HAUSA NOVELZYNAH Hausa Novel

ZYNAH Hausa Novel

Karfe takwas suka isa abuja, zynah tayi murna sosai, a ďakin hjy suka fara sauka, saida sukayi sallah sukaci abinci, sannan hjy tace zynah taje ta gyara masu side ďin da bakura yayi samarta ka, kafin a saman masu inda zasu zauna”.

Kwana Am’abuwa biyu da dawowarsi mijinta yazo ya dauketa suka tafi gidansu, duk a cikin abuja ďin ne”.

Bayan wata daya da zuwan su sadiya abuja, Allah yayi wa Asiya rasuwa, an kwanta da ita Amma ba’a tashi da ita ba”.

Kafin sallar asuba duk aka sanar wa su hjy khursum da hjy Ashe, hjy Khursum ta dauki sadiya suka tafi tare, cikin ikon Allah itace da zynah sai wata mata dake area suka yiwa gawa wanka suka shiryata”.

Dama tun a kauye idan anyi rasuwa sadiya ake kira, tayi wa gawa wanka, sabida tanada ilimin addini sosai, hakan yasa ta koya wa zynah”.

Anayi bakwai kowa ya watse, yarage yara da babansu, babu yadda en’wan Asiya basuyi da alhj Husaini akan yabasu yara su tafi tare ba, amma yaki, dole yasa  suka bar yaran tare da babansu, da shike ba masu girma sosai bane, babbansu 15year ne da ita, sabida basu sami haihuwar da wiri ba, sai kanninta biyu,maza”.

Lokacin da zai koma bakin aiki a germany gidan su hjy ya kawo yaran, tun daga lokacin haka yakeyi, suma da shike su saba yasa basu damuwa”.

Daddy ya haďa hauwa da Fatima ya sasu makarantan su Zara’u yarinyar Asiya”.

Hjy nada wata biyu da dawowa sannan Yah-na tazo, tun daga kofar falo, hjy ta hanata shiga mata gida, babu yadda ba’a da hjy ba amma taki, har saida sadiya tasa baki, gwiwa bibiyu Yah-na ta duka mana rokon hjy gafara, ga shohon cikin dake jikinta, amma be hana hjy yi mata faďa ba, da kuma nuna mata kuskurenta”.

Tawan Asiya biyar da rasu, ranar da alhj Husaini yazo gidan su hjy, lokacin sadiya tana falo suna hira da hjy yayi sallama, tunda ya shigo idonsa ke kan sadiya, gani haka yasa tabar gun, tana fita slhj Husaini yake tambayar hjy Khursum waye ita?”

Bata boye masa komai ba, akan sadiya, alhj Husaini be tsaya su gaisa bama, balle suyi hira, ya mike ya bar gidan, yana fita ya kira daddy bayan su gaisa yake sanar wa daddy abinda ke ransa game da sadiya”.

Daddy yaji dadi hakan sosai, nan ya kora hjy ya sanar da ita, hjy Khursum batayi mamaki ba, sabida dama biri yayi kama da mutum, koda hjy ta sanar wa sadiya, sadiya bata musu sa, nan hjy ya fara zuwa zance, yara da rashin wayo, middu suga babansu yazo murna sukeyi sosai, hakan yasa koda maganar auren ya taso, ba karamin murna sukayi ba, samumman Zara’u sabida sadiya na koya mata duk wani abu daya shifi addini, alhamllh yanzu ta kara sani sosai ba kamar dah ba”.

Ita kanta zynah murna tayi sosai, bayan sati uku, ranar asabar aka daura auren sadiya da alhj Husaini, da dare su hjy Khursum da hjy Ashe suka rakata gidan alhj Husaini, kwana nan su uku da daura aure ya kwashesu zuwa germany, harda su hauwa da Fatima, haďe da nasa yaran”..

Gani pakhryya ta tafiya ko ina, yasa hjy Khursum amsarta ta yayeta, a cewarta zynah ta huta da tsotso”.

*******

Bayan wata biyar tun dare Yah-na ke nakuda, gani haka megidanta ya dauketa zuwa asibiti, nan akai ta fama, kwananta biyu tana labour daga karke har aka yanke shawarar za’ayi mata operatinon, cikin ikon Allah, saiga haihur yazo zanga-zanga idan banda kiran hjy babu abinda takeyi”.

