NIDA AMARYATA 11-12

1⃣1⃣_1⃣2⃣..
Sam Bata samu fitowa ba sai wajen magriba ma sannan ta tashi daga ciye-ciyen da taita dibgawa kanta,danko abincin Rana Bata naima ba,ita ma kuwa Hajiya Bata nemeta ba Dan taci.Tana Nan zaune zuwa can ta mike ta shiga Tayo wankanta,kamar yadda Aunty Hama tace ta ringa yi,aikuwa bayan
ta fito ta dade tana wasanta ma kafin ta nufi gaban dressing mirror ta zauna,Mai ta shafa,taso yin kwalliya saita tuna Aunty Hama tace Mata intayi wanka ta rinka shafa Mai da powder kadan,tasa lipstick shikenan,aikuwa hakan tayi,bayan ta Gama ta mike ta nufi wardrobe dinta.Budewa ta shigayi duka harta bude bangaren da taga an jera undies din maza sababbi.zarosu ta shigayi tana dariya,inda ta zaro wani gajeren wandon Alhajin maroon da ratsin fari,batare da tunanin komai ba ko ta shiga kiciniyar sawa,iya gwiwar ta ya tsaya mata.sai Kuma ta tsaya neman rigar da zata had a,ganin yadda a cewarta wandon yayi Mata yawa,tasan maje gaba Aunty Hama tasai mata.Singilet ta zaro itama ta shiga sawa,wadda itanma ta tsaya Mata iya gwiwar Amma Bata karasa tsawon wandon ba.
Ta jima tana kallon kanta a madubi tana yaba kanta da kanta,kallon kanta tayi kawai saita yanke shawarar sa hula,Dan tun da can Aunty Hama ta hanata Zama ba dankwali tace sbd tankawar da akewa gashinta.hularta tasa aikuwa tahau juye-juye ta dama da haggu Dan ganin tayi ko batayi ba.tsalle ta buga tare da fadin yissss nayi kyau…
***
Shikuwa Alhaji bayan ya Gama cin abinci,Hajiya tabishi da kallo tana son yi Masa magana tana Kuma Jin shakka,domin duk abinda takeyi akan Alhaji dai ba nasara,Dan haka ta Dan daure tace,
“Dama Alhaji akan batun Kara aurenka ne,yanzu Alhaji kana ganin kayimin adalci kenan? Ko Kuma kayiwa yaranka ko Kuma Kai kanka! Ka rasa wadda zaka auro sai ‘yar cikinka,yanzu duba shirmen data tabka gaban ‘ya’yanka,bakaji kunya ba,har yaushe zakasan Annabi ya faku! Gaskiya abinda kayi Sam Bai Dace ba” ta karasa maganar tana huci.
Saida ya tabbatar ta Gama ya mike,ya Isa gaban mirror Yana cire kayansa da alama wanka zaiyi,harta cire rai zaiyi Mata magana sai Kuma taji muryarsa Yana fadin.
“Ai saiki fadamin hadisi ko ayar da tayi Hani daka auri mace Dan kawai ka girmeta ko ka Isa haihuwar ta,Kinga bana son shashanci,ki kiyayeni ka Kama girmanki da bakinki kamar yadda Kika Saba a baya”,Yana karasa fadar hakan ya shige toilet ya barta Nan zaune cike da kunar zuciya,Bata wani jira fitowarsa ba tasa Kai ta fice.
Shikuwa ransa ne ya baci da maganganun Hajiyar,Yana wanka yana tsaki,har ya Kare ya fito,Yana goge jikinsa ya tuna Daya kashe wayoyinsa,Dan haka ya jawo su ya kunna,kamar ko jira ake ya kunna Kiran Alhaji kabeer ya shigo.yana dagawa ya shiga yi Masa kirarin ango kasha kamshi.
Amsawa yayi kamar yadda suka Saba nan suka taba Hira kamar yadda suka saba,kafin suke sanar dashi suna Nan tafe anjima suga amarya,tunda ya hanasu rakoshi jiya,Yana shirin Basu amsa yaji wayar dibbb,sake Kiran wayar yayi yajita a kashe,a fili ya furta ya Allah! Taya Zan hanasu ganawa da wannan mahaukaciyar Amaryar!”
