ZYNAH Hausa Novel

Da sauri bakura dake kwance ya mike zaune yana faďin da gaske my zynah? ”
Kai kawai ta ďaga masa tana dariya, sabida daďi bakura besan lokacin da yayi tsalle ya jawota jikinsa ya rungume ba”..
Nan suka shiga haďa kayan tafiya, da safe jirgin safe sukabi zuwa egypt “”””””….
*mmn uswan ce????✍*
????????????????
_*ZYNAH!!!*_
????????????????
*WRITTEN ✍ BY MMN USWAN*
_______________
©©©©©©
_*follow me on*_
_*wattpad:Hauwa s zaria*_
_*Facebook group*_
_*Mmn Uswan*_
*THE????????*
https://www.facebook.com/groups/157572201857733/
➿➿➿➿➿➿
_*BISLLAHI RAHAMANI RAHIM*_
_*In the name of Allah, The Beneficent, the Merciful*_
_wannan book ďin sadaukarwa ne ga taskar ďan-hamza, a gaskiya ni nama rasa ta iya zan fara domi gaba daya banida kalmomin da zanyi amfani dasu wajan godiya a gareka,sai dai kuwa nace Allah ya saka da alkhairi, wannan litafi sadaukawa ne gareka tare da babana Abubakar sadiq namiji *1* Allah ya amintarmin dakai, yasa kafi haka, ya karemin kai ya kuma bani uwa tagari Amen_
*KORAFI*
_naji korafinka sosai akan AISHA ayi hakuri ba laifina bane, haka ta ďoro mana, amma ga kaina bisa kan wiyata, afuwan afuwan insha Allahu hakan bazai sake faruwa ba, ko ba komai nima AISHA uwa tace, kakoga ance uwa mafi uban koda uban sarki ne,ngd ngd sosai_
????4⃣5⃣-5⃣0⃣
“Bayan isar su egypt a yanayin da zynah ta gama hjy a ciki, tayi matukar tausayawa hjy, kukan ba’a magana, daga ita har Bakura babu me bawa ďan uwarsa hakuri, daddy ne yayi karfin hali ya yayi masu magana, da kuka ba shine mafita a gare ta, addu’a kawai take bukata”.
Tun daga lokacin daga zynah har bakura babu abinda sukewa hjy sai addu’a subata tasha ragowa kuma su fasha mata a jiki, likitici suma suna iya kokarinsu, amma duk da haka shiru kakeji, babu wani alamar sauki, kashi a kwance fitsari ma haka, gani haka ne aka koma yi mata amfani da pampas, na safe daban na rana daban haka ma na dare, wani lokaci ana sanya mata take batawa”.
Duk kwana biyu uku daddy ke zuwa daga germany yake dubasu, shima bakura lokaci-lokaci yake zuwa nigeria yana duba shago, da shike akwai amana,hakan yasa suke tafiyar da harkan business ďin yadda ya kamata, sai dai abinda baza’a rasa ba”.
Sati hjy biyu a egypt sannan aka sanar wasu Am’abuwa da Yah-na, ranar da aka sanar dasu, washe gari Am’abuwa ta taso daga chana zuwa egypt, ita kuwa Yah-na sai bayan kwana uku sannan tazo”.
Am’abuwa tayi kuka ba kaďan ba, tun daga lokacin ta roki maigidanta arzikin zata tsaya tayi jinyar mamanta” Da shike mai fahimta ne, bai nuna damuwa akan hakan ba”.
Saida yayi kwana uku sannan ya koma ya ya barta a gun”.
Tun daga lokacin komai tare sukeyi, hakan yasa aiki yayi wa zynah sauki, ba kamar dah ba”.
Sati Yah-na daya ta koma England wajan maigidanta, da shike shi be zoba,iitace kawai tazo”.
~~~~ ~~~~~ ~~~~
_*KUNCI*_
Tun bayan rasuwar malam shehu , zainab ta fara gani canji daga gun usman, zagi da gori kuwa abin ba’a magana, daga shi har danginsa, balle tunda asiri ya tonu kowa yasan rakiya tayi sanadiyar malam shehu ya kori Amina daga gari, hakan yasa kullum magana ya tashi tsakaninta da dangin miji basu yi masa ta wasa, yanzu haka fita unguwa niman gagaranta yakeyi, abinka da kauye gidan suna da gidan biki, idan taje basu da aiki sai habaici, wasu kuma a gabanta suke faďi mata”.
Bayan sati bati da bikin kannin usman ya tada maganar aure zaiyi, sabida shi yanaso yadda aka haifesa shi ya haifi nasa, zainab da rashin hakuri da bancewar basira, kuma dama shifa gwano bayajin warin jikinsa, zainab najin sunar yarinyar da usman keso nan ta hau masifa da bala’i tana faďin wlhy idan har ina raye baka isa ka auro karuwa wacce ta kare rabawa maza kanta a waje ba, duk garin nan babu uban da besan uwani er’iska bace”..
