JIDDATUL KHAIRJIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

JIDDATUL KHAIR 56

Bayan few minutes Ramlah ta sake komawa ta leka compound sai bata ga Hajja ba, wani ajiyar xuciya ta sauke ta wuce dakin da Jiddah take, tana cire Uniform ta sameta, Ramlah ta jingina da kofa tace “Toh Aneesah ta maki wani abu ne da baxa ki je gidan nata ba Jiddah?” Jiddah taki kallonta tace “Bata min komai ba, kawai dai baxan je bane…” Ramlah tace “Amma ai nace idan ma kin rakatan xa ki iya kin shiga

kiyi tsayuwarki a waje har ta fito” Jiddah tace “Kofar gidan ma baxan iya tsayawa ba” Murmushi kawai Ramlah tayi ta juya ta fita daga dakin. Ranan Friday da daddare Aneesah na xaune parlor downstairs bayan Magrib tana kallon wani indian Series tana shan fruit salad, ta ji footstep ana saukowa downstairs din, daga kai tayi ta gansa yana sakkowa, lkci daya kamshinsa ya baxa ko wani lungu da sako na parlon,

kafin tace komai yace “You still haven’t pray Aneesah” Tace “I know, ina xaka je da daddaren nan haka Captain?” Ya shafa beard dinsa yace “Wajen Budurwa ta” tayi wani dariyar da bata shirya ba tace “Hmm, kar Allah ya nuna min wannan bakar ranan, ni fa kasan wani abu captain?” Yana sakkowa yace “Sai kin fada” tace “Wllh duk ranan da yau aka ce da gaske kayi wata budurwa Allah xan iya kashe koma wacece

har lahira, sai dai nima a daureni….” Yana kallonta bayan ya sakko parlon yace “Toh duk ranan da aka ce nayi wani auren fa?” Ta kallesa kamar baxata ce komai ba don gaba daya mood dinta ya canxa, sai kuma tace “Wai ka auri wata matar a duniya bayan ni?” Yace “Ehh” Wani murmushin ta kuma yi tace “Gwara a bar xancen kawai Captain…” Sai kuma ta hade rai tace “Kasan Allah? Wllh wllh xan iya kasheta in kashe kaina sannan kai ma in kashe ka duk mu hadu a lahira” Da mamaki ya dinga kallonta ganin how serious she is, cikin bacin rai tace “Wllh duk ka bata min mood wnn xancen da kayi captain, mu fa kaf xuri’armu

fa ba a mana kishiya wllh, Aunty Salaha ma da aka yi ma satin amaryar uku ta bar gidan babu wanda ya koreta” Shi dai Abuturrab kallonta kawai yake ganin da gaske ran nata ya baci sosai, D’an murmushi yyi yace “Sai na dawo…” Ta mike babu yabo babu fallasa tace “Wai ina xaka da daddaren nan ne?” Yace “Ban ma Umma sallama ba, daxu gida kawai naje” kauda kai tayi ta ta6e baki, sai kuma ta kallesa tace
“Toh bari in saka hijab mu je tunda ban ta6a xuwa gidan nata ba dama” Yace “No, ni kadai xanje, duk ranan da kika shirya sai kije ki gaisheta” Da mamaki take kallonsa tace “Ban gane No ba, yanxun idan

naje laifi ne?” Yace “Eh saboda sai da xanje mata sallama sannan kika san xaki gaisheta” Bai jira cewarta ba ya nufi kofa ta bi sa da wani irin kallo xancensa na sake yawo a kanta wai duk ranan da aka ce yayi wata matar fa?? Tabb shi me ma ya kai sa fadin wannan mugun xance, ai daga ita ya rufe aure har karshen rayuwarsa, ita ce first and last dinsa, shi din nata ne ita kadai, tsaki tayi ta koma ta xauna ta ci

gaba da kallonta amma ba cikin dadin rai ba… Abuturrab na parking ya dau wayarsa yayi dialing number ya kai kunne, wayar na fara ring aka daga, ya amsa gaisuwarta yace “Ki turo ta ta amsar maku sako!” Ramlah tace “Wa xan turo yaya?” Yace “Warce ke gidanki” Kallon agogo tayi don anyi isha, sai kuma ta mike ta fita xuwa dakin Jiddah, Jiddah ta gama sa kayan baccinta kenan tana shafa turare kafin ta dau

takardanta ta fara karatu saboda exams da take da shi gobe Ramlah ta shigo, tsaye Ramlah tayi bakin kofar tana kallonta, Jiddah ta ajiye turaren hannunta tace “You need something?” Ramlah tace “Wai sako xaki amso a kofar gida” Jiddah ta dinga kallonta tace “Sako kuma? Sakon me? Kuma wajen wa?” Ramlah tace “Ya Aliyu” sosai gaban Jiddah ya fadi jin sunan da Ramlah ta ambato, Jiddah ta girgixa kai

tace “Sakon me da daddaren nan, maimakon kice ya shigo da shi ki amsa don Allah, ji fa karfe nawa” Ramlah dai ta ma rasa abinda xata ce, Jiddah ta tafi ta dau takardanta ta xauna gefen gado, irin ita baxata je din nan ba, wayar Ramlah dake hannunta ne ya fara ring, ta daga ta sa handsfree tana kallon Jiddah, daga daya bangaren yace “Kuna bata min lokaci” Ramlah ta d’an fara kame kame, sai kuma tace

