AHUMAGGAH 12

_*♡AHUMAGGAH????*_
_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_
_Bismillahirrahmanirrahim_
_1⃣2⃣-path♡_
Bangaren subaya kam murnan jin khaldun ya amince dani a matsayin yar uwansa ya sa ta kasa hakuri Site din jahan taje ta shiga bata labarin abunda yace.
Jahan murmushi kawai take tayi aranta tana jinjina murdadden hali irin na danta tasan
Bazai taba yin abu direct ba Wani bin har tausayin macen da zai auro ya zauna da ita take.
Cikin hirar su da subaya sai ga kiran alhaj hamood.
Anan subayan ta kejin ashe cewa da khaldun yayi zai tafi ya bar ta ba wasa yake yi ba dagaske ne.
Khaldun sa’ood zai tafi chan iran dawlan kakkanin sa watoh iyayen mahaifin sa..
Bayan ya dade baije bama gashi yanzu wani muhimmin Aiki ya hada shi da sojojin india rajiskhan iran da duk wani karamar yankin data shiga tsakanin wayannan kasashe
Dan haka zaibar gida nigeria na kusan shekara 4.
A Take jikin subaya ya mutu sai taji wani iri aranta
Sai dai kuma inda sabo ta saba dan haka koda akayi confirming maganan tafiyar sa awajen jahan sai ta daure bata ce komai ba.
Ni kuwa ina chan daki ina kan dresing kaina,dan da shike yau banyi wanka da safe ba sai naga zaifi dacewa nayi wankan kafin naje ansa kirar jahan.
Puss pink ember gown dan dai dai da jiki na na saka,sai na goga light pink oily chapet a lips dina,ban wani shafa turare dayawa ba dan haka mutum bazai ji qamshin da jiki na take yi sai yana daf da ni..
Wajen jahan na nufa dan haka Tafiya ta nake yi shiru akan tsari Ban lura da wanda yake biyo ni abaya na ba
Shikuwa khaldun tun daga saukowar sa a akan step din shigowa shashen ya zuko qamshin jikina sai ya dago idanub sa ya sauke akaina yana ta kallo na
He loves keeping straight face,dan haka babu alaman daya nuna cewa qamshin jikin nawa ne ya burge shi,toh whats he looking at dan ko ni ban isa nace na sani ba.
Da shike waje daya muka dosa sai Motsin takun sa a daf dani ya fargar dani.
Gefe na koma na rabe alaman na bashi hanya,.
Banyi tsammanin zai kalle ni ba sai gashi har mun hade ido.
Dauke kansa yayi
da sauri ya dan shige gaba nikuwa tsaban bugun da zuciya keyi sai da na kusan minti 10 ina tsaye ina ta tuno da wulgawar kyakwan fuskan sa
sanda har ya kure bana ganin sa ban lura ba sai chan kafin na tattaro kaina na biyo bayan sa.
Da sallama na dan yaye curtain din da zimman ganin sa shida jahan sai wayam naga ba kowa acikin hall din.
Dada shigowa nayi ina dube dube amma shiru banji motsin kowa ba,dada kutso kai nake yi ina bin palourrs din ta dakii daki gashi wajen ba kadan ba
Ganin shiru yayi yawa sai na juyo da zimman zab fice,wani sanyin iska ne mai dan karfi ya buso ni dana ke takowa ta hall way yana faman daga transparent curtains to a chan bayan site din na hango big sis subaya tana xaune tana ta dariya alaman anan suke
Dan kadan na dafa glass wall din na yaye curtain din ina kallon murmishin ta
Haka kawai naji wani irin dadi acikin raina danaga tana cikin wannan yanayi
I just love seeing her happy,sai dai bansan meyasa na tsani mijin ta har cikin zuciya ta ba.
Hankalina ya fara bani cewa baya kaunar khaldun and he is not so caring with big sis.
A tunani na yanzun ma ba bazai wuce da shi take tare ba,hmm big sis is realy in love with him,and its so unfurtunate that sadat shine farin cikin ta..amma da za’a bi ra’ayi na i feel like he dosnt even derseve her.
Ajiyan zuciya na sauke zan sake labule naji kaina ya wani sara,bugun kirji na ya karu.
