MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 61

 

*Page 61*

………….Hannunsa yasa a wuyanta bayan ya sauke little ɗin yana lallashi dan kuka yake nemanyi dan an saukesa a wuyan mamansa. 

       Tsatstsare ta da idanunsa masu tarin kwarjini yayi, cikin kulawa yace, “Zazzaɓin dai har yanzun?”.

      Kanta taɗan jinjina masa batare data kallesaba. A mamakinsu sai gani sukai shima little dake jikinsa ya saka hannu a wuyanta kamar yanda AK yayi, 

yakuma kwaikwayi zancen daya faɗa. “Zazzaɓine har yanju?”.

        Kallon juna sukai suka saki murmushi lokaci guda haƙoransu na bayyana a waje. dan yanda yaron yayi maganar cikin serious dolene kai dariya. Shiko da 

yayi ko’a jikinsa, dan saima ya miƙe saman gadon ya hau tsallensa.

       AK daya samu ya danne dariyarsa da ƙyar sai murmushi ya kamo hannun Zinneerah daketa faman kare bakinta dan da gaske dariyar ke cinta itama amma dai 

taƙi yarda tayi sai murmushi. “Yaron nan wayonsa yayi yawa, minene sirrin?”.

       Ƙoƙarin shanye dariyarta tai da faɗin, “Kawai dai danya tashi cikin yarane”. 

     “Uhmyim, su Sadiq sun iya raino kenan?”.

      Ɗan kallonsa tai mamaki sosai a fuskarta, a tunaninta ina yasan su sadiq har haka. Murmushi yay mata cike da basarwa ya miƙe. Batare daya ƙara cewa 

komaiba ya fita a ɗakin, ajiyar zuciya kawai ta sauke da juyawa ta kalli little dake cigaba da tsalle-tsallensa hankali kwance. Sai kawai ta yaye bargon ta 

sauka baki ɗaya duk da kuwa dai tanajin zazzaɓin har yanzun.

    Bata sake ganin AK ba sai da akai magriba, ta idar da salla kenan tana ninke sallaya, little na gefe zaune yana raira kukan makesa da tai saboda ɓarna 

da yake neman mata a mirror ta hanashi yaƙi hanuwa AK ya shigo. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa yana maidawa ga little ɗin. Wajensa ya nufa, ya kamashi 

ya ɗaga jikinsa yana murmushi, “Wai mi akaima sojan nan ne?”.

      Zinneerah little ɗin dake cigaba da kukansa ya nuna. AK ya kalli Zinneerah ɗin shima, “Mami mi mukayi haka aka samu kuka?”.

        Ɗan kallonsu tayi tana harar little ɗin, cikin muryarta datai sanyi saboda zazzaɓin da takeji tace, “Ɓarna zaimin nace ya bari yaƙiji shiyyasa na 

make hannun”.

       Hannu yasa yana sharema little ɗin hawayen, “Handsome babu ƙyau a hana mutum abu ya ƙi bari, kaga Mami bata da lafiya ma uhmyim?. Ce mata sorry”. Yay 

maganar yana matsawa gabanta.

      “Mami Shoyi”. Little ya faɗa jin AK ɗin ya kirata Mami.

       Ɗan hararsa ta ƙarayi ta ɗauke kanta kawai. AK ya riƙo hannunta, dole ta sake ɗagowa ta dubesu. Sai dai narkakken kallon da yake mata yasata janye 

idanunta. Batare da ya damu da yanda tayinba yace, “Ai munce ayi haƙuri ko”.

    “Nima na haƙura ai, zanje na kwantane sanyi nakeji Yayanmu”.

      “A’a ba kwanciya zakiyiba, shirya asibiti zamuje”. 

    Kanta ta jinjina masa, dama jikinta doguwar riga ce da hijjab. Dan haka sai kawai taɗan ƙara turare a jikinta tabi bayansu dan shi harya fice ɗauke da 

little.

        A general falo ta iskesu, batare da yayi maganaba ya nuna mata hanya alamar suje. Gaba tai ya bita a baya ɗauke da ɗansa. Shine ya rufe ƙofar sannan 

suka ƙarasa ga mota. Ganin little kamar zai takurasa a wajen tuƙin yasata miƙa masa hannu alamar yazo wajenta, amma sai ya noke.

