gida ya wuce batareda jiran Anne ba wadda zata taho dasu Laylan ya wuce airport ya komawarsa Dan yanada baqin Dake jiransa a Abujan.

Fes Laylah take zaune daki cikin adon Dan lace dinta da aka Bata jiyan saidai batai gangancin fitowaba sbd biki sukeyi gidan sosai har dare tukuna aka Kira Sa’adah din akaita mata nasihu da waazin da sirrikan Kama miji musamman Miji irin nata Wanda aqalla kafin yafara Mata kallon mace ma kila saita kusa hade shekaru nawa a gidan kafin yafara Mata kallon Mata Amma dai sun Yarda da sirrinkansu na kayan gyara dasukai Mata Dan Haka suna jiran kyakkwan labari.

Shiru tayi ta a sauraronsu jikinta duk a mace kukanma takasayi sbd batasan ta Yaya zasuji zancen waye auren yake kansaba
Saidai tasan ko tana hauka bazatai gigin fadar komaiba sbd a yanda tsanar Laylah take cikin jininsu komai zasu iya aikatawa akanta
Shiyasa ta sake roqar Anne da Kawu akan Kar afadawa ko Momy sai lokacinda aka tabbatarda zasu wuce da Abba Germany yanda batada lokaci ko damar sanarwa dangi bare wani mummanan al’amarin ya biyo baya tunda Suma a goben zasu wuce.

Daki Takoma inda ta tararda Laylah tayi sallah tana daga zaune gurin datai sallar
Ta dago ta kalla Sa’adah cikin yanayi na Dan bayyanarda tayata murna tace”

Anty Sa’adah duk ranarda Abba yatashi zaiyi farin cikin ganinki da aure,
Allah ya Sanya alkhairi Anty Sa’adah.

Wani irin murmushi Mai Dan ciwo Sa’adah tasaki tana cewa”

Amin ya Allah qanwata.,
Kuma kinsan kece Zaki ringa yimun dawainiyar kulawa dashi tunda Kinga kin fini iya aikin musamman abinci.

Fararen idanuwanta ta zubawa Anty Sa’adah din cikin jinjina Kai tace”

Eh Zan Miki komaima na aikin gidan Anty Sa’adah Inshallah.

Dafa kanta Sa’adah tayi kawai tana sake murmusawa
Aranta tace”

Tabbas wannan shine bahaguwar sauyin qaddara,
Anmiki aure batareda kinsan kece matarba,
Zakije gidanki da sunan ‘yar riqon ‘yayarki da kikewa kallon nice Matar,
Nikuma daga aure naqare a zuman riqo gidan Auren qanwa
Wannan badan akwai zumunci ba da dawane suna zasu Kira wannan sauyin lamarin.?.

Gidan umma Jamila ta kwana sbd goben da safe su Momy zasu fara wucewa kafin suma su wuce
Dan Haka duk wani saura ragamar rayuwar Sa’adah umma Jamilan tagama karbarsa daga yau din tunda momyn dai zatabi Abban bayan irin hanatan dasu umma Jamilan da Haj Karima basuyiba har fushi sukaso Yi da ita akan zata kassara sauran rayuwarta gurin jinyar Wanda gurin Cin Amanarta da son zuciyarsa ya hadu da hukuncin dasuke ganin Allah yayimasa akan abinda yayiwa momyn
Amma sbd zamtowarta sirikar Turaki yasa Suka danne fushinsu Dan yanzu Kam zata wuce rainin kowa duk da sunsan har abada sune masu juya momyn sai abinda sukace Mata takeyi.

A Daren Momy tasake jaddadawa Sa’adah komai nata yanzu su umma Jamila ne
Tunda batanan yanzu sune iyaye Kuma gatanta Dan Haka karta ringa komai batareda shawararsu ba
Itadai Sa’adah to kawai take cewa sai alokacin nema tasamu ta rungeme Momy tasaki kukan data keta dannewa aranta tun jiyan ga Kuma kewar mahaifiyarta dazatai dama mahaifin nasu da Babu tabbacin zasu sake haduwa dashi tunda ciwone Babu Wanda yasan yanda Allah zaiyi dashi,
Wani irin nauyi takeji aranta shiyasa ta qanqame momyn tana sake kuka siriri Mai tsananin tsima zuciya Amma su umma Jamila Kam Babu wani Abu dasukaji a zuciyarsu saima rarrashin dasuke Mata akan ai aure bautar Mata ne taje ta Kama uwar mijinta da kyau Dan kuwa mace ce Mai tsananin iko da kaida,
Sam Bata daukan Wasa ko shirme
Komai nata Kai tsaye take yinsa.

Sai datai kuka sosai har idanuwanta sukai nauyi ajikin momyn kafin ta saketa tanajin wasai a zuciyarta
Duk nauyi da radadin datake ji ya sauka gabaki daya tasauke Ajiyar zuciya tareda miqewa ta nufi dakinta tana Jin komai ya Kau akanta sai Kuma fuskantar sabuwar rayuwar Dake jiransu a Gidan riqonsu
Dan kuwa tasan Laylah ma dai kamar riqo ne za’ai Mata Dan maganar auren Anne tace ba yanzu zaaita ba lafiya da ilimi zasu kutsar da ita ciki.
Da wannan tayi adduarta ta kwanta ranta ba wata doguwar damuwa Dan kuwa tasan kyakkyawar rayuwarda mahaifinsu ke musu buri da fata zasuyi ta samun ilimi Mai inganci da zurfi.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button