Ya jima Yana tunani kafin daga can ya samu mafita ,guri ya samu ya Kara zama,inda shiga kallon bakinsa ganin yadda ya sabe sosai.
Sai da yaji an Kira sallar magriba ya mike ya fice Dan zuwa masallaci,a falo yasami yaransa a falon suna kallo,gaba dayansu umartar su yayi da su tashi suje suyi sallah Nan yasa kansa ya fice.
Sam Bai dawo ba,saida akayi sallar isha’i,Yana kokarin shigowa Dan ya sanar da me gadi duk Wanda yazo yace ya fita,Yana dab da shiga yaji ana Danno Masa horn,aikuwa ya waiga Dan ganin su Alhaji kabeer,yake kawai yayi musu,Amma harga Allah badan yayi murnar ganinsu ba,Dan ya so dakile wannan zuwan nasu,Amma sun shammace shi,Dan haka ya karasa Yana murmushin Nuna Jin dadin ganinsu.
Tsiya suka shiga yi Masa yayin da yayiwa me gadi umarnin ya bude su shiga daga ciki.
Suna karasawa Nan yayi musu jagora zuwa falon gidan,Dan sunce suna son su gaisa da Hajiya.
Bayan sun zauna ne,Alhaji Kabir ya kalleshi tare da fadin,”ya Naga bakin ango kamar ya kumbura,fatan dai ba amaryar ce tayi aika-aika ba?”
Cikin son basar da maganar ya juya ya nufi bangaren Hajiya Hafsa danya Kira musu ita su gaisa.
Yana shiga ya isketa tana waya,ganin shigowar shi yasa ta katse tare da maida hankalinta ga Mai gidan Dan Jin abinda yake cewa,bayan ya fada Mata tazo zasu gaisa da Baki ta amsa da “to” tace gatanan zuwa.
Falon ya dawo ya zauna,Nan suka ci gaba da tsokanarshi akan amarya.
Suna Nan zaune Hajiya Hafsa ta shigo Falon dauke da sallama a bakinta,inda tana shigowa suka shiga yimata kirari da uwar gida sarautar mata,amsa musu tayi da “ai kune masu sarauta,tunda kuke da damar Kara aure”.
“Ah ah aike kowacce tazo saidai tabi bayanki,Dan haka ki Kara mike kafa,zamanki daram gidan Alhaji Sani.
Bata tanka musu ba,ta mike tace “NI kada ku cikani da surutunku da bazai Kare ba,Bari in kawo muku abin motsa baki,”,
Kitchen ta nufa Dan kawo musu abin sarrafawa cikinsu.
Tana barin gurin Alhaji Adam ya kalli Alhaji sani,tare da fadin,” Kai mu fa munki wayon,a fito Mana da amarya mu gaisa,kawai katashi ka hadamu da tsohuwar fuskar da muka Saba gani,kawai ka kirawo Mana balarabiyar amarya mu Kara ganinta.
Hmmm”ai yanzu zancen da nake muku amarya nacan tana zazzabi,Dan haka bazata samu damar sakkowa ba,sai dai KU Bari kwa dawo wata Rana ko Kuma inta haihu”.
Shigowar Hajiya Hafsa ya katse musu maganar,Nan aka sake dasa wata hirar.
****
Itako Nihila tana can dakinta tana ta adungure akan gado,ganin ta gaji yasata mikewa Dan ta leka inba kowa a falon kasa ta more da yin sililiu a kafar bene, tana mikewa Saida ta Kara kallon kanta a madubi taga yadda kayan suka zauna Mata a jiki duk da a cewarta tasan maje gaba ne.
Directly ta nufo Falon kasa Dan jin hayaniya da dariyar da taketa jiyowa,Dan haka tace Bari taje ta gani Dan itama ayi da ita.
