ZYNAH Hausa Novel

Cikin kuka rakiya tace sai me, idan kadawo da sadiya gidan nan, tazo mana, wlhy sai dai idan ba ni rakiya ba, domin sai tayi data sani dawowarta gidan nan, makwadaicin banza makwaďancin wofi, daga gani mota har jikinka na rawa, to wani yasani ko kuďin shan jini ne, domin ance yaeanci masu kuďin birni duk rn’mafiya ne”.
Ba dare da malam shehu ya tanka mata ba, ya fice daga ďakin”.
Su zynah suna isa kofar gidan ummata, tun kafin bakura yayi baki, hannu tasa zata buďe motar da fita, kallo daya bakura yayi mata ta dakata, har saida ya sami gu yayi parking, saida ya fita ya zagayo ya buďe ya amsa pakhryya sannan ta fito, dai-dai lokacin da hauwa na fitowa daga daga cikin gida, da sauri ta kwaďa mata kora da hauwa!!”.
Hauwa na juyowa suna haďa ido da Amina, a guje Amina taje ta rungumeta tana kwalla, haďe da tambayar ina umma?”
Cike da mamaki sabida hauwa bata gane ta ba” hakan yasa ta tsorata da Amina, balle suna haďa jiki wani irin laushi da kamshi taji na tasowa daga jikin Amina, take jikon hauwa ya fara rawa”.
Zynah dake rungume da ita, tana sakin hauwa a guje hauwa ta ruga cikin gida haďe da kwadawa umma kira, da sauri umma ta fito daga daki tana tambayar lafiya hauwa irin wamnan kiran haka? Umma umma da wasu mutane suzo suna tambayarki, wlhy umma matar kamar balarabiya,dariya umma tayi haďe da cewa labarabi kuma””.
Sallamar bakura ne ya katse umma, da sauri ta dago kai, zynah dake bayan bakura tana hango ummata a guje taje ta rungume umma haďe da fashewa da kuka,tana kiran ummata, umma,ashe dama zan sake ganinki a rayuwata?”
Itama umma dake rungume da zynah kukan takeyi, shiko bakura tsayawa yayi yana kallonsu, da’kar umma ta sai saita kanta, sabida gani subar mutum a tsaye, hauwa akasa ta dauko tabarma, ta shinfiďa mata ya zauna, hauwa dason yara hannu yasa ta dauki pakhryya, duk da dai batasan alakar dake tsakaninsu da ita”.
Duk da kiwan pakhryya amma da hauwa ta mika hannu zata dauke ko musu bayi ba, taje”.
Ďaki umma ta koma ta sanyo hijib sannan ta fito, kusa da bakura taje suka gaisa, lokacin itama zynah ďin ta shiga ďakin ummata, bayan su gaisa ne, umma take tambayar sa daga ina?”.
Murmushi bakura yayi, sannan yake sanar da ita waye shi, wani kokan umma ta sake fasawa dashi, tana wa ubangiji godiya, bayan sallar isha lokacin su gama komai, umma da zynah da kuma bakura suka zauna suna hira, su hauwa da Fatima suna gefe rike da pakhryya suna mata wasa ita kuwa sai faman wage baki takeyi”.
Nan bakura ya kara tambayar umma asalin abinda yasa zynah tabar gida” Umma bata boye masa komai ba, hatta sanadiyar barinta gidan malam shehu, tayi tana kuka, zynah dake zaune itama kukan takeyi, bakura ya tausaya masu matuka”.
Shima bakura be boye mata komai ba, akan aurensa da zynah” *shi ciki ba’a yisa dan cin tuwo kawai ba, hakan yasa bakura be faďi wa umma abubuwan da suka faru dashi kafin aure ba”*
Su hauwa da Fatima umna tasa suka gyara wa bakura ďakin dake zaune, zynah ta kara gyara masa, duk ta feshe dakin da turare”.
Gani 11:PM yayi yasa umma cewa yaje ya kwanta, sabida gajiyar hanya, ummace ta fara mikewa, sannan bakura ya mike, gani zynah dake zaune bata mike ba, umma tace tashi kije ku kwanta mana, wani irin kunyane zynah taji, domin taji maganar yayi mata wani banbanrakwaiiii” Babu yadda zatayi dole yasa ta mike, shi kuwa bakura jin haka dariya yayi haďe da yi mata gwalo”.
Dole yasa ta mike suka nufi ďakin, yana jawota yayi suka faďa katifa, yana mata dariya, da cewa wato dan kinga umma shi ne kika guduna ko? To ai ba kekadai ce da umman ba, har dani, dariya zynah tayi sannan tace nima bance nikadai ce da ita ba”.
