LabaraiMtnPulseTech

Yadda Zaka Sayi 1.2Gb A 150, 350Mb A 50 A Layin Mtn

Assalamu alaikum yan uwa barkan ku da wara haka da fatan kuna lafiya.

Kamar yadda muka saba kawo muku garabasa da kuma yadda zaku saya data cikin sauki yauma ina tafe muku da wani sabon hanya yadda zaku sayi data me saukin gaske a layin ku na mtn.

Wanda zai baku damar sayan data 1.2gb a naira 150 kachal sai kuma zaku iya sayan 350 a naira 50.

Wannan datan wadan da suke cikin tsarin mtn pulse ne kadai zasu iya saya kaga idan kaima kana son ka mori wannan datar saika garzaya zuwa tsarin mpulse.

Tsarin mtn pulse tsari ne wanda yakeda sauki wajen kira dan suna cajar 11kb per sec ne kaga duk minti 1 naira 6 kaga zaka ci riba biyu dan zaka sayi data me sauki kuma ga sauki wajen kira.

Kuma wannan datar baya zaban layi indai layin ka yana tsarin mtn pulse to zaka iya saya.

1 Domin shiga tsarin mtn pulse kaje wajen tura sako saika rubuta mpulse saika turawa wannan number 131.

ko kuma ku danna *344*1# ko kuma ku danna *123*2*3#.

Ko kuma ku shiga myMTN App ku shiga Other Plan saiku zabi Mpulse.

Bayan kun koma tsarin saiku danna *344# saiku zabi number 2 idan ya bude saiku sake danna number 1 zai nuna muku adadin datan da zaku saya kamar haka.

Kamar yadda kuka gani na 50 yana kwana 7 na 150 yana kwana 30 saiku wanda kuke so ku saya atake zakuga sun baku kamar haka.

Ku sani wannan datar yana amfani ne a iya website na mpulse amma kamar yadda nace zan gwada muku yadda zakuyi amfani dashinya bude muku ko wani app da sauran.

Abun ba wani wahala cikin kankanin lokaci zaka saita yadda zakayi amfani dashi ya bude muku komai ma ana kuyi komai da datar.

Yadda Zakuyi Amfani Da Datar Kuyi Komai Dashi.

Da farko ku sauke app dinnan me suna stark vpn anan DOWNLOAD bayan kun sauke saiku bude ta.

Saika taba wannan waje dana nuna da zanen.

Sai kayi kasa ka duba a hankali zaka inda aka rubuta Mtn Pulse 2022 saika danna.

Saika sake dannan wajen dana nuna da zanen kadan jira zaka ga yayi connected shikenan saika cigaba da amfani dashi Allah bada sa a.

Idan kana da tambaya zaka iya aje mana a kasa.

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button