HAUSA NOVELZYNAH Hausa Novel

ZYNAH Hausa Novel

Ihu bakura yasa, a guje ya fito daga gidan, a wannan lokacin har ya mance wani dokar da hjy tasa masa, ko takalmi babu a kafarsa yaje ya shiga mota, a shiyace ya fisgi motar zuwa gida”.

Allah maji kan bayinsa, da kuma tausayi,wanda duk halin da zaka shiga idan har ka digara dashi, bi’izinillahi zai fiddakai, wani iko ta Allah, Allah mai hikima, ya kawowa zynah dabaran yi nishi, tana kwance ba tare data tashi ba, wani irin nishi tayi, haďe da ihuuuuuu mai karfi, take baby da mahaifar suka fito gaba daya, wani iri naunauyar ijiyar zuciya tayi, anan ta leme ko motsi batayi”.

Baby kuwa, tunda tayi kuka sau biyu bata sake yi ba, duk halin da zynah ke ciki Am’abuwa tana kallonsu ra windom, hawaye ne kawai suke gangaro mata, sabida gashi daga zynah har baby suna niman taimako amma babu halin taimaka masu”.

Tana cikin hali kenan, saiga bakura ya iso, ko parking da’kyau beyi ba, a fito daga motar, a guje yaje ya buďe gidan, kai tsaye bedroom ya nufa, yana shiga ne, Am’abuwa ta hangosa da glass, da sauri itama ta zago”.

Bakura yana shiga gani halin da zynah ke ciki, ihu kawai yasa yana faďin na shiga uku zynah, zynah,!

Am’abuwa na shigo wa, itama ihu tana, bakura be tsaya bata lokaci ba, hannu yasa ya cicibi zynah dake kwanta, ya sagalata a kafaďa, ba tare daya bi takan baby ba, shi ta matarsa yake, Am’abuwa ce ta dauki baby cikin wani ďankwalin zynah dake kan gado, ta haďa da mahaifar suka fita zuwa mota”.

A baya ya shinfiďata, sannan ya dawo suka shiga, suna shiga a tsiyace yaja mota zuwa asibiti, duk maganar da Am’abuwa keyi, jinta kawai yakeyi domin bemasan mai take faďi ba”.

Suna isa taimakon gaggawa Dr suka bata, ita da baby, duk da tana motsi,amma batasan me sukeyi a kanta ba”.

Bakura dake waje, sai kai da kawowa yakeyi, a bakin kofar ďakin, bayan su gama suka fito, domin tasamu bacc, yanzu hutu kawai take bukata”.

Dr ďin tana fitowa,da sauri bakura ya taresa da Dr yaya jikin nata?”

Jiki da sauki, dama galabaita ne, amma idan suka samu hutu, insh Allahu komai zai dai-daita”.

To kawai yace, a lokacin ne, Am’abuwa tayi tunani kiran gida ta sanar masu, number hjy ta kira, lokacin suna falo suna breakft, gani number Am’abuwa ne yasa hjy dagawa da sallama”

Tana hjy, dama kira nayi na sanar dake, muna asibiti”.

Da sauri hjy tace keda wa?”
Amina ce ta haihu”..
Kafin ta karisa maganar, tsaki hjy tayi, sannan tace, saime?dan ta haihu?”.

Jin haka yasa Am’abuwa ta fara yiwa hjy nasiha, cikin masifa hjy tace,ke dakata nifa na haifeki, bake kika haifeni ba, sabida haka kisan abinda kika ciki, idan ba haka ba, ranki ya baci”.

Sake wani tsakin tayi haďe da kashe wayar ta”.

Bakura dake zaune kusa da ita, kallo daya yayi wa Am’abuwa ya gano ba alkhairi hjy ta faďi akan haihuwar ba, ďan karamin tsaki kawai yayi, aroud 12PM daya daga cikin nurse ce ta fito tace subada kayan da za’a sawa baby”.

Dukkansu a lokacin ne, suka tuna da maganar riga, hannu yasa aljihunsa ya cire A.T.M ya mikawa Am’abuwa yace taje ta cire kuďi, tayi siyayyar daya dace”.

Zynah bata falka ba,sai bayan azahar, ta samu sauki sosai, akan yadda suka kawota”.

Saida bakura yaga zynah ta samu sauki sosai, sannan ya kira daddy ya sanar masa da haihu”.

Daddy yayi murna sosai da kuma fatan Allah shi ďaiyaba”.

Kwanan zynah biyu a asibiti aka sallamesu suka koma gida, bayan su koma ne, bakura ya kira daddy ya faďi masa yadda sukayi da hjy, da kuma dokar data sanya masa, murmushi daddy yayi sannan yace kada ya damu, zai mata magana”.