Ohh bakura yace, haďe cewa kima ce mana, duk dariya sukasa, su daďe suna hira sannan sukayi sallama, ta tafi dakin umma, nan suka dora sabo hira, na kuka dukkansu suyi kuka na dariya kuma suyi dariya”.
Kafin gari ya waye maganar zuwa zynah duk ya karaďe gari, labari har wajan maigari, hakan yasa maigari yace yanason ganisu, tare sukaje har gun maigari, daga maigari har en’gari zuwa sukeyi ana kallon zynah, zainab ma tazo, duk da taji daďin gani er’uwanta amma kushe da hassada ya hanata da nuna jin daďin, da kuma tsoron ummata”.
Anan ne magana ya fashe, kowa yasan gaskiyan san gaskiyar zance, malam shehu ba karami kunya yaji ba, bayan su koma gida hakuri sosai ya bawa Amina, haďe da rokon ta yafe masa, Amina na kuka tace ta yafe masa”.
Gani kayan dake jikin zainab duk susha klin su koďe yasa zynah ta ďibi wasu daga cikin kayanta ya bawa zainab, ita kuma rakiya alkhairi zynah tayi mata sosai, amma besa rakiya tayi godiya ba, ita kuwa zynah da shike ba shine a gabanta ba, shi isa bai dameta ba, domin inda ta daka tata ma, da bata kalleta”.
Kwanan su zynah bakwai suka shirya zuwa abuja, bakura ya dauki karamar wayar zynah ya bawa umma, yace duk abinda take bukata ta kirasa ta sanar dashi, su hauwa da Fatima harda kukansu, itama zynah kukan takeyi, kuďi masu yawa ya bawa umma da malam shehu, itama umma ta haďa masu tsaraba sosai.
Aroud 10:AM suka dauki hanya zuwa abuja”.
Bayan tafiyarsu ne, malam shehu yaje har gidan da sadiya take, hakuri ya bata sosai, sannan yace tazo su koma gida”.
Sadiya ta tubure tace babu inda zata, babu yadda malam shehu beyi da sadiya ba, amma taki yarda su koma, dola yasa ya hakura ya tafi”.
Yana shiga gida kai tsaye ďakin rakiya ya nufa,yana sallama ko amsa masa batayi ba, banza dashi tayi, hakan yasa malam shehu yana shiga ya hauta da faďi, itama da shike a jirace dashi take, nan ta kama, yana faďi tana faďin, da shike yasan hslin rakiya sarai da iya tijara da rashin mutumci, gani yadda take daga murya, yasa ya fita a ďakin sabida kada makwabta suji”.
Yana fita tace, banza da kadawo kaga aiki da cikawa”….
_*kuyi hakuri da wannan, yau da gobe ne, mesa a mari amarya????????*_
_Ina gani kamar labarinmu yazo karke insha Allahu. Sannan kuma juma’a asabar lahadi, ba lalla ne nayi posting coz ranaku inada lecture kodama zaku samu gaskiya ba zaiyi yawa ba, ina fatan zaku fahimceni ngd_
*mmn uswan ce????✍*
????????????????
_*ZYNAH!!!*_
????????????????
*WRITTEN ✍ BY MMN USWAN*
_______________
©©©©©©
_*follow me on*_
_*wattpad:Hauwa s zaria*_
_*Facebook group*_
_*Mmn Uswan*_
https://www.facebook.com/groups/157572201857733/
➿➿➿➿➿➿
_*BISLLAHI RAHAMANI RAHIM*_
_*In the name of Allah, The Beneficent, the Merciful*_
_*Fatan alkhairi gareku, bazan mance da kuba, ubangijin Allah ya amitarmin daku*_
_(Anty Rukky-mmn Abdul jalal) (Sis maryam L.I) (Rahma Muhmmed nalele) (Zainab bugaje) (Anty Haleema Auwal) (Anty Maimounath O.G) (Bilyn Abdull ce) (Zainab Shu’aibu) (my doter jamila janaf) (Aufana) (Umme Abieda) (mmn ahamed-Mardiya ko’ije) (chibado Muhmmed) (Real mai dambu ce) Rahma Abdullahi) (fasma niger) (Sis narja’atu) (Rahina m Abubakar er’garinmu) (Hafsat Ibrahim, anty sisi) (my name sake hawwa,Real smsher)kai dama wanda bansamu damar ambata ba, duk kuna raina, Alkhairi Allah ya gaida min ku, sann kuma ya biya mana bukatunmu na Alkhairi Ameen_
????4⃣0⃣-4⃣5⃣
Malam shehu yana fita, zuwa yayi gun liman da wani kani baban sadiya, ranar wanka ba’a boyan cibi, ko kafin malam shehu ya isa garesa, labari duk ya karaďa gari, hakan yasa malam shehu be boye masu komai ba, ya zare gaskiyan zance ya faďi maki”.