HAUSA NOVELZYNAH Hausa Novel

ZYNAH Hausa Novel

Gani haka suma suka rungumeta suna kuka, a lokacin ne Am’abuwa ta falka, gani abinda sukeyi ne yasa ta saukowa daga kan gadon da take kwance tayo kansu, kamar a mafarki taga idon hjy a buďe, cikin kuka ta rungumeta”.

Nan bakura ya sanar wa daddy, sannan kuma yaje ya sanar wa Dr nan yazo suka canza mata drip ďin dake hannunta, kafin safe hjy har tafara magana, gani zynah yasa hjy jin kunya, domin a halin yanzu ta rasa gane abinda ya kawo zynah inda take, ita da take son gani Adyra amma kuma sai taga zynah ce ke faman aiki a kanta”.

Am’abuwa ta kira en’uwa da abokan arziki duk aka sanar masu,har da hjy Ashe, hjy Ashe najin haka ta fashe da kuka, washe gari ta isa egypt gun hjy Khursum, suna haďuwa da kuka hjy Ashe taje ta rungume hjy Khursum”.

Idan kuma koma gida nigeria kuwa, tun daga lokacin da bakura suka tafi da hjy, be sake waya da adyra ba, duk da yana zuwa nigeria duba shago, amma beyi tunanin zuwa inda take  ba, iya kacinsa gidan zynah anan zaije ya kwana, har ma ya gyata mata gida kafin ya koma, idan kuma maganar bukata ne, acan ďin ai da matarsa yake, duk da ba shine a gabansa ba, amma tsakani mata da miji sai Allah sai dai idan basu samu gu ba”.

Hakan yasa ya tattara al’amarin adyra ya zuba a gefe, dan a halin yanzu ma har mantuwa yake kamar yanada wata mata amma maganar abinda yana sawa a siye a kai mata”.

Duk da kemar bakura yana dami adyra amma a ganita zudda wa kai mutunci ne ta dau waya ta kirasa, bayan taji labari yana zuwa nugaria amma be iya zuwa ya dubi lafiyar ta ba, tunda haka ya zaba wa kansa, itama bazata kira sa, koda shekara nawa zai yi, domin tasan koda ta kirasa tasan cewa zaiyi yanada mara lafiya, to ina ruwana da rashin lafiyarta, tunda ba uwata bace, tama mutu mana”.

Daga ban garen maiduguri kuwa, kullum suke waya da ummata, haka take zama tayi ta shirya wa umma tata karya, tana bata labarin jikin hjy, ita kuma umma tata duk abinda zata faďi tana yarda, sabida a duk lokacin da zasuyi magana, kamar wata me allalmusu, duk abinda zata faďi yana zuwa iri daya da abinda daddy yake faďi masu akan hjyn”.

Kwana hjy Ashe bakwai sannan ta dawo, jiki kam sai son barka, domin a hakin yanzu hjy tana iya komai da kanta, sai dai wanda baza’a rasa ba, su zynah da bakura basu dai bata tuwan addu’a tana sha ba, duk da rashin gani Ni’eemat a gunta yana damuta,amma tunda Dr yace ta daina yawan surutu yasa tabar abin a zuciyarta”.

A lokacin da mijin Am’abuwa yake zuwa duba hjy ne, tace ta haďa kaya tabi mijinta haka, ta gode Allah yayi mata albarka ya bata masu saka mata”.

Da shike ďan albarka ne yace ya yafe mata ta zauna taci gaba da jiyar hjy har lokacin da zata samu sauki, yanzu haka ma gobe zai koma gida Nigeria’s nan suka sallama, kuďi masu yawa ya bawa Am’abuwa haďe da sallar saiya sake dawowa ďuba mai jiki”.

Ita kuwa Yah-na tunda aka kawo hjy tazo sau daya, ta tafi bata sake zuwa ba, har wannan lokacin”.

Bayan wata daya da jin saukin hjy aka sallamaesu, domin yanzu hjy ta dawo dai-dai, daddy yaso su biya germany su kara hutawa amma hjy taki, ďan haka suka kwashi kayansu gaba daya zuwa gidan Nigeria, suka inaso hjy Ashe ce da malah suka tar besu, daga airpot nan suka daukesu har gida, abinci kuwa kafin su isa hjy Ashe ta gama komai”.

Anan gidan su hjy duk suka kwata, har da su zynah, domin hjy tace su bari su huta kafin suje gida su kama aikin gyara”

Kafin 12:PM gida ya cika ďangi da abokan arziki, matan abokan hjy duk suzo gaida me jiki, basu bar gidan ba,sai bayan la’asar, hjy Asiya ce ta kai har dare, sabida mijinta amini daddy ne sosai, taso zuwa egypt duba jikin hjy, abinda ya hanata zuwa, itama ba wani isasshen lafiya ne da ita ba, hawan jini ke damuta”.

