ZYNAH Hausa Novel

Oho, koma waye, kuma wlhy yau saika sakeni, azalumai kawai”..
Kafin ta rufe maki, ji kawai tayi tass tass tass, har sau uku akan fuskanta”.
Wani irin ihu tasa, nan ta kara rikesa sai dai suyi ďanbe”.
Igijeta yayi ta faďi a gefe, sannan ya a karisa tubewarsa, gani ta dauki waya tana kuka, daga gani iyayenta zata kira, yasa bakura karbe wayar, dashi ya shiga toilet, bayan yayi wanka ya shirya, da wayar yaje falo ya kwanta, duk zagin da take masa, be tanka ta ba”.
Ranar kwana tayi tana tsine su hjy da daddy” Duk abin yana masa ciwo, amma haka ya ďanne, domin a cewarsa ba’anan ya kamata ya hukuntata ba”.
Da safe kuwa yana sallar asuba yayi wanka ya fita, be bar mata wayar ba, dashi ya fiya, yaje gun suna” A masallaci ya raďa wa yarinyarsa suna *FATIMA* sunan anty Am’abuwa kenan, amma zasu rinka kiranta da *PAKHRYYA* yau kusan kwana yayi a gidan”
Washe gari bayan kanďe tayi pakhryya wanka ta shirya ta, bakura ya dauketa zuwa *WUSE MARKET* gun wanzamai ya kaita, zani sukayi mata, irin nasa, na barebari,sannan ya dawo da ita”.
Tunda Adyra taji cewa bakura yana da wata matan bayan ita, ta daina kulasa, ko a jikin bakura, sabida ba itace a gabansa ba”.
Bayan kwana buyu da suna, yace ta shirya zasu tafi unguwa, da farko kin zuwa tayi, saida ya fito mata a namijinsa sannan ta dauki mayafi suka fita, kai tsaye gidan su hjy suka nufa”.
Gani gidan hjy ne, tace bazata fita a motar ba, itafa saida ya medata gida, ďan bataga abinda zatazo tayi a gidan ba”.
Fika ta karasa, hannu yasa ya fisgota, janta yakeyi kamar wani kayan banza, har zuwa ciki”.
Suna shiga falo yayi hurgi da ita, dai-dai lokacin hjy na fitowa daga ďakinta, gani hakan yasa ta fito da sauri haďe da tambayar lafiya?”.
Jin haka yasa Adyra fashewa da kuka” Bakura yana shigowa yace dama alkawari na dauka wa kaina, bazan hukuntaki a gida ba sai a gaban hjy, dan haka yanzu zan maki hukunci dai-dai da laifinki”.
Hjy najin haka tace subhallilahi, me zangani haka?
To wlhy baka isa ba, a gaban tawa?”
Dukawa yayi har kasa yace, dan Allah hjy kiyi hakuri, domin nariga nayi alkawarin hakan, sabida ita bazanyi kaffara ba”.
Cike da mmki tane,
Mai tayi maka?”.
Ba tare daya tanka hjy ba, yaci gaba da cewa, ke idan kinada kunya kyayi magana? Banza wawiya sha-sha-sha, mara kamu kai, Allah wadarai dake, banza er’iska kawai”…
Kafin ya karisa, tuni hjy ta daukesa da mari, tana faďi lalla bakura, abin naka har yakai ga haka? A gaban tawa? Zaka rika zaginta”.
Faďa sosai hjy taci gaba dayi masa, duk yadda bakura yaso yayi mata bayani amma hjy taki sauraransa, da zuciya ya ďibi bakura ficewa yayi ya bar gidan”.
Kai tsaye kasuwa ya nufa, bai sske bi ta kanta ba, saida dare yayi sannan yazo ya dauketa, zuwa gida. Har yasa kafa zai fice yasake juyowa yace, na rantse da Allah idan kika leka nanda bakin kofa Allah ya isa ban yafe maki ba, sannan yasa kai ya fice daga gidan” Tunda yabar gidan, gidan zynah ya koma da zama, bai sake bi ta kanta ba”.
*★★★★ ★★★★*
Kwaanci tashi babu wiya, har zynah tayi arba’in, daga ita har pakhryya sun gare suyi kyau sosai, musamman ma pakhryya tayi wayo sosai, ita kuwa zynah tasha gyara har taji babu daďi, ina ruwan nida abata, bakura ka gyara ďah/ matan wasu ma balle taka”.
Kanďe nata koma gida sulaje ba, saida takai kwana hamsim sannan bakura ya haďa mata sha tara ta arziki, sannan ya kaita har gida, gani irin hidimar da yayi mata,ba karami daďi taji ba”.
Ban gare Adyra kuwa, hankalinta yayi matukar tashi, sabida yau tsawon kwana arba’in kenan batasa bakura a ido ba, gashi kuma batada da kuďi a waya balle ta kirasa, ko takira hjy ta sanar mata da abinda ake ciki”.