“Yaya ko dai in fito in amsa ni? ita naga ta kwanta ne” Calmly yace “Taso ta” Tace “Wai dama exams…” Katse ta yyi yace “Ki taso ta nace” a hankali tace “Toh Yaya” ya katse wayar, Ramlah ta kalli Jiddah da ta 6ata fuska kamar xata yi kuka jin duk abinda yace, cikin rawar murya tace “Bayan ya Ahmad bai sani ba xan je kofar gida amsan sako, to gwara ki kirasa ni dai” Ramlah ta xaro ido tace “Ince masa me, salon ya

kira yayan?? ke dai kawai ki sa hijab dinki ki daure kije kiga sakon meye” Jiddah ta girgixa kai da kyar tace “Ni baxan iya fita ba wllh, dubi fa agogo” Ramlah tace “Toh me kike so in ce masa bayan kinji yanda

muka yi da shi Jiddah” Jiddah ta kwanta kan gadon ta lullube tace “Da gaske fa ni baxan je ba kawai ki kashe wayarki gaba daya, tun da rana me yasa bai kawo sakon ba” Ramlah dai ta rasa abun cewa tana ta tsaye, sai ga kiransa ya sake shigowa, ta xaro ido tace “Na shiga uku Jiddah ki rufa min asiri ki tashi kije,

ni dama ba ni ya kira ba, bakin gate ne fa kawai xaki tsaya ya baki sakon da yace ki juyo ki shigo, wllh ban san kuma me xance masa ba idan na daga kiran nan” Ganin ya kusa katsewa ta daga tana rawar baki tace “Yaya na kuma ga tana wanka ne…” Yace “Ramlah” ta xaro ido tace “Na’am yaya” Yace “Mika mata

wayar” karasawa tayi ta ajiye wayar kusa da Jiddah tace “Ga ta” Jiddah tayi narai narai da ido tana sauraronsa, yace “Fito ki amshi abinda nace yanxu, minti biyu na baki…” daga haka ya katse wayar, Jiddah ta mike xaune har hawaye ya kawo idonta, Ramlah na lallabata tace “Ki daure ki je pls Jiddah ai

nan da kofar gida ne, kawai yana mika maki sai ki shigo kin ji” Mikewa Jiddah tayi daga kan gadon ta bude wajen kayanta ta dau hijab har kasa ta saka sannan ta fita, tun da ta isa gate gabanta ke faduwa, tana fita taga motarsa ta karasa tana tafiya slowly ta tsaya kusa da motar ta tsaya, sauke glass yayi yace

“Shigo ki amsa” kamar xata yi kuka tace “Don Allah ka bani a nan, wllh ya Ahmad….” Yana kallonta directly in the eyes yace “Shiga nace” Sosai hankalinta ya tashi ta rasa yanda xata yi, da kansa taga ya

bude motar ta matsa gefe ganin kallon da yake mata sai kawai ta shiga xuciyarta na bugawa, amma bata kulle motar ba, yace “Kulle min mota” Ta xaro ido tace “Don girman Allah ka bani sakon in koma wllh karatu nake gobe ina da exams, kaga dare yayi” da kansa ya kulle motar ya tada motar, hawaye ya shiga

sauka idonta tace “Na shiga uku don Allah ka bude min in fita” barin layin yayi ba tare da ya saurareta ba, ta fashe da kuka sosai tana kallonsa cikin tashin hankali…. Bai ko kalleta ba ya ci gaba da driving dinsa, jingina tayi da kujeran motar tana kuka a hankali, bayan tafiyar kusan minti ashirin taga sun shiga wani katon shopping mall wanda wajen kamar da rana saboda fitilu da ya haska ko ina, ya nemi waje yyi

parking ita dai bin wajen take da kallo gabanta na faduwa, sauka yyi daga motar ya xaga ta inda take ya bude motar, kasa kallonsa tayi shi kuma bai ce mata komai ba, bayan few seconds ta goge idonta ta sauka daga motar ya kulle, tafiya ya fara, da farko ta d’an yi jim ta bi sa da kallo, amma tsoron kada ya

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button