HAUSA NOVELZYNAH Hausa Novel

ZYNAH Hausa Novel

Har ďakin ummata zynah ta kai hjy, duk da ďaki babu laifi, domin a share yake tsaf babu datti, kuma ga ledar kasa daya rufe ko’ina, amma hakan bewa hjy ba, domin kin zama tayi a kasa, gani hakan yasa sadiya cewa ta zauna a bakin katifa”.

Nan sadiya ce ta fara gaida hjy, bayan su gaisa, matan dake waje, da gulma suka kara shigowa suna gaida hjy, amma dan tsabar rashin mutunci iri na hjy, ko kallo basu isheta ba, sadiya ce take amsa masu sai kuma zynah”.

Nan labari ya kai kunni rakiya, jin haka yasa rakiya cewa basai naje ba balle suyi min kallo banza?”

Ruwan swan sadiya tasa aka siyo masu, dasu juice amma duk ba mai sanyi bane, sabida garin babu wata, mutum daya ne yake kunna genarato, a ranar kuma baya nan yaje cikin kano siyayya,  koda aka kawo saida ta ďibawa su bakura da daddy nasu sanna aka bawa hjy nata, kaďan kawai hjy tasha sannan tace zatayi sallah”.

Da sauri zynah taje ta zuba mata ruwa a buta, sannan tazo ta sanar wa hjy, to kawai hjy tace, tana mikewa ruwan swan ďin da sadiya ta siye mata tashi dashi tayi alwala sannan tazo ta fara sallah”.

Nan take sadiya ta fito da kuďi ta aiki wata kanwarta kasuwa tayo mata cefane, hjy na idarwa sadiya tace zynah ta rakata ďakin rakiya su gaisa”.

Zynah ce ke daga hjy na biye da ita, da takalmi hjy ta shiga ďakin rakiya, duk da mutuwar da akayi wa rakiya, amma besa ta daina masifa ba, suna haďa ido da hjy tun daga sama har kasa ta ďibi hjy dashi sannan ta zubar”.

Hjy dake tsaye tace sannunku”.
Buďe bakin rakiya tace, kema sannunki”.

Tun daga sannan rakiya bata sake magana ba, matan dake zaune a ďakin rakiya ne suka amsa wa hjy, daya daga cikin matan tace hjy ga gun zama”..

Da sauri hjy ta dauki mayafinta ta rufe hancinta dashi, sannan tace ina gun zaman yake?”

Jin haka da shike rakiya ta fahimci abinda hjy ke nufi, tsaki tayi, haďe da cewa aikin banza, ni za’a kawo wa rainin hankali?”.

Ba tare da hjy ta tsaya jin abinda rakiya zata ceba ta fita daga ďakin”.

Koda aka gama abinci a ka bawa hjy, kin ci tayi, biscuit da juice hjy ta dauko daga handbag ďinta taci ta kwanta” kafin hjy ta kwanta saida ta feshe ďakin da turare, gani sadiya zata ruwa ďakin da sauri hjy tace a’a bata yarda ba, sabida bazata iya kwanciya a ďaki irin wannan kuma a rufe kofa ba”.

Sadiya bata nuna damuwar ta ba, haka ta tashi ta buďe kofar,a lokacin ran zynah ya baci sosai sabida tunda suka shiga ďaki hjy take masu wani irin kallo na raini, gashi kuma duk kokarin da sadiya keyi a kanta bata gani”.

Washe gari kuwa babu yadda ba’a da hjy ba tayi wanka amma taki, a cewarta bazata iya amfani da ruwan garin ba” nan  hjy ta tsama sai dai su tafi, daddy beki ba, sabida shima akan hanya yake, daddy kuďi masu yawa ya bawa sadiya da rakiya, shima maigari da liman ba’a barsu a baya ba, alkhairi yayi masu sosai, kafin su tashi saida sukayi masa addu’a sannan su daddy suka dauki hanya shida hjy, bakura kuwa yace tare zasu dawo da zynah”.

Bayan anyi addu’ar uku ne, bakura ya shigo har ďakin umma, hira sukayi sosai, nan ya tambayi umma abinda take bukata, duk da umma najin kunyar bakura, amma babu yadda zatayi,sabida yadda bakura keyi mata kamar wanda ya daďe  da saninta, nan umma ta faďi masa, bakura da zynah suka shiga kasuwa siyayya sosai sukayo sannan suka dawo, bayan an kawo kayan cikin gida ne zynah tace a dauki buhu daya na shinkafa a bawa rakiya”.

Shidai matsiyaci ko a tandun mai aka sashi fitowa yakeyi tarmasasau, koda  aka kai mata shinkafar dake tasa aka dawo dashi haďe da kuďin ta daddy ya bata, a cewarta ita ba matsiyaciya bace”.

