ZYNAH Hausa Novel

Jin haka yasa hjy bata musa ba, saima fatan alkhairi da tayi masa”.
Yah-na ba matsalarsa bane, Am’abuwa kuwa ce mata yayi zaika zynah suleja idan yadawo daga tafiya zaije ya dauketa” Itama Adyra haka yace mata, duk basusan zasu soyewarsu bane, hakan yasa yace kada kowa ya rakasa, driver ne kawai ya yarda daya kaisa, ita kuwa zynah shirin larabawa yayi mata, domin hatta hannu saida tasa safa, balle kafa ko fuska”..
Ta rigasa isa airpot, sannan ya iso, bayan driver ya tafi ne, yaje inda take zaune ya amshi pakhryya, nan suka zauna suna hira, har lokacin da zasu shiga jirgi yayi, waje ďaya suka zauna, bayan an kammala komai suka jirgi ya tashi zuwa dubai”….
*mmn uswan ce????✍*
????????????????
_*ZYNAH!!!*_
????????????????
*WRITTEN ✍ BY MMN USWAN*
_______________
©©©©©©
_*follow me on*_
_*wattpad:Hauwa s zaria*_
_*Facebook group*_
_*Mmn Uswan*_
https://www.facebook.com/groups/157572201857733/
➿➿➿➿➿➿
_*BISLLAHI RAHAMANI RAHIM*_
_*In the name of Allah, The Beneficent, the Merciful*_
????3⃣0⃣-3⃣5⃣
Su bakura suna isa, taxi ta samu masu, su h’au zuwa hotel ďin dazasu sauka”.
Pakhryya na hannu babanta yana mata wasa, idan ba dariya ba babu abinda takeyi”.
“Suna isa sallah suka fara yi, domin shine gaba da komai, sannan bakura yasa aikai masu order abincu, suna gama ci sukai wanka, Pakhryya kuwa zynah na mata wanka bacc tayi”.
Saida bakura ya huta sosai sannan ya kira hjy ya sheda mata ya isa, bayan su gama magana da hjy ne, ya kira Am’abuwa itama yashe mata”.
Ita kuwa Adyra bai samu kiranta ba, sai cannn cikin dare, tana bacc kamar a mafarki taji wayarta na ringimg da sauri ta ďaga, domin tasan ba kowa ne zai kirata a wannan lokacin ba sai bakura”.
Da sallama ta daga, haďe da gaishesa da gajiyar hanya, yace, hanya alhamdullh” Be dauki lokaci ba sukayi sallama”.
Wanka sukayi suka shirya cikin english wear,kalar kayan su irin daya harda Pakhryya, marron colour, ba karami kyau dressing ďin yayi masu ba, lokacin da zasu fita bakura ya dauko after dressing ya dora mata akan kayan jikinta, sannan suka fita”.
Tunda suka fita kuwa, basu dawo gidan ba, saida bakura ya kaita guri-guri, pict kuwa ba’a magana”
Ban garen zynah kuwa, cire duk wani kunya tayi ta nuna wa mijinta tsatstsan tsagwaron soyayya, idan da suyishi kantakile ne to yanzu ta kile, wani abu idan tayi har mamaki bakura keyi, hakan yasa shima ya dirje ya nuna mata soyayya, pict kuwa duk inda sukaje sai suyi, bakura ke turawa facebook instagram,” duk pict ďin da zasuyi Pakhryya na tsakiyarsu”.
A ban garen hjy kuwa kullum cikin kira takeyi ta tambaya ko yasamu kayan”.
Ana gobe zusubar Dubai hjy ta sake kira, tana tambaya, bakura cewa yayi, duk inda zaije dan yasamu yaje bai samu ba,shi isa ma gobe yakeso ya dawo gida”.
Da sauri hjy tace, a’a kada ya dawo, daga nan ya wuce india ko chana, maybe Allah yasa a samu a can”..
Da sauri yace, to hjy, nan sukayi sallama, dama bakura ya faďiwa hjy hakane, amma har cikin zuciyarsa ba haka bane”.
Daga Dubai basu tsaya ko ina ba, sai india, nan ma kwanansu hudu sukar kasan zuwa england, daga nan basu tsaya ko ina ba sau saudia, bakura yaso suyi aikin hajji ne,duk da dai shida yayyunsa suriga suyi amma kogi beki kari ba, sai dai gashi ba lokacin aikin hajjin bane dole yasa sukayi ummah, nan ma susha pict kamar babu gobe”.
Allah sarki adyra, kwata-kwata bakura ya mance kamar yana da wata mata nayan zynah, dama hausawa suce matar shige bata daraja,gani be cika kiranta ba, yasa utama bata kiransa, haka taci gaba da zaman kadaita”
Duk inda suke hjy na bibiye dashi wajen kira da massage, harda video call take cewa suyi, dai-dai lokacin yana cikin wana kanti yanawa Pakhryya siyayya saiga kiran hjy, da sauri yace zynah ta dawo bayansa, saida ta dawo bayansa sannan yayi receiving call ďin, haďe da sallama, duk da ba ganisa takeyi ba, amma hakan be hana bakura dukawa ba, abinda su ringa da su saba”.