Dariya usman yayi haďe da cewa da gaske? Ke zainab idan kin san abinda kira kunya, ke kinada bakin da zaki buďe ki kira wata da sunan karuwa? To wlhy idan ba tonan asiri kike nema ba, nima kike nayi maki tonan asiri ba, gwama ki kama kanki da bakinki, in har kikaci gaba da aibanta min matata na lahira saiya fiki jin dadi”.
Banza er’iska er’mai mugun hali kawai, duk garin nan babu wanda besan mugun halin uwarki rakiya ba”.
Baďe bakin zainab tace badai uwata ba wlhy”””…..
Kafin ta rufe baki tuni usman ya dauketa da mari haďe da shaka, yana faďin sai uwarwa? Ehhh ko nace sai uwarwa?”
Shiruuuuuu tayi sabida shakan da yayi mata yasa ta kasa magana, usman yaci gaba da cewa babu mamaki zaman gidan ne kika gaji dashi yasa,idan banda butulci irin taki zainab ke har kina da bakin da zaki buďe ki zani wani dan yayi karuwanci?”
Kwalla ne kawai suke zubo wa zainab daga ido, gani haka yasa usman ya saketa haďe da binta da tokari, faďi tayi a kasa tasa kuka tana faďi Allah ya isa mugu kawai kuma wlhy sai Allah ya sakamin”.
Kai da gske, ashe dai wanda Allah zai saka mawa suna da yawa”..
Muguwa azuluma kawai, duk na tattara aci burin zan rakarkashi amarci nima naji abunda kowa keji a ranar daren farkonsa, ashe muguwa ta riga ta bawa wani a gama, sannan aka kawomin raguwa, wlhy sai Allah ya sakami, kuma in sha Allahu sai kin kwashi kayanki a hannu”.
Tun daga lokacin usman ya kasa zaune ya kasa tsaye a gidan su uwani, a dole sai su rage kwanakin bikin da suka yanke”.
Gani haka yasa suka rage zuwa sati mai zuwa, nan usman ya shiga gyara gida, ďakin uwani yasha gyara da fanti, har bakin kofa saida aka bisa da farin alli, bakin kofa kuma shima aka masa siminti”.
Yanzu tsakani zainab da usman, magana mai daďi baya haďasu, gani haka yasa tayi yaji zuwa gida, sai dai bayi sa’a ba, sabida koda taje hakuri rakiya ta bata tace ta koma ďakinta, domin itama yanzu ta kanta takeyi, abinda zataci niman gagaranta yakeyi, hakan yasa dole ta koma, har usman ya rufe ďaki ya kwanta yaji ana bubuga masa kofa, kamar bazai tashi ba, sabida a lokacin har ya fara bacc, jin bugun kofar yaki karewa ne yasa shi mikewa ya buďe mata kofar”.
Suna haďe ido ya kwasheta da uwar harara, ba tare suyi wa juna magana ba, suka kwanta, da safe kuwa ya shirya zai fita da sauri zainab ta mike haďe da kiran sunarsa, ba tare daya juya ba, yace lfy?”.
Zaka fita baka bani kuďi kunu safe ba”.
Kije inda kikaje jiya ba tare da kin sanar dani ba kije su baki kuďi kunun”.
Me kake nufi usman?”
Abida kunniki ya jiye maki to haka ne”.
Amma kasan idan baka bani abimcin ba Allah ba zai barka bako?”
Ehh, kamar yadda kema Allah bazai barki ba”.
Allah ya isa”.
Ma uwarki”.
Usman yana faďin haka yasa kai ya fice daga gidan”.
Kwalla kwai zainab keyi, sabida magana ma ta gagateta”.
Ranar talata aka daura auren usman da aisha, (uwani), usman baki har kunni, gidan sa kuwa, en’uwansa su cika suyi fakil, habaici kuwa ba’a magana, hakan yasa zainab ta kasa fitowa daga ďaki”.
Da dare aka kawo amarya gidan mijinta, zainab tayi kuka har ta gaji, bayan mata suka watse ango da abokansu suka shigo,(na tabbata kowa yasan irin shegantakar da akeyi, idan aka rako ango, kunga kenan ba sai na bata lokaci wajen bayanin ba)” bayan su fita ne, usman sukayi abinda ya kamata, sannan sukayi alwala haďe da sallah raka’a biyu, bayan suyi ciye-ciye da lashe-lashensu, usman ya tambayi wani game da tsarki, duk ta bashi amsa, bayan su wanke baki ne suka kwanta”.