Labarai

Yadda Wani Malamin Tsubbu Ya Dirkawa Abokiyar Huldarsa Ciki Da Aurenta

Wani Magidanci da matarsa ta kaishi wajen wani boka da sunan Malami domin neman taimakon haihuwa, daga karshe dai Malamin shi yayiwa matar mutumin ciki.

Al’amarin ya farune a wani gari dake yankin Arewacin Nijeriya ya bar Malamin tsumbun da mai matan cikin rigimar da suka tanawa junansu asiri.

Kamar yadda mai bamu labarin ya sanar damu. Matar mutumince ta yiwa mijinta tayin ganin Malamin domin neman taimakon haihuwa ganin dukkaninsu suna da lafiya amma haihuwa yaki samuwa. Garin zuwa neman maganin ne Boka ya ribaci matar auren yayi ta zina da ita har ciki ya shiga. Shi kuma mijin ya hadashi da wasu jijiyoyi da tawada yana amfani da su da sunan maganin da zasu bashi haihuwa.

Sai dai asirin bokan ya tonu ne bayan da na kusa da matan dake neman haihuwar ta tona zancen a gaban wasu matan a lokacin da suka saba wata yar matsala na bacin rai sai kawai ta tona zancen daman kuma itace ta baiwa kawarta ta shawaran zuwa wajen Malamin na Tsubbu.

Yanzu haka da rigama ta kacame a tsakanin Miji da mata da kuma bokan inji wanda ya sanar damu labarin.

Idan muka samu ci gaban labarin yadda ta kaya zamu kawo.

Tabbas duk matar da zata maida malaman Tsubbu abokan huldanta, sai ta zama abokiyar zinarsu kowacece kuwa ita, kuma komai tsufanta.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button