HAUSA NOVELZYNAH Hausa Novel

ZYNAH Hausa Novel

Biki yayi biki kuďin da aka kashe faďinsa bata lokaci ne, bayan kwana biyu da biki duk suka dawo abuja, ya rage amare da angwayensu, suma ranar da suka ciki sati duk dawo abuja, washe gari kowa ya dauki matarsa zuwa kasashen waje cin amarcinsu”.

Anan gun bikin ne, malah yaga yarinya yace yanaso, bayan dawowarsu abuja ya sanar wa hjy Ashe, hjy Ashe batayi kasa a gwiwa ba ta sanar wa alhj maigidanta”.

Sali hali yafi sani kama, hakan yasa basuyi kasa a gwiwa ba suka tafi nema masa aure, nan take aka basu, haďe da sanya masu rana,.

Tun daga ranan bakura yasha alwashin wannan tafiyar da zynah za’ayi da shike ba lokaci me tsayi suka saba, nan hjy khursum da hjy Ashe suka shiga shiri, kwana hudu ya rage biki suka tafi maiduguri, duk yadda bakura yaso tafiya da zynah wannan karonma haka hjy ta hana, a cewarta sai dai ya tafi da adyra idan yanaso yaje ta matarsa ne, idan kuma ba zaije da ita ba, to kuwa sai dai kuwa ya huta, jin hakan yace duk su zauna ba zaije da kowa daga cikin ba”.

Duk da haka hjy baya yarda ba, duk inda bakura zai shiaga idon hjy nakai, ko zatagansa da zynah, ranar da aka daura aure ita da ďangin su Ashe suka dauko amarya zuwa abuja, shima bakura da malah motarsu na bayan nasu hjy”.

Biki kam ya kawatu sosai, kwana damĝin amarya da ďangin hjy Ashe uku duk suka koma gida maiduguri”.

Duk a lokacin amarya na gidan hjy, bayan tafiyarsu ne hjy Khursum ta dauki amarya zuwa gidan mijinta, *gwarinfa L.I.D. STREET* hjy ta jima tana masu nasiha sannan sukai sallama, shima bakura be daďe ba yayi sallama”.

Tun bayan biki hjy take zazzbi, amma a lokacin an dauka cikine, hakan yasa babu wanda ya damu, bayan kwana biyu, gani jikin nata babu daďi yasa bakura cewa zynah tana gama aiki tazo gidan hjy ta rika dubata, sabida yanzu gida babu komai”.

Idan zynah taje yau, gobe kuma sai Adyra taje, amma ita bai faďi mata ba, sabida ba a gidanta ya kwana ba”.

Zynah bata kiba, yadda bakura yace haka takeyi masa, ranar data fara zuwa, lokacin hjy na ďaki kwance, hakan yasa suka shiga har cikin bedroom”.

Bayan su gaisa bakura yace hjy ga zynah tazo tayaki zama, koda kina bukatar wani abu, take hjy tace bata bukatar komai sabida haka ta fita mata a gida, idan ba haka ba wlhy zata mata Allah ya isa”..

*kai jama’a kuji fa, koda hjy Khursum ke faďin haka, pakhryya na zaune kusa ta mirrow tana wasa. Wannan wani irin bakin haline dan Allah?”*

Jin haka yasa bakura cewa zynah ta tashi ta tafi gida kawai, zynah tasa hannu zata dauki pakhryya, kuka tasa tana zullo, akan bazata ba”.

Jin kukanta hjy tace idan kin san bada gidanku kikazo da ita to ina bukata ki ijeta”.

A sanyaye ta cire hannu daga jikin pakhryya ta fita, zuwa gida”.

Zynah na fita hjy tace wa bakura ya kira mata adyra tazo, bakura be musa ba, nan ya dauki wayarsa ya fara kiran adyra, ashe koda bakura ke kira tana zaune tana kallon wayat amma da batayi niyya ba, hakan yasan ta zuba wa wayar ido”.

Bakura yayi kira har ya gaji da kira,bata gana ba, hjy tace yadai sake kira wata kila bata kusa da wayarne”.

A kira na biyu shine adyra ta daga wayar haďe da sallama, bayan su gaisa ne bakura yake sanar mata hjy ce ba lafiya, kuma tace tazo sabida ita kadai ce a gida, koda tasamu abokiyar hira”.

To kawai tace,ganinan zuwa”.
Hjy da murnanta, bakura yace bari naje na dawo kafin tazo”.

To hjy tace, tunda bakura ya fita, hjy kesa idon adyra amma shiru, gani har azahar yayi bata zoba yasa hjy daukar waya ta kira ta”.

Adyra na kallo taki daga wa, ringing ďin wayar na tsikewa adyra tace, bazan zoba, haka kawai nazo ki addabeni da masifa”.

