ZYNAH Hausa Novel

Himm kawai yace, yana fita kamar yadda hjy tace haka bakura yayi, saodai kiran zynah yayi ta waya ya sanar mata, bata nuna bacin ranta ba, babu komai kawai tace masa”
Yana shiga dai-dai lokacin tana fitowa daga wanka, ko kallonsa batayi ba, saida ta shafa abinda zata shafa sannan ta dauki kayan baccnita tasa, Bakura dake tsaye murmushi kawai yayi, haďe da cewa ni wlhy Ni’eemat kina bani mamaki, ke kullum bazaki canza ba? taran mijin ma baki iya ba?”..
Ko zaka koya min ne?”
Me zai hana, idan na koya wa matata yadda ake tarban miji a tawa gani ai ba abin kunya nayi ba”.
Suna haďa ido, wani irin uwar harara ta harbesa dashi haďe da hayaewa gadon”.
Da sauri bakura ya bita kan gadon, haďe da kamota, yana faďi tashi ki kawowa mijinki abinci yaci”.
Buďe bakin adyra tace, nima a bincine kazo ka cini”..
Da gaske?”
Kai fa kasani”.
Kafin ta juya tuni bakura ya hayeta,adyra tayi kokarin turesa amma ta kasa, bakura be sauka na har saida yakai geji, sannan ya sauka yana yi mata dariya”.
Adyra kuwa, baki be mutu ba, kusan kwana tayi tana zaginsa, da safe ma haka, bakura bebi ta kanta ba, tashi yayi yaje ya shirya, yana gamawa yaje ya haďa tea, falo ya dawo ta zauna yana sha, adyra na fitowa suna haďe ido, cikin jin haushi tace oh!! An dai ji haushi”.
Mudai ji haushi, domin na tabbata bani kadai naji haushin ba, au na mance bance maki yaya gajiyar jiya ba, ko za’a bani na kara ne?”.
Dariya ya kwashe mata dashi, jin haushin hakan yasa adyra inda take shiga banan take fita ba”.
Ashe duk abinda takeyi hjy na bakin kofa tana jinsu, jin zagin yayi yawa ne, ita kuma nazata iya jure jin hakan ba,da sauri ta juya ta koma da baya”.
Tunda hjy ta koma gidan irin maganganun da adyra ke faďi wa bakura ya dami hjy, yadda abin ya dameta ji tayi kamar ta kira hjy Ashe ta sanar da ita, sai dai kuma idan tayi haka tamkar da tona wa kanta asirine, dole yasa ta bar maganar a zuciyarta yaci gaba da cikinta, domin ko daddy taki faďi mawa,abinda sufi kusa da adyra akan daddy”.
Shi kuwa bakura, al’amarin adyra ya daina damusa, domin idan da sabo yariga daya saba”Shiyasa yanzu idan ya shigo gida in har be takareta suyi faďa ba, bayajin daďi”.
Cikin satin nan daddy zai dawo, sabida zasuje gida maiduguri, shida bakura, akan maganar auren su am’abywa da Yah-na, gakan yasa daddy yace wa bakura ya shirya yana isowa zasu tafi gida”.
Tunda adyra taji labarin tafiya gida, tun daga lokacin ta fara lallabarsa, sabida tanason zuwa gida”.
Da shike bakura ya gano, duk yadda tabi haka shima yake binta, da haka har daddy ya dawo, ranar tafiyarsu yayi, zynah ce kawai ya sallama amma banda adyra, har suka isa, gani yamma yayi be dawo gida wayarta ta dauko ta kirasa, bakura yana daga, saida suka gaisa, haďe da tambyarsa ya kasuwa, a lokacin ne yake sanar da ita yana maiduguri, take tasa ihu haďe da hurgi da wayar””””..
~~~~ ~~~~~
*kunci*
Tun bayan komawar su zynah abuja zazzabin malam shehu ya tashi, da haka har ya kaisa ga kwanciya”.
Bayan kwana uku da kwanciyarsa cikin dare ciwo yayi zafi, malam shehu yayi murkusu-murkusu har rai yayi halinsa,shiruuuu da rakiya taji ne har karfe takwas na safe malam shehu bai fito ba, yasa taje dubashi, tun kafin ta karisa bakin fokar take kwaďa masa uwar kora, amma shiru, hakan ne yasa ta karasa ďakin da sauri”.
Tana shiga ganinsa tayi yayi wani irin kwanciya, take gabanta yayi mummunar faďuwa, da sauri tayi kansa, koda tabasa shiru tayi,take tasa wani irin ihuuuu tana faďin na shiga uku na lalace”.