Dayake Alhaji ne ke facing din inda step din benen yake,kamar da wasa ya maida hankalinshi ga kallon gurin,aikuwa idonsa ya sauka kan wani yaro na tahowa sanye da gajeren wando da singilet na manya,Wanda sai yawo yakeyi a cikinsu,Yana gab da son tantance Ina suka Sami bakon namiji,aikuwa idonsa ya tantance Masa Nihila tana kokarin nufo su…
Da mugun sauri ya mike Wanda shi kanshi baisan yanada wannan kuzarin ba,Saida ya ganshi a gabanta dai dai karasowar sakkowarta,surarta yayi a sukwane ya Fara haurawa da ita saman benen,yayin da sai a lokacin hankalin mutanen Falon yakai gareshi,domin sunga ya tashi ya zura da gudu,Basu San meya faru ba,amma sun hangoshi kamar rungume da mutum,Wanda hakan yasa sukayi tunanin ko amaryar tasa ce tayi yunkurin sakkowa Dan su gaisa,ko jiri ya debeta shine ya diba a miliyan dan taimakonta.Dukansu wannan tunanin sukayi,sabanin Hajiya da Bata fahimci meke faruwa ba.
Yana haurawa da ita Bai direta a ko Ina ba sai a dakinta,duk da wutsil-wutsil din da takeyi na ya sauketa kuwa.
Yana Direta cike da bacin Rai ya daga hannu da niyyar sharara Mata Mari, sakamakon kallon kayan dake jikinta Kuma take Shirin fita a hakan,har ya kusa kaiwa fuskarta,Saiya tuna da karon battar dazu da safe.wanda baiji ba Bai gani ba Saida yayi ta miliyan daya,Dan haka ya sauke hannunsa tare da sauke huci kamar want tsohon zaki!
“Are mad? Da Zaki tashi ki fita a haka?
Murguda Baki tayi tare da fadin,”wallahi mu ba ‘yan maiduguri bane ehe!
Wani bakin ciki ne ya Kara tunkarar zuciyar sa Dan haka cikin wani takaicin yakuma cewa,
“What is your prolem? Anything I say u want try to change my mind!”
Cikin daga murya tace,”you stupid shortcut tsamiyar biri,me na big big everything, Wallahi I fadawa Anty Hama by gobe idan tazo,and say you are zaginta, that is All of u.
Sandarewa yayi,sakamakon Jin makahon turancin da tunda yazo duniya Bai taba Jin malamin Daya koyar ba.jin a batun nata tace zata fadawa Aunty Hama in tazo,yasa shi saurin karaswa gabanta cikin kwantar da murya yace,
“Haba baby! Me yayi zafi da Zaki fadawa Aunty,ai ba komai Zaki dinga fada ba kinji ko? Duk abinda yafaru tsakaninmu ki dinga barinshi a sirri kinji ko!
“Naki naji din,wayasa kacemin baby,sai kace wata baby’n roba ta karasa maganar tana zirarar hawaye.
“Ikon Allah ya furta! Yau Kuma abinda ya jawo wa kansa kenan! Wannan aure ko kaddara,gashi a wannan auren ya kashe kudin da shi kanshi baisan adadin su ba,gashi ba biyan bukata.shi Bai mori amarci ba bare aje batun Fara kara’i.
Matsowa ya kuma yi tare da kama hannunta zuwa gefen gadon,cikin sigar rarrashi ya Fara fadin,”waye yace miki.kisa wannan kayan?
“Ba Aunty Hama bace tacemin wankan dare na kananan Kaya ne Amma ba mattsatsu ba,shine nasa maje gaba Dan in burgeka.
Kura Mata ido yayi,sai yaji wani Abu ya tsarga Masa,shi sai yau ma ya gara tantance tsantsar kyau da haliltta irin nata,sai dai daka kura Mata ido Inka nutsu zaka hango zallar kuruciyar dake tattare da ita Dan haka ya Kara gyara Zama tare da cewa,
“Ke Baki san wannan kayan na waye ba?
“Ai a cikin sif Dina na gansu,nasan Kuma nawa ne”
Girgiza Kai yayi,tare da fadin to kayan maza ne,Baki ganin Abbanki ko yayanki nasawa?
“Ai ni banida Yaya Kuma banida baba,Dan Aunty Hama tacemin duk sun mutu,Kuma ni bana ganin wani namiji yana shigowa gidanmu,Kuma ni fa ba fita nakeyi ba”
Tirkashi ya furta a fili.
*Shin Wai wacece NIHILA?*
*Kada ku Manta wannan littafin na siyarwa ne gamai bukatarsa zai aika da naira dari biyu kacal…ta wannan account number,0448266382, Hadiza Usman muhammad, GTbank.ko Kuma katin waya na MTN na naira dari biyu ta wannan number,07033558928.
*Alkalamin khady* ✍