HAUSA NOVELZYNAH Hausa Novel

ZYNAH Hausa Novel

Duk bakura na maganar ne yana shafeta, shiruuuu tayi ko motsi batayi, shi kuwa bakura yaci gaba da cewa, nasan kina fushi sabida rashin kiran da banyi maki bane ko? Wlhy wasu al’amura ne suka shami kai amma kiyi hakuri”.

Gani har a lokacin bata tanka masa, kuma yasan ba bacc takeyi ba, yasa bakura hayewa jikinta yana kokarin kai mata kisss”.

“Da sauri ta turesa ta mike zaune, tana faďin, dallah can malam, ni zaka raina wa hankali?to wlhy baka isa ba, kuma abinda kakeson yi wlhy bazan bayar ba, ai ba sha-sha-sha bace ni, kaje ka kwaso jatabarka kazo ka sauke anan, to bazan bayar ba”…

Dallah can malama bakima gode ba, taimakoki fa zanyi, idan ba taimako ba kema kinsan nafi karfinki,”.

“Taimako fa kace?”
“Kwarai da gaske”

Allah ya kiyaye, kai bakura bari kaji wlhy idan banda iyayenka su boye min ba, wlhy babu abinda zanyi dakai, banza ma yaudaran banza ma yaudara wofi, kuma wlhy Allah ya isa tsakanina daku, bazan taba yafe maku ba, azalumai kawai”.

A isgilance bakura yace,in da ke kisan kunya har zaki kalli kwayar idona kice iyayena su yaudareki? Ni’eemat kenan, zaki iya faďin abinda yafi haka, amma nasan iyayenki basu isa su faďi haka ba, sabida susan taimaka masu akayi””..

Da sauri Ni’eemat tace, taimako fa kace?”.

Kwarai da gaske,ko kuma nace sabida kuďin iyayena, idan badan kuďinsu ina na taba gani daga tayi sai a sallama? Koda shike, dole suyi haka sabida susan er’tasu kwankoce,”..

Da ssuri ta dakatar dashi, da cewa kaiiiiiii bakura ya isheka haka, duk abinda zamuyi kada ka sake ka zagan min iyaye”.

A marerece yace dan Allah, da gaske kinaso iyayenki? Allah sarki, kuma haka ne fa, iyaye sunada matukar daraja da mutanci, amma a gun er’su”.

Wani irin kallon banza tayi masa, haďe da tsaki, daga sannan  bata sake tanka masa ba, sabida ita kanta tasan bata kawo budurcinta gidan ba, duk abinda zata gani daga garesa dole tayi hakuri, *duk abinda ya sami shamuwa watan bakwai ne yaja mata” Yau inda ta kama kanta be isa ya kalli fuskanta ya kirata da kwanko ba”*

_Kalu bale gareku en’mata, kai budutci gidan miji ba karami kima da daraja yake karawa mace ba, kuma wlhy duk rashin kunyarsa da rashin mutuncinsa be isa ya kalli kwayar idon ka ya faďi maka magana data danganci wannan ba, idan har kikakai budurcinki gidansa, idan zai maki wani rashin kunya, wlhy kinada right da zaki tsaya a gabansa da full comfedacen ki faďi masa magana, sabida shi ya bareki, bakisan kowa ba bayan shi. Amma idan kwanko kikaje ina kikaga bakin magana, kema kinsan sai abinda Allah yayi” Allah ka tsaremu ka tsare mana yaranmu ka kuma rabasu da sheďanu maza hatsabibai ameen_

Hayewa gadon tayi ta kwanta, duk da maganar yana cinta amma babu yadda ta iya”

Shima bakura dauko wandonsa yayi yasa yana faďin banza kawai, a zuciyarsa kuma ji yake kamar ya koma gidan zynah”.

______________

Duk da kasancewar Usman ďan kauye ne, amma da shike yayi karatu, shi isa yake amfani da babban wayar, yana hawa social media kamar su whaAspp instegram facebook, yana kwanta shiga zainab, ta dora kai a jirkinsa suka kallon pict a instegram, sunayi suna hira, sai Usman ya kamo pict ďin su Zynah da bukura,har ya wucesu sai kuma ya dawo da baya, kurawa pict ďin ido yayi sosai, sannan yace zainab”.

Na’am”.
Dan Allah matan cikin pict ďin nan bata maki kama da Amina ba?”

Itama kallo pict ďin tayi sosai,sannan tace, ehhhh wlhy amma dai kamace, ina Amina taga haka? Babu mamaki tanacan tana karuwanci, domin kwanaki ummata taji lavarin wai  anganta a gidan wata magajiyan karuwai”.

Duk da magana da takeyi, jikinta ya bata cewa amimce,  amma hasada ya hanata ta fahimci haka”.

Usman yace, amma wlhy su birgini, kuma matan sunyi kama da Amina sosai, dubi er’su kyankyawa, ina ma da nine, tsaki zainab tayi, haďe da cewa to bakai bane sai kayi hakuri”.

