WUTSIYAR RAKUMI 27

Zaune yake tacan bayan ɗakunan sashen Attahir inda bayajiyo hayaniyar sosai, wajen Attahir ya gyarasa sosai saboda hutawa, kansa jingine da kujera ido a lumshe ya tafi duniyar tunani.
Sautin takun mutum ya fara jiyowa kafin zazzaƙar muryar ta mai fita da nutsuwa, sosai gabansa ya faɗi danjin muryar da bazai taɓa mantawaba, ya tabbata ko a cikin barci ya jita saiya gane balle a zahiri. Ya kuma buɗe hancinsa yana zuƙar mayataccen ƙamshin Khumra daya haɗu da turare a jikinta.
Dukda ƙwaɗayin ganin mamallakiyar muryar da yakeyi hakan baisashi yin ko motsiba balle buɗe idanu saboda tsabar miskilanci da jin kai.
Sam Ummukulsoom bata lura da mutum ba a wajen, dan haka take kuma narke murya tana zubama Baba shagwaɓa akan rashin zuwansa walimar, sannan babu ko ɗaya daga cikin yayunta da yazo, danma Inna harira da Aziza na nan.
Kasa jurewa da zuciyarsa tayine, yasakashi Buɗe idanunsa a hankali, akan bayanta data juya masa ya sauke, yanda rigar ta fita da ainahin surarta ne yasaka numfashinsa yin sama yay kasa saida yay kokawar tarbosa ya haɗiyi yawu dake neman daskare masa da a ƙirji, sam duk yanda yaso ɗauke idonsa ya kasa, babban burinsama ta juyo yaga wacece ita….
Isowar Zaid wajen batareda Ummukulsoom ta fargaba yasata tsorata ta ɗan zabura tana yanke wayar.
Saurin riko hannunta Zaid yayi ganin zata zube ƙasa saboda tuzguɗewar da takalman ƙafarta sukayi kasan cewarsu masu tsini..
Tai azamar son fizge hannunta ta dafa flowers ɗin dake wajen, dan bata buƙatar yaya Zaid ya taɓata, sai dai kuma aka samu akasi ɗayan takalmin ma ya tuzguɗe tai baya zata faɗi gaba ɗayanta.
Shi kansa baisan lokacin daya baro inda yake zauneba yazo yay azamar fisgota ta faɗo jikinsa saboda ganin Zaid na shirin haɗata da jikinsa danya bata taimako daga faɗuwar da take shirin yin.
Da ƙarfi Ummukulsoom ta rumtse idanunta saboda takaicin faruwar abinda take gudu fiyema da zatonta, sai dai abinda ya ɗaure kanta sam ba ƙamshin turaren Yaya Zaid take shaƙaba, jikinma yasha banban dana yaya Zaid ɗin zata iya cewa.
Ƙoƙarin janye jikinta tayi yay saurin fara tureta yana haɗe fuska fiye da ko yaushe, kafin yaja siririn tsaki batareda ya ko kalli fuskartaba ya raɓa gefenta yabar wajan yana harar Zaid dake tsaye kamar gunki yana kallon ikon ALLAH daga Yaya Amaan, shi sam baiga sanda yazo wajenba, sai Ummukulsoom daya gani kwance a ƙirji sa.
Baki hangame Ummukulsoom tabi bayansa da kallo, cikin takaicin tsoron da Zaid yazama silar bata tace, “Shikuma wannan dangin tsakar daga ina? Waya bashi lasisin taɓani ma?”.
Dukda yayi taku kusan biyar a tsakaninsu hakan bai hanashi jin abinda taceba, dan haka ya tsaya cak furucinta na dukan ƙahon zuciyarsa da ƙarfi….
Azamar saka hannu Zaid yayi a bakinta jin zata kuma wani magana, ya ja hannunta suka shige ƙofar kicin din Maman Ahmad dake a wajen.
Hakanne yasa koda Amaan ya juyo domin ganin wannan tsagerar yarinyar sai yaga shigewarsu ciki kawai, da ƙarfi ya rumtse idanunsa tareda shafar girarsa da ɗan yatsa ya yarfar da hannun………
“Ajiwa dama kana nan naketa nemanka?”.
Haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa yayi sannan ya buɗe idanunsa dake a rumtse da harsun fara canja launi.
Attahir da yay maganar ne ya kuma kafesa da idanu saboda mamakin yanayin daya ganshi, “Ajiwa lafiya kuwa?”.
Batare da yasan maganar ta subuto daga bakinsa ba yace, “Yaushe Zaid yayi aure ban saniba?”.
“Aure kuma? Zaid ɗinne zaiyi aure baka saniba? To miyasama kamin wannan tambayar?”.
Fahimtar kato ɓarar da yake nemanyine yasakashi maidama Attahir amsarsa da harara ya raɓa gefensa yabar wajen.
Da kallo kawai Attahir ya iya binsa, yayinda yake juya kalmar auren Zaid ɗin da Amaan yayi a ransa, yaɗan ɗage kafaɗa da taɓe baki alamar shiyya sani yajuya shima yabi bayansa.
Su Ummukulsoom kam na shiga ta ture hannun Zaid dake kan bakinta tana fusge hannunta, “Yaya Zaid dan ALLAH kabar min irin haka banaso wlhy”.
“Yi hakuri Ummukulsoom wlhy nima bada niyya nayiba, gani nai zaki ƙwanto mana ruwa haka kawai, kinsan kuwa wanene kike jifa da kalmar dangin tsaka?”.
Cikin halin ko in kula tace, “Oho yaya Zaid, nidai koma wanene ai gaskiya na faɗa, haka kawai yakama mana tsaki wani yace ya taimakeni? Ya barni na faɗin mana ai dai jikinane, ALLAH ya isana ma taɓanin da yay wlhy”.
Sosai Zaid ya waro idanu yana hangame baki, sai dai kuma tai gaba ta fice binta tana gyara zaman ɗan kwalinta ranta duk a dagule, dolene ta cire kunya ta takama Zaid burki bisaga take-takensa da take gani, dan bazataso yazama sahun farko a cikin jerin mazan da zata ja a ƙasa ba kodan mutuncin ahalinsa a idonta.
Binta da kallo yay harta fice, ya dafe kai tare da zubewa cikin kujerar falon, shikam baisan wane irin so yakema yarinyarnanba, amma sam takasa fahimtarsa tunba yauba, dukda iyakar iyawa yana yaɗa manufofinsa a zahiri gareta.
Ummukulsoom kam na fita taci karo da Maman Ahmad data taho kiranta saboda ana bukatarta a wajen………✍????
Asha hutun ƙarshen mako lahiya????????????????♀️⛹????♀️⛹????♀️⛹????♀️.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????