Har umma ta mike zataje, bakura da zynah suka hanata zuwa, dole yasa ta hakira”.

Sati su bakura da zynah bakwai suka suma abuja”.

~~~~   ~~~~  ~~~~

*ABUJA*

Su zynah basu iso gida ba sai dare, sabida basu tashi a wuri ba, hakan yasa beje gidan su hjy ba, bayan suyi sallah sukaci abinci zasuci kwanciyarsu sukayi”.

Da safe bayan suyi wanka su shirya, bakura yace suje su gaida daddy da hjy da gajiyar hanya, haka suka nufi gidan hjy”.

Bakura ke dauke da pakhryya har suka isa, da sallama suka shiga, lokacin daddy na falo shida su Am’abuwa da Yah-na suna hira, hjy kuma tana ciki, har kasa suka duka suka gaida daddy, shima da fara’arsa ya amsa masu, haďe da sanya hannu ya amshi pakhryya, nan suka gaisa dasu Yah-na da Am’abuwa, suka kara gaisheta da hakuri”.

Duk hiran da sukeyi da bakura bata sanya masu baki ba, saida ta jima sannan ta mike ta sallamesu ta koma gida, nan tabar pakhryya shima bakura be daďi ba ya nufi gidan adyra, pakhryya na wasa ta zame ta sauka kasa, tana wasa, da haka har ta rarrafa ta shiga ďakin hjy, lokacin kallo ya dauke wa su Yah-na da Am’abuwa hankali”.

Hjy dake bacc ji kawai tayi ana shafe mata kafa, da sauri ta buďe ido, tana buďe ido pakhryya ta gani tana tsaye rike da kafar hjy tana mata dariya, tsaki kawai hjy tayi sannan ta koma ta kwanta”.

Duk da haka bata daddara ba, cigaba da jawa hjy kafa tayi, gani haka yasa hjy ta dauke kafarta daga gun, da yake pakhryya me kiriniyane, take side dorower tayi ta haye kan gadon, hannu tasa tana jawa hjy dankwallin dake kanta”.

Cikin jin haushi hjy ta zuba wa pakhryya mari, a gigice tasa kuka, gani yadda tasa kuka ne, sai hjy taji babu daďi a ranta, nan ta dauketa tana lallashinta har tayi shiri”.

Nan sukaci gaba da kwanciya
Gani pakhryya bata da niyyar bacc yasa hjy sauka daga gadon ta fito falo, su Yah-na da Am’abuwa suna gani pakhryya a hannu hjy, duk haďa ido sukayi suna kallo juna batare da suce komai ba”.

Hjy na zuwa ta mika wa Yah-na pakhryya sannan ta koma ta zauna kusa da daddy, suna cikin hira pakhryya ta sake komowa gun hjy, tun daga lokacin duk ranar da bakura ya kawo pakhryya, bata cika yarda da kowa ba idan ba hjy ba, duk yadda hjy takai ga kin daukarta dole ta hakuri, yanzu kam duk ranar da ba’a kawo pakhryya har wani iri takeji, kodan sabida gyaran da take mata a ďaki”.

Yau da gobe ya wici wasan yaro, idan da sake bakura ya saba da halin adyra, musamman ma bikin su Yah-na da Am’abuwa daga gabato, domin yanzu be vika zata a kasuwa ba, abinda gyaran yayyunsa da yakeyi”.

Kusan kullum yana gidan hjy, idan yazo da safe baya komawa sai dare, idan ranar da yake gidan adyra ne kafin magrib yake tafiya, idan kuma gidan zynah ce, har bayan isha yake kaiwa, sabida yasan ita ďin mai fahimtane”.

Da lokaci yayi bakura yaso tafiya maiduguri da zynah, amma hjy tace bata amince ba, sai dai yaje da adyra, tunda ana daura aure zasu dawo nan abuja ne, tayi hakuri idan suzo abuja sai taje taga gida”.

Duk da beso haka ba, amma ya ďanne bai nuna mata ba, sai yasan ta bata masa show nasa, sabida gaba daya da ita yayi niyyar tafiya, hakan yasa ya gyarata sosai, sabida kada suje a raina mata wayo, to amma yaya zaiyi, tunda umace”.

Koda bakura ya faďi wa zynah, duk da bataji dadi ba,amma yaya zatayi, dole ta hakura, tun ana saura sati suka kwashi jiki zuwa maiduguri dukkkansu, babu wanda aka bari a abuja sai zynah kawai, duk abinda suke ciki daddy be saini ba, sabida ya rigasu tafiya”.

Bayan su bakura su tafi ne,zynah tayi kuka sosai, tunda suka isa aka fara wasa, har zuwa ranar daurin aure, ko wani prgrm da za’ayi tare suke zuwa da adyra, abu gwani sha’awa tankar basu faďi a tsakaninsu”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button