ZYNAH Hausa Novel

Duk da su san bai kyauta ba, amma babu yadda za’ayi su goyawa sadiya baya ta kashe aure, sabida aure ba abin wasa ba, Allah da kansa ya halarta saki amma kuma bayaso yita, idan ba ya zama dole ba”.
Tare suka je gidan sadiya, shinfiďa ta kawo masu, bayan su zauna, suka gaisa, sannan suka faďi mata abinda ke tafe dasu”.
Shiruuuuuu, sadiya tayi tana sauraransu har suka kare, sannan tace dasu suyi hakuri, ita kam yanzu ta hakura da auren malam shehu, amma idan yanada ra’ayin kwashe yaransa ga sunan bata hanasa ba”.
Su liman suyi iya kokarinsu,amma taki, hakan yasa dole ya hakara, maganar yara kuma yace su zauna a gun ummansu zaifi masu kwanciyar hankali”.
Malam shehu bai so haka ba, dan dai kawai bashida yadda zaiyi da ita ne”.
_*To malam shehu, dama haka rayuwa take, kuma dama shi mai hakuri bai iya fushi ba, idan aka kuresa Allah ya kyauta*_
~~~~ ~~~~~ ~~~~~
_*JABI ABUJA*_
Su zynah basu isa gida ba sai gab da magrib, kai tsaya gidansu suka nufa, bayan su shiga gida, zynah ta haďa masa ruwan wanka, kafin ya fito ta shiga kitchen indomie da kwai ta ďora masa, sabida shine kawai abicin da yafi saukin dahuwa, kafin ya fito har ya nuna, juyewa tayi a plate ta kawo masa bedroom ta ije a gefe”.
Zama tayi tana jiransa ya fito, sannan ta shiga tayi nata wankan da alwala, domin a lokacin pakhryya tana bacci, yana fitowa da sauri ta mike saida ta shinfida pakhryya ďan karamin table ďin dake tsakiyar ďaki ta bashi ya zauna, sannan ta dauko towel tana goge masa jiki”.
Murmushi kawai yayi me dauke da nuna jin daďin abinda takeyi masa, bayan ta gama goge masa ne, gani lokacin zafi ne yasa batayi tunani shafa masa mai ba, short nicker ďinsa ya daika yasa, sannan yace zynah ta dauko masa jallabiyarsa, yana sawa ya fara sallah” Lokacin ne ita kuma ta shiga toilet tayi nata wankan da alwala”.
Bakura yana idar da sallah daukar abincinsa yayi yaci gaba da ci, lokacin ita kuma zynah fito daga wankan sallah takeyi, duk suna gamawa tace zaka tafi kenan ko?”
Bai amsa mata ba, wayarsa ya dauko ya lalubo number ta ya fara kira, lokacin adyra na zauna tana kallo wayar amma bata daga ba, bakura yayi kira har ya gaji amma taki dagawa, saima wani tsaki tayi ta juya wa wayar baya, bakura na gani haka, ya kashe wayar bai sake bi ta kanta ba, mikewa yayi ya cire jallabiyar dake jikinsa ya haye gado ya kwanta”.
Zynah taso ta masa magana,amma kuma sai ta fasa, bayan ta gamawa pakhryya wanka haďe da bata kunu, kwanciya tayi, duk da gajiyar da suka kwaso amma bai hana zynah faranta wa mijinta ba, domin sai da yaji ya kai geji ďan kansa sannan suka kwanta”.
Da safe kuwa bayan ya shirya, dai-dai lokacin zynah ta kare wa pakhryya shiri, daukarta yayi suka nufi gidan su hjy, da sallama ya shiga, Am’abuwa dake zaune da sauri ta mike tazo ta amshi pakhryya, amma a yau pakhryya kin zuwa tayi, babu yadda Am’abuwa batayi ba amma taki zuwa,dariya kawai Am’abuwa tayi sannan suka karisa cikin falon, Bakura yana zauna pakhryya ta kafa wa hjy ido tana kallonta, dukawa bakura yayi har kasa ya gaida hjy, duk a lokacin pakhryya na kallon hjy, gani haka yasa Am’abuwa ta mike ta fisgi pakhryya da karfi daga hannu bakura, ba tare da hjy ta ankara ba ji kawai tayi an dora mata yarinya a jiki”.
Da sauri hjy tasa hannu zata cire pakhryya daga jikinta, take pakhryya tasa kuka, haďe da rikewa hjy wiyar riga da karfi tana kuka, duk da kukan da takeyi besa hjy ta kyaleta ba, da karfi ta cire wa pakhryya hannu a wiyarta har zata hurgata kenan, ihuuuuuu pakhryya tasa, taci gaba da rike hjy, dole yasa hjy ta kyaleta a jikinta amma baďan taso ba”.
