Labarai

‘Yan Sanda Sun Tasa Keyar Wani Malamin Da Yayi Sallar Idi A Yau A Garin Sokoto 

Daga Bin Saluhu Garu

Uban Kasar Gada ta Jahar Sakkwato Yasa Jami’an Tsaro Sun Ciko Hannu da Wani Limani Da Yayi Sallah Yau Lahadi….

Biyo Bayan Tabbacin da Limamin Wani Gari da Ake Kira da ƊAN_TUDU Ya Samu Akan Cewa Anga Watan Shawwal Yasa Malamin Shida Mabiyan sa Sun Sha Ruwa Yau Lahadi.

Dalilin Hakane Yasa Uban Ƙasar Gada ta Jahar Sakkwato Yasa Aka Kamo Malamin Domin Gurfana Gaban Masautar Tasa Don ya Bada Dalilin sa Nayin Sallah Shida Mabiyan sa, Cikin Tambayoyin da Masautar Tayi ma Malamin ta Tambaye shi Kan Cewa Shike da Ikon Fadar Anga Wata Shawwal Ko Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ada Abubakar.

Limamin ya Amsa da Cewa “Shi Malamin da Yayi Karatu a Wajen ya Gaya Masa Matukar ya Sami Tabbacin Anga Wata to Yana Iya Ajiye Azumin sa Yayi Sallah, Tuni Dai Al’ummar da Suka Karbi Fatawar Malamin Suka Ajiye Azumi Sun Garzaya a Fadar Mai Alfarma Uban Kasar Gada Wasu Riƙe da ‘Pure Water’ da Biskit da Kayan Ciye_Ciye Suna Bukatar a Sallami Malamin Bai Aitaka Kaifin Komai ba Kamar Yadda Masautar Take Zargin sa.

Kuma Dai Tuni An Sallimi Limamin ya Koma Gida Tare da Mabiyan sa.

 

~ Alfijir Hausa

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button