     Baki ta taɓe da hararsa ta ɗauke kanta. Sai da ya tada motar suka fice a gidan yay magana batare daya kalletaba. “Nikam wannan harar ɗan akemawa ko 

baban? Tunda shima mai laifine?”.

       Gefe tai da kanta tana murmushi da faɗin, “Kai Yayanmu ni dai wlhy banceba”.

    Shima murmushin yayi da sumbatar kan little dake cinyarsa suna tuƙin tare. Daga haka ya maida hankalinsa a tuƙinsa itako ta lafe cikin kujera ta lumshe 

idanu.

      Sun isa Shira hospital inda suka samu ƙyaƙyƙyawar tarba ga ma’aikatan. Anata kallonsu cike da sha’awa da birgewa. Yayinda suke nuna son ɗaukar little 

amma sai yaƙi yana dai maƙale da babansa. A office ɗin Dr Mahmud suka yada zango, shima ya tarbesu cike da murna da girmamawa yanata tsokanar Zinneerah. 

Yayinda ya ɗauka little kuma da ƙyar.

           “Ranka ya daɗe kune da dare haka? Lafiya dai ko?”. 

      “To da sauƙi dai madam ce babu lafiya”. AK ya faɗa yana duban Zinneerah da kanta ke ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

       “ALLAH ya ƙara lafiya, Ko gajiyar biki ce ƙanwarmu?”.

     Murmushi kawai tai batace komaiba. Shima sai ya murmusa da mikama AK little. Kafin ya maida hankali wajen mata tambayoyi. Magunguna kawai ya rubuta 

musu yay kiran wata Nurse a waya ya bata ta sayo. Ganin an kira isha’i suka fita salla suka barta a office ɗin. Suna dawowa ko zama basuyiba AK yace ta 

tashi suwuce kar dare yayi.

        Har wajen motarsu Dr Mahmud yayo musu rakiya, sai da yaga tafiyarsu sannan ya koma ciki. 

Daga asibiti AK wani shagon sai da wayoyi ya kaisu, a mota ya barta suka shiga ciki shi da little. Babu jimawa kuwa sai gasu sun dawo ɗauke da leda. Daga 

haka gida suka nufa bayan ya sake tsayawa ya sai musu gasashshen kifi.

          Sosai Zinneerah kejin barci lokacin da suka shigo gidan, fahimtar hakan da AK yayi ya sakashi dakatar da ita a falon farko na sashenta. Tsareta 

yay sukai zaman cin kifin tare, bama wani sosai taciba dan bakinta babu daɗi. Ya bata magungunanta ta sha taɗan tattare wajen ta shige. Shima sashensa ya 

nufa da little. Acan yay masa wanka, sai dai babu kayansa kuma balle na barci. Shaf yama manta da batun amso masa kaya. Pant dinsa kawai ya maida masa ya 

kwantar dashi a gadonsa dan sai hamma yake. Shima shirin barcin yayi sannan ya nufi sashen zinneerah. Isketa da yay har tayi barci ya sashi fitowa ya dawo 

sashensa. little ya ɗauka yaje can shima kawai suka saka yaronsu tsakkiya.

    Zinneerah batasan da zamansu a ɗakin ba sai da asuba data farka, dan ta rigashi tashi. Ta jima tana kallonsa shi da little zuciyarta fal saƙe-saƙe iri-

iri. daga ƙarshe dai ta mike ta shiga toilet. AK da shima ya jima da farkawa ya bata damar cigaba da kallon nasune tana shigewa ya miƙe. A bakin gadon ya 

zauna harta fito sanann. Ɗan kallonta yayi yana lumshe ido, muryarsa a dasashe irin ta wanda ya tashi barci yace, “Naje massallaci”.

        Tace, “A dawo lafiya”.

__________________

       AK bai dawo gidan ba sai da rana tai ɗan haske. Ya shigo ya iske Zinneerah nata aikin kimtsa gidan kamar ba itace mara lafiyaba. Har ƙasa takai ta 

gaidashi. Ya amsa mata da kulawa yana tambayarta yaya jikinta. “Alhmdllh naji sauƙi ai”. Ta faɗa a hankali.

      “Masha ALLAH”. Shima ya amsa mata kafin yace, “Ina little?”. “Bai tashiba har yanzun”. “Okay bara to na watsa ruwa dan inason fita da wuri”.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button