Saida sukayi sallar isha sannan suka bar gidan ita da hjy Ashe”.

Koda adyra taji labarin dawowar su hjy, bata zobs sai ďayan washe gari sannan tazo, dai-dai da isowar en’maiduguri, hakan yasa gida ya sake cika fakilll da jama’a, gani haka yasa bakira daukar zynah suka tafi gidansu”.

Masu kuka suyi masu kuma jsjsntawa duk suyi, tsakani bakura da Ni’eemat kuwa sai ido, kamar akaya ta zuba ido tana kallonsa tana jira ya gaisheta, hakan yasa shima ya zuba mata ido”.

Su hjy da daddy suna ďaki, bakura yayi sallama, a ladabce ya zauna,  sannan ya meda dubansa ga daddy yace daddy inada magana da kai, amma Allah yasa ku fahimceni”.

Daga daddy har hjy suka tattara hankalisu su bawa bakura, nan bakura ya faďi masu yadda suke zaune da Adyra, da kuma yadda sukayi da ita a lokacin da yazo daukar ta”.

Himm kawai hjy tace”.

Bayan sallar isha, lokacin duk su haďu a falo suna hira, nan hjy Khursum ta tada magana a gaban en’uwansu da sukazo daga gida msiduguri, har da kin zuwa jinyarta da tayi”.

Nan kowa yasa salati, itako mmn Adyra bata iya cewa komai ba, harrr sai da mutane daga gun sukayi shiru, sannan ta kira sunan bakura, bakura dake duke yace am’an umma”.

Idan ka cika cikin uwarka da ubanka,inaso ka saki Ni’eemat saki uku”…………..
Duk jama’an dake gun sukasa salati”.

Umma taci daga da cewa, ke kuma dan ubanki daga lokacin daya baki takarda inaso ki nimi wata uwar amma bani ba, ke harrr kin isa ki raba mana zumunci, wlhy kinyi kadan”.

Dan haka rubuta kabawa shege, take Ni’eemat tasa kuka tana faďin na duba umma, dan Allah kiyi hakuri ki yafe min”.

Mikewar da zatayi ta haye kan Ni’eemat, ta hauta da duka, anyi-anyi ta tashi daga kanta amma taki”.

Da kar aka samu ta sauka, gani bakura na zaune, beda niyyar tashi balle ya dauko paper da pen ya rubuta takarda yasa tayi kansa, da sauri aka riketa, dakar dakar aka samu ta hakuri,  saida komai ya lafa, hjy tace wa bakura ya kira mata zynah”.

Bakura na kiran zynah ta waya nan take tazo, da sallama ta shigo falon bayan su gaisa da baki ne, hjy dake zaune ta fara bayani, tanayi tana kuka, haďe da niman gafarar zynah, akan dukkani abinda ya faru a bayan”.

Babban yayi su hjy ce, tayiwa hjy faďi haďe kuma da nasifa, shi dan Adam ba abin walakantawa bane, kuma kowa da kagansa a rayuwa yanada ranarsa, to kare ma yayi rana balle ďan Adam”.

Ita dai hjy batace komai ba, idan ba kuka ba babu abinda takeyi”.

Itama zynah dake duke kuka takeyi tana fadi babu komai ns yafe maki, Allah ya yafe mana baki daya”.

Nan mmn Adyra tace wa bakura, daga yau, umarni take bashi, yadawo da Ni’eemat cikin gida su zauna tare da hjy, daga yau kuma kada hjy su sake daukar er’aiki, tunda ga Ni’eemat nan, idan kuma batayi ba, bakura ya zuba mata ido ya kyaleta har taji labarin, musamman zuwa zatayi da kanta ta hukunta shi, tunda shi ya kasa hukunta ta”.

Nan akasa dariya, masu jin zynah da wasa kuma sunayi”.

Washe gari duk suka shirya zuwa gida maiduguri, bayan tafiyarsu da sati daya, daddy da hjy sukasa bakura ya kira zynah,  sukace ta faďi duk abinda tasoke in har baifi karfinsu ba, zasuyi mata”.

Zynah tana kuka tace babu komai, ita dai dama damuwarta daya ne, ummata takeso ta dawo kusa da ita”.

Da sauri hjy da daddy sukace idan shine kada ta damu”.

Washe gari daddy yasa driver da bakura suka tafi dauko sadiya,  dai-dai lokacin rakiya ta biya wasu samari akan idan dare yayi, suzu su sawa sadiya da su hauwa wuta a daki”.

Hakan yasa rakiya tayi bakin ciki ba kaďan ba, ranar  bakura ya isa, washe gari suka dauki hanyar abuja, daga kayan sawa babu abinda sadiya ta dauka”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button