Da kar aka samu baby ya fito, amma ta kafa, ba takai da akasan baby na fitowa ba, shi isa tashi wiya sosai, satinta ďaya sannan aka sallamesu, dole yasa aka kaita gidan su hjy, a lokacin ne ta kara sani uwa nada daraja da muhimmmanci, kara rokon hjy tayi gafara sosai”.

~~~~    ~~~~~~

_*kunci*_

Tunda rakiya ta sami labarin
Sadiya tayi aure har ma ta tsallaka tabar kasan, yasa rakiya haďiyar zuciya ta yanke jiki ta faďi, gaba daya yanzu babu abinda ke aiki a jikinta, ita da gawa babu maraba”.

Ba garen zainab da usman kafin uwani ta haihu zainab taga abu iri iri, daga gun uwani har gun usmab ďin, amma tun bayan haihuwar, hawalar da tashi, yasa gaba daya tayi sanyi da al’amarin duniya, yanzu haka koda usman ya taso zai yi mata walakancin daya saba, uwani ke hanasa”.

Bayan wata biyar Allah ya azurta zainab da ciki, yayi da rakiya kuwa ta amsa kiran ubangiji, wanda a yanzu da haka zamansa mukeyi idan lokaci yayi”.

 

****

A bangare adyra da bakura kuwa, ba karami sanyi tayi ba, hakan yasa ta roki bakura gafaran duk abinda tayi masa, shima kuma ya yafe mata”.

Zynah kuwa dama bamai matsala bace, wanda tayi masu ma su yafe mata balle ita er’kallo, dykkansu bakura ya hadsu yayi masu faďa sosai akan su haďa kai, tun daga lokacin babu me jin kansu, duk da ba gida daya suke ba”.

Bayan wata biyar Am’abuwa ta haifi er’ta mace, yayi dasu zynah da Adyra kuwa suma duk sunada ciki”.

Idan muka waiga germany kuwa, watan da alhj Husaini da sadiya sukayi aure watan ta samu cikin, hakan yasa yanzu take faman da kanta sabida cikin ya tsufa sosai har ma ta shinye watar haihuwar ”

*kunci*

Bayan wasu watanni zainab itama ta haifi ďanta baby boy, wanda yaro yaci sunan malam shehu, murna a gun usman kamar ya haďiyeta, da shike meson haihune sosai”.

Bayan sallar asuba sadiya ta tashi da nakuda, da sauri alhj Husaini ya dauketa zuwa asibiti, bata dauki lokaci suna zuwa ta haifi yara duk duk maza, daga alhj Husaini har yara sai murna, ana gobe suna suka iso gida nigeria, washe gari akasha suna, alhj Husaini be canza wa yara suna ba, haka ya barsu da sunansu”.

Tunda hauwa tazo gidan zynah, lokacin malah yazo gun bakura, yaga hauwa nan yakasa ya tsare shifa yaga matar aure, babu yadda hjynsa bata yi dashi ba, amma yaki, domin a ce warsa shima haihu yakeso, killan sanadiyar auren da zai kara matarsa zata samu ciki”.

Alhj Husaini yace yaji, amma yayi hakura saita kammala karatunta na nurse da takeyi a can germany ďin, duk da malah beji dadin hakan ba, amma yaya zaiyi dole yasa ya hakura”.

Satinsu biyu suka koma germany, idan malah yanajin ganinta binta yakeyi har can germany ďin”.

Ranar wata juma’a zynah ta tashi da nakuda, da sauri bakura ya sanar wa hjy, hjy tazo ta dauketa zuwa asibiti, yayin data haihu twist ďinta mace daya miji, ba’a suna ba adyra itama ta hauhu baby girl, hakan yasa aka haďa suna, na adyra taci sunan hjy, amma suna kiranta a *AMRAH* na zynah kuwa ba’a canza masu suna ba amma suna ana kiransu da *AZEEM DA AZEEMA”.

Bayan shekara biyu lokacin Hauwa ta kammala karatunta, suka dawo gida nigeria domin shan biki, a kunci akaje aka daura aure, sannan aka dawo abuja yin shagalin biki, wa zaiga su zainab a birni sai faman kauyanci suke zubawa, kallo kuwa kayar wacce aka wanke ma makanta” .

Duk da an gama biki amma sadiya ta hanata tafiya saida tayi kwana bakwai, sannan suka hada mata abin arziki, har da waya suka bata, sannan kuma sukace duk abinda take bukata ta kirasu ta waya, insha Allahu zasu aika mata dashi”.

Biki sa sati daya malah ya kwashi matansa zuwa America, suna su sadiya suka koma germany.

 

_Yayin da nima er’mutan zazzau nace bari na kwashi kayana zuwa zaria, tunda banida kuďin jirgi balle na bisu na jiyo maku wacce irin wainar za’a soya a America_

 

Tamman billah

 

_Alhamdulillah alhamdulillah_

*kuyi hakuri fan’s labarin ba mai yawa bane, nidai fatana, sakon da nakeso nisarwa Allah yasa ya isa gareku Ameen ngd*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button