Bakura be dawo gidan hjy ba sai bayan la’asar, yana zuwa hjy tasa masa kuka, gani haka yasa hankalin bakura ya tashi, da sauri yaje kusa da ita yana tambayarta meke damuta”.

Tace kai ne ke mata ciwo, kamar zai rabe biyu”.

To kin sha magani?”
Eh nasha amma har yanzu be sauka ba, gashi gaba daya jikina yayi min nayi kamar ba tawa ba”.

Ina Ni’,eemat ďin?”
Bata zo ba”…
Bata zo? Kamar yaya?”
Shiru hjy tayi”.

Nan take ya dauki waya zai kirata, hjy ta hanasa”.

Dole bakura ya hakura da kiran adyra, nan ya zauna yaci gaba da kulawa da hjy”.

Gani har dare yayi be dawo gida ba, yasa zynah ta kirasa tambayesa yana ina?”

Gidan hjy ya faďi mata”.
To kodai nazo ne?”
Aa ki bari kawai, da safe zan shigo”.

To Allah ya kaimu, kuma ya bata lafiya”.

Ameen ngd yace,sannan sukayi sallama”.

Tun daga lokacin bakura be sake kiran adyra ba, itama bata nemesa na” yanzu ko gidan zynah baya zuwa, yana kusa da hjy, gani jikin nata kamar yayi zafi yasa bakura daukarta zuwa ssibiti, yana zuwa aka basu gado”.

Acewar Dr jininta ne ya hau sosai, duk da suna iya kokarinsu a kanta amma ciwo kullum sai karuwa yakeyi, bakura ke kwana da ita, babu yadda zynah batayi ba,akan ya barta ta rinka kwana da hjy, amma yaki, ita kuwa goge batama kira ba balle tasan halin da ace ciki”.

Ranar da hjy ta cika kwana uku a asibiti, suka tashi babu hannu babu kafa, bakinta ya koma gefe, tun cikin dare likitoci sukai cannn a akan amma sai a hankali, bakura kuwa idan ba kuka babu abinda yakeyi”.

Nan ya sanar wa daddy halin da ake ciki, take daddy yace bakura ya dauketa zuwa egypt, jirgin karfe goma sukabi zuwa egypt, kafin su isa tuni daddy ya kammala komai, su kawai ake jira”.

Suna isa aka dauketa zuwa asibitin, nan fa Dr ya shiga dubata, saida ya gama dube duben da zaiyi sannan ya faďi wa daddy iya dadadin kuďin da zataci, dashi ke ba shine damuwar daddy ba, take ya biya su, sannan Dr yake faďi masu zata kai kamar wata biyu ana jinyarta, kuma ya kamata ta samu wani kusa da ita”.

Jin haka yasa daďi da bakura suka fara tunani wanda zaizo ya zauna da ita, gani wata kusan tafi wata kusan hakan yasa, bakura yanke shawarar tafiya dauko adyra tunda yarinyar kanwarta ce”.

Washe gari bakura ya koma gida nigeria kai tsaye gidan adyra ya nufa, tunda yana nima a garesa dole yayi hakuri da duk wani abinda zata masa”.

Tana zaune tana cika da batsewa, bakura ya dukar da kansa yace kina lafiya ya gida? Kiyi hakuri nayi tafiya ba tare dana sanar dake ba, wlhy jikin hjy ce sai a hankali yanzu haka ma tana egypt juya ta kaita”..

Da shiri tace subhllh, duk jikin ne haka?”

Eh wlhy, yanzu haka ma zuwa nayi mu tafi dare dake, sabida Dr yace zatakai wata biyu a can kuma tana bukatar wani kusa da ita”.

To Allah ya sauwake, amma ni gaskiya babu inda zani, haka kawai dan nice er’wahali shine za’a daukeni naje jinya? Ba’a kaini dan daďi ba saida wahala yazo, wlhy babu in zani”.

Yau ba masifa yakeji ba, hakan yasa shi yin shiruuuu har ta kare, sannan yace hjy ce fa, idan bataci darajan uwar mijinki ba, ai zataci darajan yayar mamaki””..

Yayan mamata kace, bafa mamata ba, sabida babu inda zani, iya kacina da ita addu’a”.

Ran bakura yayi mugun bacc, a fusace ya tashi ya fita zuwa gidan zynah” Yana shiga be tsaya ko’ina ba sai bedroom, kan gado ya haye ba tare daya tube ba,rum da ciki yayi yana kwalla, shiruuuu ta zynah taji ne yasa ta shigo bedroom ďin, gani yadda ya kwanta yasa zynah gano babu lafiya”.

Kusa dashi ta zauna, a hannnkali take masa magana, gani yadda takeyi ne yasa bakura faďi masa damuwarsa” Take tace akan dan wannan shine duk ka dami kanka? Idan har ka amince, kuma bazai zama takura a gareka ba, ni na amince zanje nayi jinyarta har lokacin da Allah zai bata sauki””..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button