ZYNAH Hausa Novel

Lekawa Bakura yayi, saida ya tabbata ta shige sannan ya kira zynah ta fito daga toilet, jallabiya yasa yace zo muje”.
Direct kitchen suka nufa, ta baya suka shiga, a hannnkali Bakura ya jawo kofar shiga kitchen ta cikin falo ya rufe, ta ciki sannan yace wa zynah tayi kamar tana aiki”.
To kawai tace, sannan ta fara aikin, kamar da gaske”.
Saida Bakura ya koma ďakinsa ya canza kayan jikinsa,sannan ya dawo cikin falo, dai-dai lokacin hjy na zauna, tana faman sauke kwandon masifa”.
Fuska daure, Bakura ya shigo da sallama, sannan yayi mata sannan da dawowa, bayan ya zauna ne, ya fara magana kamar da gaske, fuska daura, yace, hjy kinga batason abinda Am’abuwa takemin, idan banda rainin wayo, ta rasa inda zataje neman Amina sai side ďina?”
Me zatayi a side ďina? Yarinyar ko side ďina bata zuwa”.
Yah-na dake zaune ta kwashe masa da dariya, tana faman kai Bakura, nidai bansan abinda Amina tayi maka ba, da katsaneta wlhy”.
Bakura najin haka ya kara murkike fuska”.
Hjy dake zaune bata tanka masu ba, Yah-na dake zaune tace, to ina Amina ta shiga ne”.
Kamar bazai tanka ba, cannn kuma yace, oho, wahh yasani? Amma kun duba kitchen kuwa?”.
A lokacin ne, duk suka tuna da maganar kitchen ďin, Am’abuwa ce ta mike ta nufi hanyar kitchen, tana zuwa, hannu tasa ta murďa kofar kitchen ďin da sunar buďewa, amma sai tajishi a rufe da key”.
Dole yasa ta koma knonking, ta jima tana knonking, sannan Amina tazo ta buďe tasa kofar, gani Am’abuwa ce, yasa Amina cewa, anty sannu da dawowa, duk yadda Am’abuwa taso da tayi mata masifa, amma yanayin da Amina tayi mata ne, yasa zuciyarta saukowa daga turban data ha’u, nan dai ta shashe da tuntuni muka dawo, bamusan kina kitchen ba, sai faman niman ki mukeyi, dan mu duba ko’ina bamu ganki ba”.
Eh, ina ciki ina aiki ne”
To meyasa kika rufe kanki a kitchen?”
Murmushi Amina tayi,alamar jin kunya, sannu tace tsoro nakeji idan gidan babu kowa, sai ni kadai yasa, nake shiga kitchen na tufe kaina”.
Murmushi Am’abuwa tayi, sannan tace, ga hjy can zaune, ki kawo mata ruwa”.
Cikin zafin murya nama Amina taje ta buďe frg, ta dauko ruwan sanyi na goran faro, haďe da glass cup, nufo gun hjy, taje mikawa hjy kenan, sai tayi tutubi, faďin da goran zaiyi sai kafar hjy, duk mutani dake zaune a gun subhallh suke ambata, ita kuwa Amina take jikinta ya ya ha’u rawa, haďe da faďin dan Allah kiyi hakuri hjy,wlhy bada sa’nina bane”.
Yah-na ce dake zaune cikin harshen barbanci tace wa Amina *Afno hankali bahhh*
_means hausa babu hankali_
Shiru kawai Bakura yayi yana kallosu, Am’abuwa ce, tayi murmushi haďe da cewa Amina jeki kici gaba da aikinki, kawai”.
Ba komai ne yasa Am’abuwa tayi haka ba, sabida tasan hakan ba halin Amina bane, wannan ma kuskure ne”.
Tsaki hjy tayi, har Amina ta juya zata shige kitchen, tsawa hjy ta daka mata, tana kiranta, da sauri Amina ta juyo tazo inda hjy take zaune”.
Tunda Amina ke tafiya idonu hjy nakan Amina, gani irin kallo da jjy ke mata ne yasa Amina har tana haďa hanya, da karrr ta samu ta kariso, kusa da hjy, kan Amina na sunkuye tace gani hjy”.
Wani irin kallo hjy take wa Amina, sama da kasa, sannan tace Amina ta juya, da haka saida hjy ta kare wa Amina kallo tasss, sannan tace ta wuce”.
Amina na barin gun hjy tace, itafa tsoron Amina takeyi, domin kwata-kwata watanta takwas a garin nan,amma dubi yadda duk ta canza, ko’ina nata su bayyana daga gaba har bayanta, ko’ina su fito lubu-lubu, to gaskiya da sake, gobe daukarta zatayi zuwa suleja ta medata gidan matar data kawo mata ita”.
Duk basuso haka ba, amma babu yadda zasuyi, shiko Bakura jin haka, yasa ya fara nazarin abinda zaiyi”.