Hjy na kyaleta taci gaba da wasa, tana tsotse wa hjy yatsutsin hannunta”.
Daga bakura har Am’abuwa suna haďa ido murmushi sukayi, gani haka yasa bakura mikewa zuwa gidan Adyra, yana isa tun daga bakin kofa ya fara sallama, lokacin adyra na kitchen tana haďa jin sallama yasa ta leko gani bakura ne tsaki tayi sannan ta koma kitchen ďin”.
Bakura beyi fushi ba, binta yayi zuwa kitchen ďin, yana shiga ya rungumeta ta baya, yana faďin oyoyo my wife, kucu-kucu adyra keyi tana kokarin kwance jikinta, gani yariga yayi mata riko da bazata iya kwancewa ba, yasa ta ha’u zaginsa, ta uwa ta uba, haďe da cewa ya koma inda ya fito, mugu azalumi, ďan wuta kawai”.
Duk da yaji zafin zaginsa da tayi masa amma be nuna mata ba, dariya kawai yayi mata, haďe da cewa, dama haka rayuwa take idan wani na kinka da kwana, wani kuma da shekara yake sonka”.
Oh!! dai adyra tace”
Juyawa yayi ya fita, batare da ya sake tanka mata ba”.
_To en’uwa na mata, shifa namiji mai mata biyu ba’a masa haka, domin a lokacin da kika bata masa er’uwanki zata faranta masa, amfani gida biyu kenan, magani gobara._
Yana fita gidan zynah ya sake komawa, yana zuwa kwanciya yayi, yayi baccinsa” Bai tashi ba sai bayan 12:PM saida ya sake wanka yayi sallah yaci abinci sannan ya leka kasuwa.
Pakhryya kuwa ba’a medata ba,sai bayan la’asar, shima bakura yana tashi daga kasuwa gidan zynah ya sake dawowa, tun daga sannan be sake komawa gidan adyra ba”.
Tun daga lokacin bakura be sake komawa gidan adyra ba, kuma be sake kiranta ba, gaba daya ya haďa ta ya bawa banza ijiyarta”.
Data gaji da zama gani bazata iya jure hakan ba, shiryawa tayi zuwa gidan hjy, da kuka ta isa gidan, gani ta shigo ba kuka ne, yasa hjy mikewa daga inda take zaune, a gigice ta tareta da lafiya meke faruwa?”
Cikin kuka take magana, gani haka yasa hjy ta kamota ta zauna, saida ta numfasa sannan hjy ta sake tambyrta, nan take cewa, hjy rabon bakura da gidan ta sati daya kenan, kuma koda ta kirasa a waya baya dagawa”.
Nan take hjy ta dauki wayarta domin kiran haka, tayi kira yakai sau biyat amma ba’a daga ba, gani haka yasa hjy ta bawa adyra hakuri tace ta koma inda, in sha Allahu zatasan abin yi, har da daukar kuďi tayi mata masu yawa, dasu turare, sannan sukayi sallama”.
Adyra na fita hjy ta dauki mayafi zuwa gidan zynah, ashe koda take kiran bakura yana gida, yazo cin abincin rana, Allah ya taimakesa ta baya yabi, hjy na isa gidan kai tsaye ta shiga da sallama, jin saallamar hjy ne yasa zynah ta fito da sauri, har kasa ta duka tana gaida hjy”.
Hjy dake tsaye
bata amsa ba”.
Ina bakura?”.
Yana kasuwa, dama haka bakura yace ta faďi wa hjy koda ta tambayesa”.
Nan ta hau zagin zynah, inda take shiga ba man take fita ba, har da cewa karuwa mara asali,duk da maganar yayi wa zynah zafi amma sai ta matse bata nuna mata ba, sai faman bawa hjy hakuri takeyi”.
Duk da haka hjy bata daina aibanta tata ba, saida ta gaji ďan kanta sannan ta fita”.
Hjy na fita, da sauri bakura ya fito, hannu yasa ya dago zynah dake duke, juyota yayi har ya buďe baki zai fara magana”……….
Da sauri zynah tasa hannu ta rufe masa baki tana masa murmushi, duk yadda yaso yayi magana, amma zynah ta hanasa”.
Da yamma lokacin ya tashi daga kasuwa biyowa yayi gidan hjy, bayan su gaisa, hjy take tambayrsa dalilin da yasa baya kwana a gidan adyra, kuma gashi koda ta kiraka baka dagawa”.
Nan bakura ya kwashe komai ya sanar wa hjy,amma duk da haka hjy bata amince ba, faďa tayi masa sosai sannan tace daga nan ya wuce gidan adyra, kuma idan ya biya gidan zynah kafin yaje bata yafe masa ba”.