HAUSA NOVELZYNAH Hausa Novel

ZYNAH Hausa Novel

Daga yau sai yau, idan har kinaso mu zauna lafiya dake, inaso ki kyalesu su wala” Buďe baki tayi zatayi magana, da sauri daddy ya dakatar da ita”.

Dole yasa tayi shiru, badan taso ba, mika mata pakhryya yayi shi kuma ya kwanta, dole yasa ta riketa, yana kwance suna magana, pakhryya kuwa sai faman wasa takeyi a hannu hjy, dan ma hjy taki bata saurareta ba”.

Su jima suna hira sannan hjy ta mike taje ta mikewa Am’abuwa ita, ita kuma ta mikewa zynah” su daďe a gidan sannan suka kamo gida”.

Ita kuwa adyra har yanzu fushi take da bakura, koda yayi mata magana bata amsa masa, hakan yasa ya shirya tafiya zuwa kano garin su zynah ba tare da sanar da ita ba, domin a yanda ya tsara wa kansa sai dai taji ya wuce, tunda tace tayi fushi da gaba”.

Gabama harda mijin da kake aure, himm Allah shi kyauta”

Bayan kwana uku, bakura da zynah suka shirya zuwa *kunci* garin su zynah, bakura saida ya shake burn da tsaraba, ita kuwa zynah sai faman munra takeyi, saida suka biya suka sallami su daddy da hjy, gaisuwar bakura ne kawai ta amsa amma banda na zynah, data gaji da tsayuwarta ne ta mike suka fita, Am’abuwa har bakin mota ta rakasu, haďe da bawa zynah kuďi wai tayi tsaraba”.

Zynah tayi godiya sosai, saida taga tashinsu sannan ta koma ciki”.

Tunda zynah tace zata gane hanya, yasa basu biya gidan kanďe ba”.

Zynah sabida murnan gani ummata ko kibta ido batayi, sai faman hura suke zubawa da mijinta’ kamar yadda tace kuwa hakane, haka tayi ta nuna masa hanya, bakura baya musu, duk hanyar data nuna masa haka yakebi, duk da a zuciyarsa yana tunanin kodai su banta hanya ne? Da haka har suka isa garin””””….

 

*mmn uswan ce????✍*

????????????????

_*ZYNAH!!!*_

????????????????

*WRITTEN ✍ BY MMN USWAN*
_______________

©©©©©©

_*follow me on*_

_*wattpad:Hauwa s zaria*_

_*Facebook group*_
_*Mmn Uswan*_

https://www.facebook.com/groups/157572201857733/

➿➿➿➿➿➿

_*BISLLAHI RAHAMANI RAHIM*_

 

_*In the name of Allah, The Beneficent, the Merciful*_

 

????3⃣3⃣-4⃣0⃣

Tun daga kofar gari, aka fata kallonsu, yara na gudu manya kuma, sai faman bin motar da kallo sukeyi, tintake camry ce motar, baka gani mutane dake cikin motar ssi dai su su ganka”.

Da haka har suka isa kofar gidan, lokacin malam shehu yana dawowa daga sallamaci kenan, sabida yau ne ma ya fara fita sabida zazzabin da yayi fama dashi”.

Gani mota tayi faki a kofar gidansa, saida yaja da baya tuku, bayan su parker ne, bakura ne ya fara fita, ya zagayo ya buďe mata murfin motar ya amshi pakhryya sannan ta fito, malam shehu dake makale a lungu yana kallonsu, saida yaji wani irin yarrrrr a jikinsa,amma duk da haka bai gane ko waye ba”.

Saida ta gyara mayafinta sannan suka nufi hanyar gida, zynah na gaba bakura na baya, suka shiga cikin gidan. Gani su shiga gidan sane yasa malam shehu fitowa daga inda yake makale ya nufo gida, da sallama suka shiga gidan” dai-dai lokacin rakiya na fitowa daga banďaki, da sauri ta jada baya, haďe da tambayar malamai wah kuke nema?”

Murmushi zynah tayi sabida tasan rakiya bata gane ta bane, sannan tace inna ninefa”.

A ladabce rakiya tace kecewa hjy?”
Saida ta kira yi mata dariya sannan tace nice amina”””..

A gigice tace amina fa kikace”.
A lokacin ne ta kare wa Amina kallo sannan ta gano ita ďin ce, can zawa da tayi ne yasa ba zakaga neta ba”.

Sulu-suluce rakiya ta faďi ta daka da ďuwawu darab ta zube a kasa, zama tayi dirrrrshap sai faman bin zynah takeyi da ido, baki kuwa a baďe yaki rufuwa”.

Zynah bata bi ta kan rakiya ba, ta nufi hanyar ďakin ummanta, shi kuwa bakura duk inda tabi yana biye da ita, tun kafin ta karisa bakin kofar ta hango dakin a wangale, a lama babu mutum a cikin, hakan ya sata karisawa da sauri ta shiga ďakin”.