Bayan su gaisa, hjy tace, bakura yaya kuma haka?”
Eh wlhy abinda yasa nazo nan, zuwa nayi na duba ko zan samu anan, idan ma ban samu ba, nasan baza’a rasa wasu kalar ba, kuma inasa ran suma zasu samu shiga”.
Ok, amma dan Allah kaduba masu kyau da kamshi”.
Ok, kawai yace”.
Har zata kashe wayar, can tana waye a bayanka,kuma kamar da baby a hannunta?”.
Da sauri yace, ban santa ba, amma ina gani kamar itama siyayya tazo yi”.
Ok, hjy tace, sannan sukayi sallama, satin su biyu a saudia, bakura beso komawa gida a wannan lokacin ba, amma jin ance daddy ya dawo dole yasa suka haďe kaya zuwa nigerin”.
Zynah tayi kyau iya kyau, idan ba kasanta ba, ba lalla ne in kaganta yanzu ka ganeta ba, domin gaba daya ta canza kota kowani ban gare, domin bakura yayi kokari sosai wajan gani ya koya mata turanci, da larabci, barbanci kuwa, zama yau da gobe yasa ta iya, domin yanzu bai cika ji mata hausa ba, cikin ukun ga daya yake mata, turanci, larabci, or barbanci, kuma dole ta bashi amsa, idan ma tabashi da hausa ba amsata yakeyi ba, dole yasa ta iya, Pakhryya kuwa itama shi suke mata”.
Bakura bai faďi ma kowa yana hanya ba, sabida kada azo tar bansa,a gansa da zynah, suna sauka bakura ya dauki mai taxi zuwa jabi, hanyar baya ya nuna masa, wanda zai kansu dai-dai da ta inda gidan zynah yake, bayan su sauka ne, ya sake komawa yaje ya shigo ta gate ďin gaba, sallamarsa cikin falo yasa duk mutane dake zaune a falo suka amsa da mamaki”.
Da sauri bakura ya saki jakar dake jannunsa yaje ya rungume daddy yana masa sannu da zuwa, gani bakura ya kara kyau da kiba, yasa daddy cewa, amma aure ya amsheka, kada yadda kayi kyau kuwa babana?”
Dukkansu dariya sukayi, nan shima aka shiga masa hannu da hanya, hjy tace meyasa be faďi kamar yana hanya ba azo a tar besa?”
A’a hjy, so nake na shammaceku”. Duk dariya sukasa, jin daddy yace ina matarsa, take hjy ta canza fuska, kamar ba ita ke dariya ba, kan bakura na duke yace suna suleja,amma yau ko gobe zanje na dauko su, ya kamata kawai daddy yace”.
Ita kuwa hjy, tsaki tayi” Bakura bebar gidan ba sai bayan isha, saida yafara zuwa sukayi sallama da zynah sannan ya tafi gidan Adyra”.
Har ta kwanta, taji ana knocking, kafin ta tashi saiga kiran bakura ya shigo wayarta, saida tayi tsaki sannan ta daga wayar, shiruuuuu tayi babu ko sallama, ji kawai tayi ance zo ki buďe min kofa”.
Bata musa ba taje ta buďe basa, tana buďe wa bakura ya kai mata runguma yana faďin oyoyo matata, wani irin hankaďa takai mata, haďe da cewa dallah ja kabani gu, dan walakanci sai yau ka tuna kanadani?”
Shima kansa yasan bai kyauta ba, shi yasa be nuna fushi ko damuwa ba, sabuda yasan koda dabba ka’ije a gida zaka waiwaiyeshi balle mutum ďan Adam, ita kuwa Adyra bedroom ta koma tayi kwanciyarta, saida ya rufe gida sannan ya bita bedroom ďin”.
Yana shiga tube wa yayi ya shiga wanka,yana fitowa ko bayan bacc be saba ba, yaje ya samu bakin gado ya zauna, juyawa yayi yana kallonta haďe da cewa tashi ki ďibomin ruwa, Adyra najinsa amma ko motsi batayi ba, balle tayi yunkurin tashi, bakura ya sake magana, nan duk a banza, mikewa yayi yaje ya ďibi ruwan da kansa yasha sannan yazo ya kwanta”.
Har Adyra ta fara bacc taji bakura na shafota, hannu tasa ta bige masa nasa hannu, duk da haka beyi fushi ba, saima kokarin jawota jikinsa da yakeyi, yana faďin haba my madam, yanzu sabida Allah fushi kikeyi dani? To naji koma menene kiyi hakuri”.