Za Mu Kawar Da Yunwa Tsakanin Dalibai A Bana – Ministar Jin Kai
Ministar tallafi da jin dadin jama’a, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana hakan a jawabin da hadimarta, Halima Oyelade, ta fitar ranar Laraba a Abuja.
Hajiya Sadiya ta ce wannan sabon hadin kai da shirin abincin duniya WFP na majalisar dinkin duniya zai taimaka wajen magance matsalar yunwa cikin yara.
“WFP na bada goyon baya ta hanyar bada gudunmuwar na’urorin zamani. Wannan ya hada da Tablet dake dauke da kayan abinci iri-iri – da zai taimakawa jami’an kiwon lafiya wajen zaben irin abincin ya kamata a rika girkawa.”
“Ta hanyar wannan, za’a iya magance yunwa, talauci, rashin aikin yi da sauransu” “Wannan wani abu ne da Gwamnatin tarayya ke zuba kudi saboda muhimmancinshi.”
Ministar ta kara da cewa a shekarar 2021, an ciyar da daliban makaranta sama milyan tara a makarantun gwamnati 53,000. Tace wannan ya kara adadin dalibai dake zuwa makaranta a fadin tarayya.
Daga Muryaryanci.com
[ad_2]