Bakura yana meda kanďe gida, be biya shago ba, gida ya dawo kai tsaye hannu biyu ririke da kaya, ganisa rike da kaya, da sauri zynah ta ije pakhryya dake hannunta tazo ya amshisa, haďe da yimasa hannu da zuwa”.
Murmushi bakura yayi, sannan yace kema sannu, gani zata zauna ne yasa bakura cewa a’a zo muje daga ciki, hannu yasa ya dauki yar’sa, sannan suka shige bedroom”.
Suna shiga ya kwantar da pakhryya a gefe,sannan ya zauna a bakin gado, hannu yasa ya dauko ledar daya shigo dashi, nan yafara ciro kayan daya bayan daya, kayane nata dana pakhryya, masu kyau da tsada, sabida murna zynah batasan lokacin da tayi masa tsalle a jiki haďe dayi masa godiya, shima rungumeta yayi yana meda mata da dariyar da take masa”.
Runguma sosai bakura yayi mata, gani zayi mata kiss da sauri ta nimi sauka daga jikinsa, gani haka bakura yace lafiya my zynah?”.
Shiru kawai tayi, ba tare dace masa komai ba, hannu yasa ya sake jawota jikinsa, a sanyaye tace dan Allah kabari”.
Na bar me kuma zynah?”
Abinda kakeson yi mana”.
Mamaki ya kamasa, kasake jawota yayi jikinsa yace zo my wife, faďimi manene?”.
Babu komai, kawai tace”.
A’a my minel ban yarda ba, gani tashi shiruuuu yasa bakura fara shafeta a hannnnkali haďe da lalabarta, kuka zynah tasa tana faďi masa irin wiyar da tasha lokacin haihuwarta, da kuma yanzu ummanta takeson gani”.
Hakuri ya bata game da maganar wiyar da tashi a lokacin haihuwar, maganar zuwa gun umma kuwa, cewa yayi sai yaje suleja ya tambayi kanďe, address ďin garin, idan ta bashi sai yazo suyi shirin tafiya”.
Da sauri tace,a nima nasan hanya, zanma iya zuwa da kaina”.
Da sauri bakura yace, niwa!! Dan Allah ki rufemi asiri, idan ba so kike kisani a wani hali ba”.
Dariya zynah tayi masa, haďe dayi masa gwalo, Au!!-ni kikayi wa haka?”.
Jin haka yasa zynah sauka daga jikinsa da sauri, gudu tasa zata fice daga ďakin” Shima binta yayi da gudu yana kokarin kamota, nan suka fara zagaye ďakin”.
Idan bakura zai kamota, sai ta doje masa,daga haka, da gangan yayi kamar santsi ya daukesa faďi yayi yana faďi wayyoooooo Allah na” Gani haka yasa zynah zuwa a guje ya faďa kansa tana fsďi subhallah, dan Allah ka tashhiiiiii”. Karafffffff yayi ya riketa yana mata gwalo, tana kokarin mikewa ta gudu, wufffffff yana ya dauketa ya dorata a jikinsa, matseta yayi a kirjinsa yana kashe mata ido, haďe da tsikaranta, idan tayi tsalle sai bakura yasa dariya, da haka har wasa ya canza”.
Ban garen Adyra kuwa, gani yau bazata iya hakuri ba, bedroom taje ta dauko mayafinta, ta fita zuwa gidan hjy, da kuka ta shiga gidan,a gigice hjy ta mike da Ni’eemat lafiya? Me yake faruwa?”
Nan ta kwashe komai ta faďiwa hjy, tana kuna, kamata tayi ta zaunar da ita, ďaki taje ta dauko wayarta, nan tafara kiran number bakura,hjy tayi kira yakai ten misss call amma bakura be daga ba, gani haka yasa hjy ta kira yaran shago, bayan su gaisa ne take tambayarsu bakura, yace ai yau kwata-kwata oga bezo shago ba yau”.
Jin haka yasa hjy bata tsaya bata lokaci ba, hijab kawai ta dauka, ta fice zuwa gidan bakura, tana shiga a falo ta tsaya tana doka sallama, lokacin su bakura suna ciki, yana kan network, balle yadda ya daďe be ha’u online ba, shiruu da hjy taji yasata sakai zuwa cikin bedroom, tana shiga ganinsu tayi hajaran majaran, ihuuuu hjy tasa tasa salati, tana faďin na shiga uku, da jego amma kuke iskanci”!!!
Saida fa hjy ta koma falo kenan, take faďin haka, domin tana ganisu cikin wannan yanayi komawa tayi da baya”.
Su bakura kuwa duk besan hjy nayi ba, zynah ce taji, kuma babu yadda batayi da bakura ya sauka ba,amma yariga yayi nisa, baysjin kira, balle yadda ya gwarata da kansa, abin bana wasa bane”.