Washe gari, Amina ta kitchen tana aiki, kiran hjy ne yasa ta saki aikin da takeyi, tana zuwa gun hjyn, hjy tace jeki ki kwaso kayanki, yau zakibar gidan nan, domin medaki zanki inda kika fito”.
A sanyaye Amina taje ta kwaso kayanta,shi kuwa Bakura tunda yaji magana tafiya, ya haďa baki da driver, yace anjima zasu fita da hjy, dan Allah yanaso idan lokacin fitan yayi yace bayajin dadi”.
Koda hjy tazo akan yaje ya kaita unguwa driver yace bayajin dadi, keyadda Bakura ya uzarcesa”.
Dole yasa hjy tace Bakura yazo ya kaisu, unguwar”.
Bakura yayi haka ne,sabida yanaso yasan inda hjy zata kai Amina, domin ko lokacin da aka kawota, baya nigerin, lokacin yana waje yana karatu, dawowa kawai yayi yaga Amina a gidan”.
Bakura yana driver, hjy ce ke nuna masa hanya, sabida duk yawon da yakeyi, bai taba zuwa ta nan area ba”.
Suna isa, duk suka sauka, shiko Bakura sai faman karewa area kallo yakeyi, hjy tana meda Amina gun wacce ta kawota aikin gunta, sukai sallama ta fito ta shige mota, suka juya zuwa gida, abuja”.
Bayan komar hjy gida da kwana uku, saiga Bakura yazo suleja, gun Amina, wannan karo har cikin gida ya shiga, bayan yayi sallama kanta ta leko, gani Bakura ne, da mamaki kande tace ya shigo, har ďaki tayi masa iso, bayan su gaisa, ya kalli Amina dake zaune gefe daya, murmushi kawai yayi mata”.
Kanďe dake zaune, tana mamaki zuwan Bakura gunta, Bakura yace, hjy gunki nazo, niman wata alfarma, amma bansan yaya zaki dauki al’amarin ba”.
Nan ya zauna ya warware wa kanďe komai dake tsakaninsa da Amina, buďe bakin kanďe tace, dama biri yayi kama da mutum, sabida gaba daya naga canji a gun Amina, nasan ba karami kaya take ja ba, lalla yaro kace kaima kana waya network”.
bakura yace, yanzu abinda nakeso, shine auramin Amina zakiyi, amma banaso kowa ya sani, hatta iyayena, kada ki damu, idan maganar kuďi ne, konawa ne zai iya kashewa dan gani na mallaki Amina”.
Jin maganar kudi yasa kanďe washe baki, nan dai suka shirya, batare da tayi tunanin abinda zaije ya dawo ba”.
Washe gari da zuwa Bakura suleja, hjy ta bijiro da maganar zata aiki Bakura england gun babansa, da farko yaso yaki amincewa da tafiyar, amma da yayi wani tunani baki kawai ya washe, yana tambayar yaushe nene zai tafi”.
Hjy tace nest week, hakan yayi dai-dai da lokacin yariga ya mallaki Amina a matsayin matarsa”.
Washe gari Bakura ya koma suleja, kuďi ba dan kaďin ba, Bakura yabawa kanďe, ita kuwa Amina daukarta yayi yaje yayi mata paspot, su jima a wani guesthouse suna hira, sai aroud four sannan ya koma abuja”.
Hjy dasu Am’abuwa suna can suna nema wa, Bakura visa, shima Bakura yananan yana nema wa Amina tasa visa ďin,”.
Ranar juma’a bayan saukowa daga masallaci, aka daura auren Amina da muhammed, wato Bakura kenan”.
Ranar asabar kuwa, daya daga cikin abokansa Bakura ya tura, suleja yaje ya dauko masa Amina, yace dashi kai tsaye airpot zai wuce da ita, kuma dan Allah yanaso yayi mata komai, har izuwa lokacin shiga jirginsu, kuma dan Allah bayaso tayi nisa dashi, kuma inaso ta kasance a gabata, ko kuma bayana, idan muzo layin shiga jirgi”.
Wani irin shiga Amina tayi, cikin bskin jallabiya, haďe da nikabi, daga hannunta har zuwa kafarta duk ssnye suke da safa”.
Har su Bakura da Amina suka shiga jirgi, su hjy da Am’abuwa basu gane ba, cikin sa’a kamar suka samu gun zama daya”.
Saida jirgi ya tashi sannan Bakura yasa hannu ya buďe wa Amina fuska, da take rufe da nikab”.
Wani irin murmushi ya sakar mata, haďe da rungumarta, yana faďin amaryata, itako Amina daga daya hankalinta baya gunsa, domin daga daya hanji cikinta han wani kugi yakeyi sabida tsoro, sabida tunda Amina take a rayuwarta bata taba zato zuwa koda filin jirgi ba, balle shiga cikin jirgi”.