NOVELSUncategorized

MAMUHGEE 1

*_1_*
Bismillahir-rahmanir Raheem.


Sauri yake faman zubawa Amma yanda saurin nasa yake tamkar Yana gudune sbd yanda ko gani bayayi sosai ga babbar rigarsa sai cika takeyi da iska tana qarawa,


Da safe kafin yafita jin zuciyarsa yakeyi fes sbd tunanin yau ranar sa’arsace tunda zasuje maula gidan mai arzikin da yafi kowane mai kudin jahar kudi harma dana wasu jahohin saigashi masifar datafi ha’darin mashin bala’i ta afko masa Dan gwara yasan sama mashin yayi dashi ya zubar akan abinda rashin hakurinsa yaja masa ayau din,

Yana shanyo kwanar layin gidansa wani mugun zufa ya yanko masa ya tattaro kuzari da qarfin hali yacigaba da tafiya Yana kallon tarin kalolin ‘yan ta’addar dake cike da qofar gidansa sun baje sunashan iskar makeken bishiyar durumin dake qofar gidan  kusan su goma Sha biyar kowanne da kalar mugun makamin dake soke cikin qugunsa ko wani sashe na jikinsa Wanda duk qaddara takaisa shiga huruminsu yanxune zasu yiwa rayuwarsa illa Kuma ba Wanda ya isa ya tanka sbd hukumar ma da ikonta suke aiki sbd zakinsu shine amintaccen yaron DIKKO DILLA.

Wasu daga cikinsu fuskokinsu cike sukeda zanen Sara ko Suka haka jikinsu kusanma Babu Wanda fuskarsa bazata saka mai qaramin qarfin jini zawoba sbd Sam babu alamar wasa atareda fuskokinsu ga wani irin warin daga da wiwi dake tashi tun daga farkon layin unguwar shiyasa yawanci duk Wanda yake Dan asalin gari yasan anguwar ba wurin ganganci bace anguwar sarki ZAKI NEYO ce Sam ba’a mata garaje.

Da gudu gudu sauri sauri yaqarasa shigowa gidan tsohuwar babbar rigarsa kalar ruwan madara data koma kalar brown tana sake dibar iska sbd sauri dayake diba kamar zai tashi sama musamman yanzu daya qara ganin bataliyar ‘yan daban dake qofar gidansa kamar qofar gidan wani qaura.

Yana shiga tsakar gidan sbd tsantsar rudewar dayake ciki ya kwashi wani mugun tuntunbe saura qiris ya kife cikin garinda iya talatu ta shanya na kayan mata datake siyarwa duk da duk rabi garin kukane take zubawa sbd yayi mata afkin siyarwa. 

Zaune take tana lissafin jarkar tsimin data Saida wadda duk rabi jollyjus ne ta zuba aciki shima sbd afki.

Kallonsa tayi amatuqar sheqe cikin takaicin yanda ya tashi goga mata asara ta hanyar barar mata da gari a ‘dan hasale tace”

Wai meye hakane kaketa muzurai kana rawar jiki kamar 6arawon daya ha’diyi kunama?,
Yanzu wannan garin dakake Shirin bararmin kasan hasarar nawane zaka jazamin Wanda nasan ko shekara zakayi kana sana’ar taka ta mutuwar zuciya bazaka Tara kudin biyana ba inyi magana jarabben sarkin gidannan yace bayason hayaniya kokuma yakamamin dabbobi yasa ayanke masa inaji Ina gani qatti suci banza.

To wlh banshirya hasaraba kusa Dan haka kafita idona inrufe.

Takalmin hannunsa ya fitar daga cikin babbar rigarsa data gama jiqewa da zufa,
zufa na qara tsatsafo masa Yana zare qananun idanuwansa dasukafi kama Dana Chinese din hauren qasa yace”

Qaddara takaini daukar aron takalmin ZAKI NEYO wainda kikaji dahiru yace dubu biyar suke nafita dasu wlh sun katse fata fata duka qafar biyu gurin gudun mahaukatan Karnukan da alhaji dikko dillah yasa aka sakarmasa ga yan maula da mabaratan dasuka tarar masa qofar gidansa duk da tarin yan sandan dake gadin gidan.

Wani irin sabon qululun baqin ciki da takaicine ya quleta tana watsa masa wani mugun kallon takaici baqin ciki yahanata ce masa qala sbd duk iya quluwa da baci ranta yayi sbd sanin masifar da hakan zai jawo
ta miqe ta tahau tattara kan akuyoyinta da kajinta dake walwalarsu filin tsakiyar gidan Dan tasan yau akwai saukar aradu a gidan Dan yau ko butar gidan saita ci uwarta idanba Allah ya tsareba baresu
Akuyoyinta da kajinta kuwa tasan tsaf zai take mata kawunansu su mace abanza,
Tana zaman zamanta rukayya taje Lagos ko wata shegiyar qasar ta hado jini da kafirai kokuma qila wata qabilar anxo anhaife mata masifar daba ita kadai ta addababa har yan gari da anguwa Dan kuwa neyo ba ubanda baya tsoro da shakkarsa ga wani irin kwarjini dayake qarawa mutane tsoronsa.