Wani daddan Qamshin jikin khaldun mai rudarwa na shaka
Ban wani jira ba na waigo a fixge har ban sani bana fado jikin shi
da kyar na dan daddafe na chakumo rigar sa
Ido na a lumshe nayi shiru ina jin tafiyar hannun sa a baya na daya sa ya tallafo ni
Ban iya hade ido da shi ba cikin marairacewar murya nace
Sorry.. Yace baki da aikin yi ko?sai Ya sake ni a hankali ya na kallo na
Sai Na girgiza masa kai ina dan matsawa gefe، tabe baki yayi ya wuce daf jikina kamar zai gogu dani dan na kara matsawa,
hannu yasa ya yaye curtain din shima ya shiga kare ma big sis kallo
Go get me something to eat
“Derset
Nace ok…k
Da sauri nayi yunkuri Zan wuce yace i want that thing !
Ban fahimce that thing din ba sai
Na juyo a slow motion,ina kallon shi har yanxu idanun sa nakan kallon waje.
Ban dai ce komai ba Na tsaya ina mutsu mutsu kamar munafuka
Har zan yanki draw na tafi sai naji yace
Wancan abun da kike dafawa shahrul yam balls…shikadai ma its ok
Hehehe yau kuma? amma ai da shahrul ya yabeni akan yamballs din cewa yayi bai masa dadi
Ba
Ko gama assimilating voice dinshi banyi ba yayi dismising dina da cewa
“Be fast about it,
Kawai sai na nufi kitchen ina ta famar murmushi
Doya na feraye na tafasa kafin na shiga hade haden da nasaba domin yin hadaddiyar yam balls mai flaked fish..
Da shike ina ta tunani kala kala,sai na dan bata lokaci ban gama hada shi a tray ba saiga mai aikin gidan ta shigo,tace min khaldun yace chan baya zan same shi
Nace toh dana kimtsa sai na biyo ta bayan da tray din a hannu,anan din ma a cikin wani garden suke ga khaldun tare da subaya,sai umbrella swing a chan yana motsawa shikadan sa wanda ya tabbatar min cewa dama su uku da jahan Aarah suke xaune Anan
sai dai banganta ba har sai da na iso daff na hango ta achan nesa tana ta waya dukan su basu lura da ni ba..
Tsayawa nayi nadan rabe jikin wire wall dib ina satan kallon wasan da khaldun yake ma sister sa subayah
Neva in my life have i eva seen him this free,tunda nake dashi sai yau na taba ganin geniune murmushin sa
Subaya Sanye take da english wears rainbow top da rim jeans ta daura cute hair band akan suman kan ta sai tayi fresh sosai kamar wata yar shekara sha bakwai.
akan farar doki yar madaidaiciya ya daura ta shi yana jan siddin daga kasa ita kuma tana masa hira yana mata murmushi
Sai Dada matse ido na nake ina so naga ko murmushin nasa zaifi haka dan motsawar dimples dinsa ne dama alamar,but he still remain geek,i just wonder if har na mutu zanga wani kakrawan dariya akan fuskan sa.
Thy both look happy nima sai naji dadin hakan,ashe bansan da cewa yawanci dama idan zai tafi haka sukeyi sukan ware lokaci makansu na junan su ba .
Duk dama ni ba jinin su bane amma sosai Naji dadi da banga sadaat anan din ba
Ko da ba’ace ba
Nikaina nasan bana son abunda khaldun baya so Am naturally getting attched to his emotions
Ganin jahan ta sauke waya a kunnen ta yasa nayi maza na fito daga bayan wall din na karaso
Ya Nooori…
Subaya ta kwalla min kira muryan ra shake da dariya da farin ciki
I cant help but to smile back,ina aje
Tray din yamballs din san sai nayi waving inta at same time ina karasawa zuwa wajen jahan.
Har kasa nakai zan rusuna ta ruko ni calmy da irin kallon ta mai kafa tasiri azuciyan mutum.
Sanda ta dago kaina ta dora min light peg a goshi kafin tayi min adduan tsawon rai.
‘Shikuwa khaldun sau daya ya kalle ni ya kau da kansa amma bai wani hade rai ba.
Jahan ce ta fara bude abincin dana kawo masa A ranta tana wondering ba dazo da safe subaya tace mata khaldun ya amince da ni ba?