Zaben 2019, Nina Lashe Zabe Amma Aka Min Murdiya, Cewar Atiku Abubakar


Ya yi zargin cewa jam’iyyar APC ta hana shi nasarar da al’ummar ƙasa su ka kaɗa masa kuri’a a 2019, amma sai jam’iyar tayi amfani da ƙarfin mulki ta yi masa fashi.
“Babu wani yanayi da za a bari hakan ya sake faruwa a zaben 2023 idan jam’iyyar PDP ta ba ni damar tsaya wa takara,” in ji shi.
Wazirin Adamawa yana magana ne da wakilan PDP na Kaduna a sakatariyar jam’iyyar a daren jiya Talata.
“Ku sake ba ni kuri’un ku kamar yadda kuka yi a 2018, ina tabbatar muku cewa ba zan ba ku kunya ba,” in ji shi.
“Idan jam’iyya ta sake bani dama na kuma zama shugaban kasa a 2023, zan zuba jari a fannin ilimi, in magance matsalar rashin tsaro, da samar da ayyukan yi ga matasa. Zan haɗa kan ƴan ƙasa yadda ko wanne ɓangare zai ji cewa a na yi da shi
“Na zo nan ne domin na sake neman ƙuri’un ku kamar yadda ku ka ba ni a 2018. Na lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2019 ta ko ina amma an yi mini fashi, kamar yadda a ka yi muku fashi a jihar Kaduna ta hanyar amfani da karfin gwamnati. Amma ba za mu bari haka ya sake faruwa ba a 2023.
[ad_2]