BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 71

71*

……….Gigitacciyar tsawa Daddy ya daka musu. “Wlhy duk wadda ta sake cewa tak sai ranta yay mummunan ɓaci, idan kuma kunji ƙarya bismillah marasa mutunci kawai. Ku har kun isa ku maidamu mutanen banza. Ku tashi kufita bama buƙatar zaman kowacce a anan”.
       Cikin ɓacin rai suka mike su biyun suka fice. Daddy ya cigaba da faɗa tamkar zai ari baki, da ƙyar dai su Abie ɗin suma suka taushesa. Haɗuwa sukai akan Fadwa da Shareff ɗin duka sukai musu tatas da faɗa musamman Fadwa a matsayinta na mace. Sai kuma suka koma nasiha a garesu. Daga nan suna jiyo hayaniyar Mommy da Gwaggo Halima, hakan yasa Gwaggo da har yanzu bata tofa nata ba ta miƙe ta fita wai zata tsawata musu. Nasiha Abie ya sake musu ta fahimta data saka zukatansu samun nutsuwa, musamman ma Fadwa da taga an nunama Shareff kuskuren marinta da yayi kuma ya nuna nadamar yin hakan da alƙawarin bazai sake ba. Duk da dai itama tasha nata, sun kuma nuna mata illar biyema su aunty Malika cikin hikima. Basu san babu abinda ke cizon zuciyar Shareff ba kamar maganar su aunty Safara’h ɗin nan. Sai dai baice komai ba dan a samu zaman lafiya, amma yay aniyar da kansa zaima tufƙar hanci insha ALLAHU.
     
        Da ƙyar wajen ƙarfe goma suka baro gidan, dan kuwa rikici ne na gaske ya ɓarke tsakanin Gwaggo Halima da Mommy har sai da Baban Fadwa ya kira waya dan baya ƙasar ne shiyyasa harta samu damar fitowa. Ya kuma janye mata wancan sharaɗin lokacin da zaiyi tafiyar saboda haƙuri data bashi akan komai ya wuce. Ashe akwai wani a gaba. Mommy dai taci alwashin sai ta nunama Gwaggo Halima itace ta haifi Shareff ba wani shege ya haifa mata ba. Haka itama Gwaggo Halima ta tabbatar mata cewa ita bata isa komai ba domin Shareff ɗin ba nata bane ita kaɗai..
     Kuka Fadwa ke masa tunda suka taho, dan kuwa rikicin Mommy da Mamanta ya matuƙar ɗaga mata hankali kuma, tana matuƙar tsoron abinda zai rabata da Shareff, tana masa so ne mai tsanani, wanda takejin in har aka rabasu zata iya rasa har ranta. Ya gaji dajin kukan, saboda shima zuciyarsa a wuya take kuma yanajin ƙuna da raɗaɗin abubuwa masu yawa. Sai dai shi jarumin mutum ne mai maida komai ba komai ba koda kuwa a ce ya zame masa komai. Dan haka har suka iso gida bai ce mata komai ba. Shine ma ya fara fita ya barta a motar, saida ta kai kusan minti huɗu a ciki tana cigaba da kukanta sannan ta fito ta rufe motar. Sashensa ta bisa kai tsaye, yana a falo zaune cikin yanayi na wanda baka iya ganemawa. Cikin jan ƙafa ta ƙarasa gabansa, ta tsugunna tare da dafa guyawunsa.
      “Ina tsugunne ne gabanka a matsayin ƙanwa Yaya Shareff, nasan ni mai laifukace a gareka tari-tari, na kuma yarda nayi kuskuren da kake son na fahimta tun kafin akai ga wannan gaɓar. Wlhy bana son zumincin iyayenmu ya lalace saboda aurenmu……”
    “Garama ya lalace, dan ta hakane kawai dake da su zaku dawo rayuwar hankali irin ta mutane. Ke kam rayuwarki naban mamaki matuƙa, mamaki irin wanda nake shiga kokwanto. Ba haka nai miki zatoba sam-sam a rayuwata ba, amma bazance ki dainaba kiyi tayi, shawara ɗaya zan baki kuma ta ƙarshe. Ya rage naki ki dawo akan ƙyaƙyƙyawar hanya ɗaya tak ki gyara halayenki muyi zaman aure na gaskiya, idan ba hakaba wlhy wlhy zan ɗauki mataki ne na ƙarshe dan bazaki maidani mahaukaci ba. Shawara ta rage gareki, ki cigaba da biyema duk wani mai zuwa gidan nan yana ɗauraki a hanyoyin da shi yake ado da su, koki zama mace tagari ki gina taki rayuwar a karan kanki. Idan kuma kika sake amfani da wani abu na kauce hanya domin mallakata, ko bani wani abu a cikin ruwan sha ko abinci ALLAH ya isa ban yafe ba!”. Ya ture hanunta tare da miƙewa ya shige bedroom abinsa.
     Hawayen da take son su zuba ma sam sunƙi zubar a yanzu, sai dai tasan gaskiya ya faɗa mata, dan kuwa a yanzu tana rayuwa ne da rayuwar su aunty Safarah, a baya komi za’a bata ta zubama Shareff a abinci bata taɓa yin hakan tunma tana gida, duk ma yanda zatai ƙoƙarin hanawa sai tayi, sai dai in Mama ta aikata bada saninta ba. Amma a wannan gaɓar ta rikice, idonta ya rufe saboda kishiya da kanta take aikata komai dan taga haske. Sai dai saɓanin hakan duhu take gani, sannan mai makon mallakarsa suɓuce mata yakeyi, kenan su magungunan na ƙarya sunfi yawa a cikinsu kenan? Ƙalilanne ake dacewa suyi aikin kuma basa wani jimawa sai kaga abubuwa sun ƙwaɓe. ‘Ya ALLAH’ ta faɗa tana mai fashewa da kukan zahiri.