Koda daddy yayiwa hjy magana duk a banza, maganar kada ya fita a gidan Adyra kan ta yafe masa,amma zuwa duba mai haihuwa kam babu yadda daddy bai yiba amma taki zuwa dubasu”.

Tunda suka dawo daga asibiti Am’abuwa ce ke kwana dasu, ita kuwa Yah-na, ko lekau, batazo ta duba suba, balle taga baby, hakan bai dami bakura ba, sabida yasan ta hannu damar hjy ce”.

Gani haka yasa bakura tafiya gidan hjy Ashe yaje ya sheda mata, hakuri kawai ta bashi, sannan tace kada ya damu zatazo tayi mata magana, koda hjy Ashe tazo tayi mata magana, nan ma duk a banza, daga karke dai, daga karke dai zuwa tayi taje gidan bakura ta dauko babyn ta kawo mata akan tasa mata albarka”.

Mikewa tayi tabar mata ďakin, kaďan ya rage ma ta ture baby ta faďo daga bakin gadon da aka ijeta”.

Sabida bakin ciki har kuka saida bakura yayi, haka kullum yake yawo, a gidan zynah yake yini shida Am’abuwa, baya tafiya gida sai dare, saiya barsu da Am’abuwa, dama tunda suka dawo daga asibiti Am’abuwa take kwana dasu”.

Kwana hudu da haihuwa hjy ta kasa ta tsare dole sai dai Am’abuwa ta dawo gida, idan ba haka ba zata tsine mata, babu shiri ta koma gida”.

Suleja bakura yaje ya sanar wa kanďe da haihuwar zynah, kuma yanaso tazo ta zauna dasu har tayi arba’in”.

Bayan tayi masa barka ne tace itafa bazata samu zuwa ba, sabida anan take samu tayi sanar da take cin abinci, amma idan ta bisu waye zai bata kuďin da take samu?”.

Bakura yace kada ta damu,tayi lissafi tun daga ranar daya dauketa har zuwa ranar da zata dawo zai biyata”.

Nan ya dauketa suka tafi abuja,

Abu namu magani a kwabemu, bakura da kansa yaje shago ya haďo wa zynah kayan su turare, na jiki dana ďaki, da kuma na gyaran jiki, nasha dana tsarki, da kansa duk ya gwada mata yadda zatayi amfani dasu” Sannan ya dauki Am’abuwa sukaje kasuwa, ita ta zubawa zynah kayan fitar suna masu rai da motsi, basu dawo gida ba, saida ta nuna masa telan da yake masu ďiki, suka bashi kayan kuma yace zuwa jibi yakeson kayan”.

Nan suka tsaďance ya biya”

Ban garen Adyra kuwa, ashe yawan fitar da bakura keyi yana damuta, tanaso da tambayesa amma tana shakkansa, amma yau kuwa yariga tasha alwashin saita tambayesa inda yake zuwa yakai dare, gashi yana sallar asuba idan yabar gidan baya dawowa sai dare”.

Da shike, gobe suna, tunda ya fita bai dawo gidan ba sai bayan *11:PM* tana zaune a falo tana jiransa, yana isowa da sallama ya shigo, Adyra na zaune amma bata amsa masa ba, juyawar da zaiyi ya ganta zaune, sannu da gida kawai yace, yasa kai zuwa ciki”.

Da sauri ta bisa cikin ďaki, yana shiga ya fara tubewa, Adyra itama tana shiga ba tare data dubi fuskansa ba, tana wai kai dan Allah ina kake zuwa ne, kakai har dare baka dawo gida ba?”

Tambaya kika ko niman sani?”.
Tambaya nakeyi”.
To gun matata nake zuwa”…
Wht????”.
Tace” Sannan tace, kai haba wasa dai”.

Ina wasa dake ne, balle har kiyi tunani ba gaskiya nake faďi ba? Ko hjyn da taje niman auren naki bata sanar dake inada mata bane?”

Take hankalin Adyra ya tashi, domin duk maganar da bakura ke faďi gani take kamar wasane”.

Nan take ta sulale ta faďi a kasa, idonta nakan bakura kam, ko kibtawa batayi, shiruuuuuuu tayi na ďin wani lokacin, can kuma kamar wacce aka tsikara, da sauri ta mike, haďe da cewa wlhy karyane, baka isa bakura, nice da kishiya? It can possible”.

Bakura naji haka murmushi kawai yayi mata, ba tare daya tanka ba, yaci gaba da tubawarsa, yana cikin rire riga kenan tayi tsalle ta cukuikuye masa rigan, yadda ba zaiga gabansa ba”.

Sakeni, kawai yace mata”.
Kin sakinsa tayi, saima tsine masa da takeyi, tana faďin Allah ya isa, shegu tsinannu, ma yaudara”.

Tambayar darko da bakura yayi mata, shine, waye ma yaudaran? Ni ko su hjy?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button