Tarkace ne kawai ta gani a ciki, da alama ďakin ya daďe babu mutum a ciki”

A gigice ta fito daga ďakin ta nufo inda rakiya take, tana kokarin tambayar ina ummata””..

Sallamar malam shehu ne yasa katseta, duk da tanajin bakin cikin abinda yayi mata, amma yaya zatayi, tunda ba’a canza wa tuwo suna, hannu ya mika wa bakura suka gaisa, amma duk a lokacin malam shehu be gano Amina ce ba, rakiya dake zaune cikin karkarwan bakin tace, Amina kece haka?”.

Cike da mamaki malam shehu yace wacce Amina?”

Babu abinda yafito daga bakin Amina sai ina ummata take? Malam shehu bebi ta kanta ba, daki yaje ya dauko shinfiďa ya shinfiďawa bakura, bayan su zauna ne suka gaisa, malam shehu yake tambayar bakura daga ina, domin har yanzu kokwanto yakeyi balle yadda gaba daya ta canza”.

Zynah dake tsaye ta samu gu ta zauna kusa da bakura, murmushi bakura yayi sannan ya zaiyana wa malam shehu daga inda ya fito, da kuma aurensa da zynah, babu abinda malam shehu keyi sai kabbara, hannu yasa ya amshi pakhryya, sannan suka kara gaisa wa, ita Amina ta gaida babanta, haďe da tambayar ummata”.

Malam shehu ya meda kallonsa izuwa rakiya dake zaune kamar wacce aka daure a gun, domin tunda ta zube a kasa bata mike ba”.

Rakiya jeki ki kawowa surinkinki ruwa mana” A lokacin ne ta dawo daga tunanin da takeyi, tana mikewa, ďakinta kawai ta nufa batare dace komai ba”.

Tana shiga tasa kuka wii-wii-wii kamar wacce aka daka, tana faďin meyasa nayi wa kaina? Meyasa nasa malam ya kori Amina daga garin nan? Yanzu ďubi yadda ta koma kamar ba ita ba?”.

Shiru da malam shehu yaji ne yasa shi mikewa haďe da faďin bari akawo maka ruwa ko?”

Yana mikewa zynah tace bakura nifa banga ummata ba, Allah dai yasa ba wani abunne ya sameta ba” a’a zynah bari dai baba yazo muji inda take, maybe unguwa taje”.

Himm kawai zynah tace, daga nan bata sake cewa komai ba, hannu tasa ta amshi pakhryya tasa mata nono a baki”.

Malam shehu yana shiga ďakin rakiya gani tana kuka yasa shi karisawa ciki da sauri, haďe da cewa rakiya lafiya?”

Ko kallo malam shehu bai ishi ta ba, taci gaba da kukanta tana faďin na ohh!! Ni rakiya na cuci kaina, nayiwa kaina, wlhy dana sani bansa an kori yarinyar ga daga garin nan, dubi yadda ta koma?”

Cike da mamaki malam shehu yake kallo rakiya dake zaune ne”.

Gani kada su raba abin kunya a gaban suriki yasa shi kita daga ďakin ta barta, taci gaba da kukanta”.

Ta kofar baya malam shehu yayi yaje ya siyo masu kayan sanyi, sannan yasa aka dama masu fura da nono”.

Bayan ya dawo ne, bakura da kansa ya matse ya tambayi malam shehu inda sadiya take”.

Malam shehu ya rasa yadda zaiyi masu bayani, saida ya ďan jinkirta sannan yace tana gidan su”.

Kafin ya karisa tuni zynah ta cire pakhryya a nono ta mikewa bakura ita, sannan ta mike, zomuje kawai tace”.

Kunya ya hana bakura mikewa, ita kiwa zynah, tuni ta mike haďe da cewa zo muje, sannan ya mike, abinda zynah tayi ya batawa malam shehu rai amma yaya zaiyi, duk da har yanzu besan gaskiyan lamari ba, amma a yadda yaji rakiya ke magana yasan akwai alamar tambaya”.

Yana mikewa suka fita, har ta kami hanya, bakura yace tazo suje a mota”.

Cike da takaici malam shehu ya gangara ďakin rakiya, bayan ya zauna ne, cikin dabara da lallashi yake tambayar rakiya, akan furucin da yaji tanayi”.

Rakiya bata boye masa komai komai ba”.

Salati yayi ya sanar wa ubangiji, haďe da kiran rakiya kin cuceni, wlhy bazan yafe maki ba, duniya da labahi, yanzu da wani ido kikeso na kallo sadiya da Amina, banga laifin Amina ba duk abinda tayi, kuma insha Allahu a yau ďin nan sadiya zata dawo ďakinta, ita kuma Amina zan roketa gafara, akan abinda duk ya faru”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button