HAUSA NOVELZYNAH Hausa Novel

ZYNAH Hausa Novel

Hjy tafi thirty minutes tana jiransu amma basu fito ba, dole yasa hjy ta tafi”.

Koda ta koma gida, Yah-na ce, tace kin dawo?”.

Shiru hjy tayi, domin gaba daya wani iri takeji, ta rasama meya kanta gidan?”

Hakuri ta sake bawa Adyra, tace ta tashi taje, da kanta zata kawo bakura har gida”.

Bakura kuwa saida yakai jeki, sannan ya dashi,daga kan zynah, bayan suyi wanka ne, zynah take sanar masa da zuwan hjy, da mamaki, yace shifa kwata-kwata bemaji zuwanta ba,jawota yayi suka kwanta, tare da pakhryya, ra suka sata a tsakiya”..

Suna cikin hira kenan saiga kiran hjy ya shigo wayarsa, a lokacin ne yaji kunya, da zynah tace hjy tazo ta samesa haka”.

Amma yaya zaiyi, dole yasa ya mike yasa kaya yaje, kunya ya hana bakura daga kai su haďa ido da hjy, duk da itama haka ne a gareta, amma sai ta daure fuska, ta faske”.

Nan ta tambayesa, dalilin yin haka”.yau da yake da lalama ta bisa, yana duke a gabanta, ya zauna mata komai, harda watsar da budurcinta da tayi a waje, sannan kuma ya tambayeta dalilin boye mata aurensa da sukayi”…

 

*~~~~ ~~~~~ ~~~~*

_*KUNCI*_

 

dan Adam kenan, kekikace an haihu, kuma kikace ďah ya koma”.

Tunda rakiya ta amshi girki, ta hana sadiya, idan har taga malam shehu yashiga ďakin sadiya kusan kwana takeyi bata bacc, sabida bakin ciki”.

A zuciyarta tace bazai yuwu ba, me girki daban me kwana da jiki daban, to wlhy cikin ciyu saidai ayi daya”.

Daga lokacin ta fara lissafi, gani girki ya dawo kanta, rakiya ta tubure tayi furrrrrr tace, sai dai tace sai dai cikin biyu ya zabi daya, domi tagaji da yiwa kantuwar banza aiki, ita kuma tana kwana da miji”.

Tun daga lokacin malam shehu ya daina shiga ďakin sadiya”.

Bayan kwana biyu,bayan rakiya ta kare girki, barinsa tayi kitchen ďin ta koma ďaki, batafi minti biyar da shiga ďakin ba, tafara ciwon ciki, nan tasa zainab takira mata sadiya, bayan sadiya tazo, tace dan Allah ta taimaketa taje kitchen ta dauko mata abincin malam shehu, bata musa ba, sabida gani yadda take murkusu-murkusun ciwon cikin”.

Tana daukowa ta ije sannan ta fita, bayan ta fitane, rakiya ta mike haďe da kwashewa da dariya, bayan malam yazo cin abinci, da sauri rakiya ta rike masa hannu tana faďin a’a malam ban shirya takaba ba, dama na barshi ka gani a matsayin sheda ne, malam da rashin fahimta yace, nifa ban gane ba rakiya “.

Nan rakiya ta shirya masa karya da cewa, da idona naga sadiya tana zuba maka guba a cikin niyar, ni kuma dai-dai lokacin ina fitowa wanka, na ganta, ita kanta bata san na ganta ba, idan kuma kana gani kamar karyane ka kirata kasa taci miyar a gabanka”.

Kwaďawa sadiya kira tayi, da sauri ta fito daga ďaki, taje jin kiran malam, tana zuwa malam yace saidai ta dauki miyar taci a gaban sa, sadiya tace itafa bazata ciba, sabida batasan abinda rakiya ta zuwa a ciki ba, nan take rakiya tasa kuka da cewa sadiya tana tayi mata shirri”.

Wannan ya faďi, wannan ya faďi, nan faďa ya tashi, gani haka yasa malam shehu koran sadiya daki, tun daga lokacin koda gaishesa tayi baya amsawa, ita kuma rakiya ta daina sawa yaran sadiya abinci, duk da malam yana gani amma beyi magana ba”.

Suyi shari’a a gun mai gari har su gaji, amma besa malam shehu ya canza hali ba, gani haka yasa sadiya barin gida, ita da yara, ta koma gidan iyayenta, duk da babu kowa a cikin gidan, domin iyayenta duk su rasu, amma hakan be hanata zama ba, nan suka fata malejin rayuwarsu, tana soya masu gyaďa suna talla, a nanne suke samu abinda zasuci”.

Tun daga lokacin da sadiya tabar gidan rakiya ta shiga yiwa malam shehu rashin mutunci iri-iri, zainab kuwa idan ta fita tun safe bata dawowa gidan sai dare, gani haka yasa malam shehu yace aure zaiyi mata ya huta”.