Wani Dan dakin kaji ta gargadasu gabaki daya ta rufe da kwado ta zare mukullin ta dawo tafara tattara garinta tana kwashewa cikin takaici da baqin cikin dake tafasa zuciyarta ta bude murya tace”

NADIA uwar uban me kikeyi a bakin murhun haryanzu dabazaki taso kitayani tattara duk wani tattalin arzikina dake tsakiyar gidan nanba kinaji mara danganar ubanki ya ballo Mana balain dayafi 1990 masifa.

Aje plate din robar dake hannunta tana fifita wutar murhu dashi tayi ta taso gabanta na matuqar faduwa sbd jikinta dayayi sanyi dajin abinda babansu yayi Dan tanajinsa duk abinda yake fadawa iya talatun koba komai tasan idanba Allah ne ya fiddataba akantane zaifi sauke haushinsa tunda itace mara galihu agidan Dan idan yafara kowa shigewa daki yake ranar bamai fitowa saiyagama fushinsa ya sauka ita kuwa dole take fitowa sbd balain iya talatu shiyasa idan tafito yake sauke Rabin haushinsa akanta ga wani irin mugun tsoronsa da shakkarsa da Allah ya halitta a dukkanin zuciyoyin ‘yan gidan harma Dana waje saidai zata iya cewa itakam tsoronta yafi nakowa duk da dai duk balai da msifar iya talatu da duk anguwar ake tsoro itama shakkarsa takeyi.

Jikinta na Dan rawa tafara tattarawa iya talatu kayanta..

Da ‘yar waqar sani sabulu wata ‘yar budurwa tashigo gidan taci ado cikin Riga da skirt na atampar sheraton ‘yar dubu uku da dari biyar fuskarta a kimtse tsaf da kwalliyar dataji hoda da foundation datai mata kyau ba laifi da Jan jambaki 24 hours hannunta riqeda Jakarta da ‘yar wayarta vivo mai Dan dama dama sai qamshin bokhour takeyi daga gani cikin nishadi tadawo.

Cak ta tsaya tsakiyar gidan tareda kallonsu cikin mamaki da ‘yar fargaba ganin sai tattara kayan tsakiyar gidan sukeyi fuskar iya talatu ba alamar rahama ko kadan ta maida kallonta kan babansu dake tsaye gefe sai zufa yakeyi kamar Wanda yaci wuta takalli iya talatu tace,

Iya lafiya kuke kakkamta kaya rana tsaka?

Harara iya talatu tafara watsawa dattiya dake tsaye har lokacin kafin tace,

Rashin hakurinsa yakaisa ga daukar takalmin ZAKI NEYO yasa yaje yawon maula aka hadosu da miyagun karnuka sukaiwa takalmin fatafata…..

Kallon babansu tayi cikeda takaicin Rashin danganarsa da ako yaushe baya jawo musu alkhairi sbd fargaba da tsoron masifar daya jawo musu basujiba basu ganiba ta turo baki tace,

Nikam baba meyasa bakason ko yaushe a zauna lafiya agidannan gashi yanzu mutum saiya kwana biyu bai wani dogon motsiba sbd tashin hankalin yaya neyo
Yanzu wlh ko mai neman aurena yazo qofar gidannan saiya gwammaci karo da mahaukacin matashin kare akan fushin wannan abin daka yi baba.

Kallon iya talatu tayi cikin takaici tace,

Ni wlh nakoma gidansu anty saratu sai dare ko gobe zandawo Dan wlh bazan yarda a mari wannan kyakkyawar fuskar tawa abanzaba tunda babu Wanda yake siyamun mai.

Juyawa tayi rai abace cikin haushi da takaici ta fice tabar gidan tana guna guni sbd tasan tsaf da marin neyo gwara mashin yayi sama dakai.

Nadia kuwa cikin sanyin jiki duk takai ma iya kayanta daki tadawo ta gaban baban nasu dake tsaye Yana muzuran ido cikin mirsisi yace,

Ke ungo nan yi musu dubara da allura da zare ki dinkesu kikai dakinsa ki ajiye masa Kuma wlh duk rintsi Kar shegen dayace nine nasakasu.

‘dagowa tayi da sauri takallesa da manyan fararen idanuwanta cikin tashin hankali.

Harara ya watsa mata yace,

Bazakiyi bane kike kallona kamar nace ki kashe mutum.

Sunkuyar da kanta tayi tareda girgizawa idanuwanta na cikowa da hawaye ta karba da hannu biyu ta wuce.

baza babbar rigarsa yayi tareda kada mata iska ya fada dakin iya talatu Yana sharce zufan daya kasa daina jiqasa.

Nadia kuwa bakin akurkin dakinta ta zauna bayan tadauko allura da zare tahau yiwa takalman kwaskwarima jikinta na matuqar rawa sbd sanin yau kwanan wahala zatayi idan yadawo yaga wannan dinkin a jikin takalmansa bayan antsinka.



