Uncategorized

MATAR UBA 31

Ad

_____

 💦💦💦💦💦💦💦💦     *MATAR UBA*

💦💦💦💦💦💦💦💦

Daga Alkalamin ✍️

      

       *Milly*

                   Fadilah Yakub

                 *(MILHAAT)*

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️*

                   *M. W. A*

 *Bismillahir Rahmanir Rahim*

Ad

CHAPTER 31

Not edited

Tashi tayi ta d’auko ta tsiiyaya Masa a cup ta mika Masa da bismillah ya fara sha, Asiyah dake sama tana kallon su abun dariya ya Bata.

Sai da ya shanye ya ajiye cup d’in.

💦💦💦💦💦💦💦💦

……….. A zuciyar sa yace “Yanzu daba don Asiya ba da Shikenan nima na Zama robot sai yanda akayi dani”

“in Kara maka?”

“A a ya ishe ni, Ni Yanzu zan tafi sai munyi waya”

“okay to Muje na raka ka”

“A’a nagode ki yi zaman ki”

Yayi ficewar sa.

Yana fita a gidan ya shiga dialing number Asiyah, duka d’aya ta d’auko, a handsfree yasa wayar kasantuwar Yana driving tana picking yace “Da fatan dai kin canza drink d’in?”

“Wani drink Kenan fa?”

Tana dariya kasa kasa, ” maganar drink d’in da ake Shirin bani Mana”

“A a ban canza ba, Yanzu jira nake na faki idon ta Kan na canza”

Zaro Ido yayi had’e da taka birkii har sai da ya kusa buge wani Mai matching.

Cike da tashin hankali yace “Me kike nufi? Kina so kice min Baki canza ba?”

“Eh Amma yanzu zanje na canza”

“Amma d’azu kince min kin canza”

“A’a baka ji da kyau ba dai,zan dai canza nace maka”

“Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un”

“Ya dai Excellency,irin wannan salati haka?”

Kasa ce mata komai yayi sai sallalami yake “Dan Allah me hakane?”

“Asiyah na Sha fa wallahi na Sha , Shikenan sai yanda akayi dani”

Dariya ta shiga harda kwanciya a kasa ,kasa cewa komai yayi har sai da ta gama Tace “Hello?”

“Ina jinki dariyar me kike?”

“Dariyar ka wallahi dariya ka bani”

“Asiyah ince Miki nasha Kuma ki tssya dariya”

” Eh man ba Dole ba Ashe haka kake da tsoro?”

“Ji man hajiya maganar sihiri fa ake anan kin San fa matar Nan ja’ira ce.”

Yar karamar dariya tayi tace “ina Raye ina numfashi sai in bar a cutar min da kai? Bazaiyu ba,wasa nake maka zuwa nayi na zubar, ka kwantar da  hankalin ka”

Jingina kansa yayi a jikin gujerar ya sauke wani ajiyar zuciya yace “zakiyi kisan Kai”

“Ban gane zanyi kisan Kai ba?”

“Saura kad’an da nayi accident na buge wani”

“Wayyo Allah na Kai baka San was bane?”

“Ina zan san wasa kike bayan baki nuna min alamun hakan ba, gaskiya kin cutar dani”

“Dan Allah kayi hakuri ni banyi hakan don na tsorata ka ba”

“Ni gaskiya ban hakura ba”

“please Mana Excellency, kasan fa bana so kana fushi Dani”

“bana fushi dake but sai na rama, Dole na hukunta ki.”

“A’a ni ban yarda ba”

“Gara dai ki bari na rama if not ko Zaki yi bayani a first night”

Sai ji yayi kitt, ta katse call d’in dariya ya shiga yi ya sa wa motarsa key ya wuce gida.

Ita ko dariya ta shiga yi ta kwanta a katifan ta, tana Kara jin soyayayya da kaunar say na Kara narkuwa a zuciyar ta.

A parlor ya tarar da Momy na zaune cikin Ladabi ya gaida ta har ya Mike Tace “Son zauna ina da magana da Kai”

Sai da yaji wani rass don idan yaji Tace hakan yasan babbar maganace.

Dukkanin nitsuwar say ya tattara, gyaran murya tayi tace “Na lura a cikin kwanakin Nan ba ka cikin nitsuwar ka wai me ke faruwane?”

“Mum wallahi maganar Asiyah ce take damina”

“Toh wani abun ne Kuma ya Faru?”

“A’a haryanzu dai Wannan maganar nata da Mummyn ta ne”

“A gaskiya bana jin dadin yanda ka Zama jibi fa,yanda ka wani kwanjame   haba,in fa abun Nan bazaiyu ba ka rabu da yarinyar Nan”

A firgece ya d’ago kansa ya kalleta cikin Rawar murya yace “Dan…..d..Dan Allah Mom Kar kice haka wallahi idan na rasa Asiyah komai zai iya samina, zan iya rasa ta” riko hannayen ta yayi ya had’a da nashi ya d’aura da fad’in “Rasa Asiyah tamkar rasa Raina ne Mom” ya karasa maganar hawaye na gangarowa da ga idanun sa har kuncin sa.

Kallon mamaki take masa (tun Yana yaro rabona da ganin hawaye a idanun sa ba,a Lokacin da mahaifin sa ya rasu baiyi kuka ba duk da shakuwar dake tsakanin su sai dai ta shiga tashin hankali matuka).

Murmushi irin nasu na manya tayi ta sa hannu ta share masa hawaye had’e da fad’in “Son kuka?”

D’ago idanun sa yayi da suka Riga suka Kad’e sukayi jaa, kallon ta yayi Murmushin gefen baki yace “Hmm Mom da ace zan iya fasa Miki kirjina ki gani na tabbata Zaki ga sunan Asiya ne a rubuce a ciki”

Huci tayi mai zafi ta Tsaya kallon sa ta sun d’auki kusan dakika goma ba Wanda yace komai.

Hannu tasa ta shafa kansa tace “Son in dai kana kaunar yarinyar Nan har haka nima ina kaunarta sabida ina son abinda kake so, zan tsaya maka wurin ganin ka auri Asiyah Amma da Sharad’i”

Murya na rawa yace “iiii….innaa… Jinkiii koma..  koma mene ne Ni zanyi in dai zan Samu Asiyah”

Hannun ta ta zare acikin Nasa ta Kuma sauke hannun ta dake kansa.

Ganin tayi Shiru yace “Mummy kinyi Shiru,ina jinki”

Cike da nuna muhimmancin maganar ta gyara Zama ta d’aura kafa d’aya akan d’aya tace “Ina so kaje gidan Nana ku dai daita tsakanin ku da Yesmin,idan kayi hakan zaka auri Asiyah”

Zaro Ido yayi a razane ya Mike yace “Yesmin!!!!

Itama mikewar tayi tace “Eh Yesmin ko ban Isa da kai bane?”

Cikin Rawar murya yace “Amma….Amma mom kin fasa san akwai maganar aurena da diyya, ya Kuma Zaki ce na auri Yesmin?”

Cike da gadara tace “Eh ina sane”

Ad

_____

1 2 3Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button