    _

       Harta fara jin barci a jiya bai dawo ba, dan ita bata san tare da Fadwa ya fita ba. Koda ta shirya ɗakin da Aysha ke kwana taje ta kwanta abinta. Ayshan batace da ita komai ba dan tasan yau Shareff ya koma wajen Fadwa. Ta ɗanyi murmushi ganin Anaam ɗin sukuku, ko bata fito ta faɗa ba tasan kewar Yayansu ke nuƙurƙusarta. Sai dai sanin itama Anaam nada halin I don’t care wasu lokutan yasa babu wannan alamar akan fuskarta sam. Sai dai kuma koda suka kwanta ta jima batai barci tanata juye-juye. Sai da Ayshan ta ɗauke hankalinta da wasu labarai  sannan ɓarawon yay mata kamun kazar kuku. Ajiyar zuciya Aysha ta saki mai ƙarfi da kai hannu ta riƙo na Anaam ɗin. Tausayinta da ƙaunar ƴar uwarta na ratsa mata zuciya matuƙa….

       ★Kamar yanda ya saba da asuba sai da yazo ya tada su, Anaam ƙin yarda tai ta kalla inda yake taima shigewarta toilet. Juyawa yay ya fita shima yana mai sakin guntun murmushi. Itama Fadwa sai da yaje ya tadasu sannan ya wuce massallaci. Daya dawo bai shiga sashen kowacce ba ya koma nasa sashen ya kwanta dan jiya ya jima bai barci ba yanata faman ƙullawa da kwancewa akan yanda zai ɓulloma matan nasa. Barci yasha sosai dan sai kusan goma da wasu mintuna ya iya tashi, baiyi mamakin ganin an gyara ko’ina ba ga ƙamshi na tashi, sai dai yaji sassauci a ransa dan Fadwa ta nuna masa ta yarda ta gyara abinda take shirin ɓararwa a idanunsa. Wanka ya farayi ya shirya tare da baje jikinsa da ƙamshin turarurrukansa masu ƙamshin daɗi. Koda ya fito a falo ya sami Fadwa zaune cikin kwalliya mai ɗaukar hankali. Tabbas ta ɗauka hankalin nasa da gaske, sai dai ya basar abinsa. Gaisheshi tayi, ya amsa a daƙile, bata gazaba wajen sake jero masa kalaman ban haƙuri da tabbatar masa zata canja fiye da yanda yake buƙata. Har cikin rai ya ɗanjin tausayinta, dan yasan ya mata hukunci dai-dai da laifinta da har idan ita ba ibilisiya bace ya kamata yaga canjin. Huci ya ɗan furzar tare da ware mata hannayensa. Ai da gudu tazo ta shige jikinsa. Ya saki ƙaramin murmushi tare da sauke hannayensa akan bayanta ya fara shafawa alamar lallashi. Hawayene suka dinga silalo mata, ita kanta ta ƙara shaidawa Soulmate ɗinta zuma ne, ga zaƙi ga harbi. Ya ɗagota yana kallon fuskarta har yanzu dai babu fara’ar da take muradin gani a garesa.
“Kin san bana son kukan nan ko?”.
Kanta ta jinjina masa tana sharewa, ya raɓata ya wuce yana faɗin, “Ina zuwa bara na duba waɗan can ya suka kwana”. Kanta ta jinjina masa, ta bisa da kallo tana ƙara tsane hawayenta dake sakkowa. Ta san bawai ya gama hucewar bane, amma ko yanzu ta samu sassauci. Zakuma tabi duk hanyar data dace domin ganin ya huce baki ɗaya sun koma rayuwar farin cikinsu….

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button