“,Abinka da kauye, take gida ya cika da jama’a har da sadiya da yaranta duk suzo, ba’a dauki lokaci ba aka yiwa malam shehu wanka aka shiryasa kamar yadda addinin musulinci yace ayi, bayan an kaisa ne, sadiya ta kira Bakura ta sanar dashi rasuwar malam shehu, salati yayi ya sanar wa ubangiji, sannan yace insha Allahu suna nan zuwa”.
Bayan su gama waya da sadiya ne yaje ya sanar wa daddy, washe gari bayan en’gidan mazajen su Am’abuwa da Yah-na suka neman aurensu, kuma aka basu, haďe da sanya masu rana, washe gari suka baro maiduguri zuwa abuja”.
Bayan su iso ne, daddy yasa bakura yaje yazo da zynah, saida yayi mata nasiha sosai sannan ya sanar da ita rasuwar malam shehu”.
Itama salati tayi, sannan yayi addu’ar Allah ya jikansa, daddy yace ta shirya gobe sanmako zasuyi”.
Bayan fitar su, hjy ke tambayar daddy, a cewarta bata fahimci maganar da sukeyi ba”.
Nan daddy ya sake faďi mata, daga nan yace ta shirya suje tare””..
Da sauri tace, wahhhhh!!
Allah ya kiyaye, saidai wata ba niba, gani daddy ya matsa ne ta amince zata”.
Bayan su koma gida bakura yaje gidan adyra, tana zaune a bakin gado, bakura na sallama bata amsa masa ba, gani haka yasa be biye tata ba, shima zauna , nan yake sanar da ita rasuwar malam shehu baban zynah”.
Tamkar bada ita yake magana ba, yana gama faďi ya mike haďe da sallamarta, domin tafiyar asuba ce zasuyi”.
Tsaki kawai tayi masa, ba tare da tace komai ba, har bakura yakai bakin kofar fita falo, da sauri adyra ta mike da cewa yanzu sabida Allah kayimin adalci kenan? Kwananka nawa baka gari kuma yau da dawowarka kace zaka sake wani tafiya? To nan dai gaskiya bazan yarda ba sai dai kasan abinyi”.
Murmushi bakura yayi sannan yace, to yanzu me kikeso ayi?”
Sai dai ka fasa tafiyar”.
Shi kawai kike so?”.
Eh”.
To kinga yanzu kinsan abinda za’ayi?”
Sai ka faďi”.
Bari naje na dawo, domin yanzu daddy yana jirana akwai wani maganar da zamuyi dashi ne”.
Duk da zuciyarta yana faďi mata, ba gaskiya bakura ya faďi mata ba, amma tace to saika dawo”.
Da ido ta bisa dashi har ya fita daga gidan”.
Bakura na fita ya kwashe da dariya, haďe da cewa sha-sha-sha”.
Tunda bakura ya shita adyra ta zauna zaman jiransa, shiru-shiru be dawo ba, wayarta ta dauko ta fara kiransa, lokacin bakura na tare da zynah suna shirya kaya, duk uban kiran da Adyra keyi yana gani amma be ďaga ba”.
Gani tayi kira har ta gaji, be ďaga dole yasa ta hakura da kiran, sannan taje ta rufe gida”.
Bayan sallar asuba, duk suka shirya, aroud 7:AM suka dauki hanyanr kano, bakura da zynah mota ďaya hjy da daddy sai driving suma mota ďaya”.
Da safe ma haka, zuba ido adyra tayi rana jiran shigowar bakura amma taji shiri, daga nan ta hau fushi bata sake tunanin kiransa ba kuma”.
Su daddy basu isa garin kunci ba sai bayan la’asar, kai tsaye gidan su zynah suka nufa, gani sune yasa en’zaman makoki duk suka zuba ido, da son gani suwaye a motar”.
Da shi motar su bakura ne a gaba, yasa shida zynah suka fara fitowa, sannan su daddy da hjy, duk en’zaman makokin sukabi su da ido suna kallonsu, galala, kamar basu taba gani mota a rasuwar suba, daga kiman har maigari duk suka mike suka yo kansu, da sannu da zuwa”.
Hjy na fitowa daga mota, ba tare da daddy ya gani ba, yawun dake bakinta ta tsarďan dashi, haďe da jan tsaki, zynah na kallonta da sauri ta dauke kansa tayi kamar bata gani ba suka nufi cikin gida”.
Zynah ce a gaba, hjy kuma a baya, tana tafe tana aibanta gidan, da haka har suka isa ciki, duk matan dake zaune jin sallama yasa suka juyo kansu, gani haka yasa hjy ta kara tsuke fuska ksmar tanajin warinsu, abinda ta mutumin kauye sai faman yake baki sukeyi suna kallon zynah da hjy”.