Hakan yasa ya bada sadakarta ga garon maigari, domin dama kwanaki maigari ya bata basa magana akan zainab ďin, yace yana nima wa ďansa”.

Ba’a dau lokaci ba, akasha biyan zainab da usman, usman yana murna zai ragargaji amarya, sai kuma be samu haka ba, ko kufar * kuyanbana* dake zaria be kaita buďewa ba, tun cikin daren ya naďa mata duka, domin kuwa usman ba mutuncine dashi ba, balle dama gani yake kamar wani uban kuďine ubansa ya kashe a wajan nema masa aurenta”.

Da safe ta tashi zata tafi gida, yace wlhy idan har tasake tabar gidan to kuwa a bakin aurenta”.

. dole yasa zainab ta hakura ta zauna” Kullum cikin zagi da cin mutunci, babu irin wanda bata gani a gun usman”.

Ban garen malam shehu kuwa, tun bayan bikin zainab yake zazzabi,”””..

 

~~~~ ~~~~~ ~~~~

Koda bakura ya tambayi hjy da lilin boye wa Ni’eemat yanada mata da tayi, hjy bata bashi amsar haka ba, faďi dai tayi wa bakura sannan tace idan baso yake tayi masa bakiba,dai to”.

Sani hali yafi sani kama, tan daga lokacin bakura ba karamin kiyayewa yakeyi ba, amma fa bai hanasa zuwa gidan zynah ďinsa ba, idan ya rage gajiya saiya tafi kasuwa”.

Bayan kwana biyu hjy da kanta taje gidan, bakura lokacin yariga ya fita kasuwa, bayan su gaisa, hjy tace Ni’eemat”.

Na’am hjy”
Gunki nazo, wata magana nakeso muyi dake, amma kuma inaso ki faďi min gaskiya, faďin gaskiya da zakiyi shi zaisa na sami maganin matsalar dake yawan shiga tsakaninku da mijinki,amma idan kikaki faďi min kuma tofa babu ruwata, da duk wani matsalar da zai sake tasowa a tsakaninku”.

Mijinki yace bai sameki cikakkiyar mace ba, kada kiji kunya, ni uwarki ce, zanso ki faďimin gaskiya”.

Nan tasa kuka, tana faďin eh hakane”
Salati hjy tayi ta sanar da ubangiji, sannan ta tambayeta garin yaya?”

Shiru tayi sabida batada amsa”.

Gani kukan da takeyi yasa hjy, cewa kiyi shiru, ki daina kuka haka, Allah ya kiyaye gaba, kuma insha Allahu babu zanda zaiji wannan maganar, idan har wannan maganar ya fita wani yaji, tofa kece,amma bani da bakura ba, sai dai wani hanzari ba gudu ba, daga har iyayenki ban faďi masu kamar bakura yana da wata mata ba, kafin ke, kuma bana bukatar susan haka”.

Ni’eemat idan har kika rufe wannan maganar to wlhy ina mai tabbatar maki babu wanda zaiji, Ni’eemat kifi kowa sanin a al’adarmu ta barebari babban abin kunyane ga iyaye ace yar’su batakai budurcinta gidan miji ba”

Ni’eemat idan har kika rufe wannan maganar, ina me tabbatar maki babu wanda zaiji abinda kika aikata”.

Ni’eemat tasan hakan ba karamin abin kunya bane ga iyayenta idan wannan zance ya fita da sauri tace, naji kuma na amince, insha Allahu babu wanda zaiji”
Nan sukayi sallama”.

Tunda daga lokacin hjy tasawa bakura ido sosai, duk motsin da zaiyi akan idanta, gashi ta tsani pakhryya dan ji takeyi kamar ta rufe ido ta bude taga bata raye”.

Koda Am’abuwa ta daukota yini, ko kallo bata ishi hjy ba, haka kuma koda kukan jini zatayi, idan Am’abuwa bata kusa, hjy bazata dauketa ba, idan ma tare suke, sai dai ta tsallakata ta shige ďaki”.

Yanda bakura yakejin zynah yanzu, koda yau ne yafara sanita sai haka, ga uban maganin mata dayake ďurra mata, planning kuwa tuni ya dade da bata magani tsarin iyali, wanda zai dauketa har shekara biyu”.

Hakan yasa yanzu yake like da ita, dan ma hjy tasa masa ido ne, babu yadda zaiyi”.

Gani takuran yayi masa yawa, karya ya shirya wa hjy, da cewa zaiyi tafiya zuwa *DUBAI* domin akwai wasu turare da mayuka da suka kare, gashi kuma ana bukatarsu sosai, idan haka yakeso yaje dubai ko zai samu, amma idan bai samu ba zai wuce har india,domin duk cikin kayan shagon sufi kawo kudi”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button