‘Daga takalmin tayi ta qura masa ido tsawon mintuna hudu kafin ta sake sakin ajiyar zuciya akaro na Babu adadi bayan zamanta na Shirin dinkin takalmin.

Iya talatu dake zaune ha’deda rai zuciyarta na qara cika da takaicinsa ta harari qafafunsa cikin quluwa tace”

Kaga nidai yi daga can gefe karka takani da wannan qafafun naka dasukafi kama da kofato,
Kuma wlh kasani matuqar Zaki yayi mummunan sauke mana balainsa aka gogamin asara wlh saikaji a aljihunka da cikinka Dan wlh sainayi sati banbaka tuwonaba tunda zuciyarka tagama mutuwa Sam ko kunya bakaji kullum Kaine daga ha’darin mashin sai karo da keke kokuma gudun fanfalaqin ceton rai duk gurin yawon maular mutuwar zuciya.

Bai kulataba yahau cire babbar tsohuwar rigarsa dake sharkaf da zufa duk saita qara canxa kala.

Ficewa yayi ya dauki buta ya nufi bayin dake tsakiyar gidan ya fito ya zauna ya wanke qafafunsa da ako yaushe talatu ke shammata sbd shegen yawonsu dashima yasan yanadashi sbd idan ya bazama cikin gari yafara yawo sai Rana ta fadi yake dawowa gida wanda wani lokacin wahalar banzace yakeyi sbd haryagamo gantalinsa yadawo bayasamo ko nera biyar.

Yana cikin wankin qafar yajiyo qarar fito Yana dosowa cikin gidan qafa daya dama ya wanke zaifara ta biyun yaji fiton Yana sake dosowa cikin gidan atake ya aje butar ya miqe sukai ido hudu da Nadia dake zaune tana kallonsa cikeda tausayin kanta na aikin daya data.

Cikeda borin kunya ya dauke Kai daga kallonta ya nufi dakinsa da iya talatu yashige bai tsaya wanke dayar qafarba tunanin qila Zaki ne yadawo duk da yasan Zaki Sam baya fito sbd tsabar mulkin dayake murzawa a dabanci Dan ko wani hakimin bai kaisa baza mulkiba atasa duniyar ta ‘yandaba Wanda shiyasa ake kiransa da sarki Zaki.

Itadai iya talatu Bata sake kallonsa ba sbd tana lureda duk hankalinsa duk ba kwance yakeba sbd abinda yayi din Saidai bazatayi masa mgn ba qyalesa zatayi ai zakin shine daidan kowane dan banza na gidan Dana waje.

Cigaba tayida hada garin kayan matanta tana daurawa a leda batareda ta kalli ko inda take zaune Yana qoqarin shafawa qafafuwan nasa Vaseline kamar Wanda zaije wani gurin.

Lalah ne yashigo gidan Yana fito daukeda wata baqar leda ta kayan neyo daya daya karbo masa guga sbd akwaisu da babbar hidima sbd AMBY DIKKO DILLA na gari Kuma zakinsu shine babban yaronsa dayafi yarda dashi da boyayyun ayyukansa.

Dakin zakin dake farkon shigowa ta zauren gidan ya shiga ya ajiye masa kayan kan katifa yafito ya jawo qyauren dakin.

Harzai fice ya dakata tareda juyowa da sauri ya kalli Nadia dake riqeda takalmin Zaki da aka siyo masa daga kaduna….

Baki ya sake cikeda mamaki da tantama ya dawo gabanta ya tsaya Yana kallon hannunta dake riqedasu Yana rawa alamar amatuqar tsorace take.

Cikin tsananin mamaki da muryarsa irinta riqaqqun yan ta’adda yace”

Wannan meyene a hannunki?? Yana nunawa da hannunsa sbd sanin ba magana takeyiba.

Jikinta har wani irin rawa yakeyi sbd tsananin halinda zuciyarta da gangar jikinta suke ciki
 hannu na rawa ta daga zata nuna qofar dakin babansu saita tuno da gargadinsa tayi saurin sauke hannu tana sake qanqame takalman.

Amasife yace”

Ke ubanwane yace ki shiga dakin sarki harki dauko wannan takalmin Dan……zaro manyan jajayen idanuwansa yayi sbd sai alokacin ya lurada yanda suke ya hadiye wani yawu cikin jinjina mata yace”

Wlh idan ko sunana yafito acikin Wainda suka gani saina qarasa mayarda maraji bayan Rashin magnar dakike fama dashi.

Ficewa yayi Yana jinjina mata Dan kuwa ba qaramin jarumtar tabama takalmin tayiba.

Yana fita qofar gidan atake ya tseguntawa Nanu Yana cewa”

Babahh yaufa akwai saukar aradu a cikin gida da anguwarnan mubi ahankali Dan kuwa yau antabo sarki inda ba’a tabowa.

Cikin gidan kuwa jiki a salube ta tashi ta sidada dakinsa ta ajiye daga ciki bakin qofa tadawo cikin gida taci gaba da aikin tuwon iya talatu na siyarwa da dare jikinta amatuqar sanyaye Dan har wani zazzabi takeji.
##Mamuh..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button