Tayi maganar ne haďe da fisge wayar ta ije a gefe”.

___________

Da safe bayan bakura ya shirya zai fita, yace tashi muje kiyiwa daddyna sannu da zuwa”.

Hararansa tayi, haďe da cewa ban zuwa”

Daddyna ne fa Ni’eemat”
Sai me, idan daddyn kane?”

Ficewarsa yayi, ba tare daya sake tanka mata ba”.

Yana fita saida ya fara zuwa gidan su hjy ya gaishesu sannan ya fita zuwa gidan zynah, yana shiga dai-dai lokacin ta fito daga wanka kenan, pakhryya kuwa an riga anyi mata nata, kwance take a kan gado tana wasa”.

Hannu bakura yasa ya dauketa yana faďin oyoyo my doter, nan pakhryya ta fara masa dariya, zynah tana fitowa suka gaisa, haďe da tambayr su tashi lafiya,fita tayi tare ta kawo masa abin breakft, koda ba inace da girki ba, amma idan mijinta yazo baya hanata karbansa, bakura na karyawa ita kuma tana shieyawa, suna gamawa bayan ta meda kayan kitchen da dawo har zata dauki pakhryya hannu bakura yasa ya rike mata mata hannu, jawota yayi jikinsa yana faďin my wife gaskiya kiyi kyau”.

Murmushi tayi masa, sannan tace nagode”.

Gani yadana niyyar bata mata kyalliyarta da sauri ta mike tana masa dariya, shima mikewa yayi yana mata dariya yace dauko mayafi muje ki gaida daddy”.

To tace, tana dauka suka fita, bakura na rike da pakhryya, suna tafe suna hira har suka isa”.

“Da shike bakura ne a gaba, yasa shine ya fara sallama ya shiga, su hjy da daddy dasu Yah-na Am’abuwa suma duk suna gun a zaune, bakura na shiga har zynah tasa kafa zata shiga, hjy na ganita da sauri ta mike haďe da cewa ina zaki? wlhy idan kika sake kika shigo na lahira saiya fiki jin daďi”.

Jin haka da sauri ta meda kafarta waje, kasa karisawa bakura yayi, cakkk yaja ya tsaya, daddy ne yace jeka ka shigo da matarka”..

Jin haka yasa jikin hjy sanyi, kasa karisawa tayi, dole ta dawo ta zauna, saida bakura yaje ya mikawa daddy pakhryya sannan yaje ya kamo hannu zynah suka shigo tare”.

Asanyaye ta shigo, har kasa ta duka ta gaida daddy, haďe da yi masa sannu da zuwa, daddy da fara’arsa ya amsheta, ita kuwa hjy koda ta juya gun hjy tayi gaisuwa yakai baki uku amma hjy bata amsa ba, gani haka yasa ta juya ta gaida sauran sannan ta zauna, a gafe daya”.

Daddy ko sai faman wasa yakeyi da pakhryya, tana masa tsalle a jiki, Am’abuwa nasa hannu ta amsheta pakhryya tasa kuka tana kallo daddy, babu irin rarrashin da basu mata ba, amma taki dole yasa daddy ya amsheta”..

Tunda zynah ta zauna, hjy ta daina magana, duk maganar da sukeyi batasa baki ba, suna haďa ido da zynah wani irin uban harara take mata, tunda taga haka, bata sake bari su haďa ido ba”.

Ashe daddy ya lura da haka, mikewa yayi haďe da kiranta zuwa cikin ďaki, suna shiga daddy ya hauta da zagi, abinda be taba yi mata ba kenan, tunda suke”

Yana cewa jahilar banza jahilar wofi, ashe haka kike? Wlhy khursum kin ban mamaki, haka kawai kisa masu yarinya a gaba? Ke idan akayi wa naki yaran haka zakiji daďi? To wlhy daga yau sai yau, kada na sake ji ko gani kwatankwacin haka, idan har nagani to wlhy sai nayi mummunar saba maki, ni musulmine nasan kaddara, sabida haka na daukesa a matsayin kaddara, idan banda Allah yana bari mutum da kayansa, daba Allah ne kadai yasan abinda zasu aikata ba”.

Kibar gani ba’a gida nake ba duk abinda kike yiwa yaran jama’a idan suzo aiki inada labari, ke a rayuwarki baki yiwa yara fata na gari, daga kice masu karuwai sai barayi,sabida Allah idan kece aka yiwa naki haka zakiji daďi? To wlhy bazan yarda da haka ba, sabida nima bazanso yarana suje wani gun ayi masu ba, idan banda Allah yana amfani da zuciyar mutum ba Allah kadai yasan irin abinda zasu aikata ba, babu mamaki da awaje zasu haifi yarinyar ga, idan banda jakanci irin naki kodan albarkacin wannan yarinya bazaki raga mata ba?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button