HAUSA NOVELZYNAH Hausa Novel

ZYNAH Hausa Novel

Jiki a sanyaye bakura ya fita, Am’abuwa dake zaune bataji dadin abinda hjy tayi wa ďan uwanta ba, Yah-na ko cewa tayi, ai wlhy hjy kinma masa kaďan da baki tsine masa ba, shegen yaro kawai, kamar bakura shine har zai aikata wannan irin aikin”.

Cikin harshen barbanci taci gaba da cewa, ki bari kawai, besan dawa yakeyi ba, kuma wlhy idan har nacika barebari sai shegiyar yarinyar ga tabar gidan nan, shi kuma ni dashi ne a gidan nan, tunda har ya’iya irin wannan aiki, ni kuma saina nuna masa kuskurensa, kuma daga yau na haramta masa cin abincin gidan nan”.

Sai kuwa hjy, wlhy bama abinci ba, duk wani abu da kikasan kinayi masa, wlhy duk ki daina, har sai ya koreta sannan kuma yazo ya duka gwiwa bibiyu ya rokeki gafara”.

Aini wlhy hjy a yadda nasanki da zafi, ban taba zaton iya hukuncin da zaki yanke wa bakura kenan ba”.

Himm kawai hjy tace, daga sannan bata sake cewa komai ba, sai faman cizon yatsa da dakeyi”.

Am’abuwa dake zaune idan ba kallonsu ba babu abinda takeyi”.

Bakura yana fita daga part ďin hjy, ďakinsa ya koma yaje ya dauki key ďin mota, restaurant yaje ya siyo masu abinci ya dawo, a lokacin da yake dawowa ne, hjy taji motsi mota, da sauri ta mike ta nufo waje, gani bakura ne a motar, tsayawa tayi har yayi parking, hannu kawai ta mika masa alama ya bata key ďin motar”.

Ba tare da musu ba ya mika mata, sannan kuma tace ya bata key ďin shagunarsa, ďaki ya koma ya kwaso key’s ďin yazo ya bata”.

Bakura na shiga ďaki yaga kular abinci, zynah take sheda masa, Am’abuwa ce ta kawo masu,  bakura yaji daďin haka sosai, na nuna kulawarta a garesa”.

Tun daga lokacin da hjy ta amshi key’s ďin shago be wani damu bakura sosai ba, coz duk abinda ya tambayi daddynsa yana turo masa shi, abinci kuma duk lokacin da Am’abuwa tayi girki tana sa masa, ba tare da hjy da Yah-na tasani ba”.

Amma ita kanta bataji daďin abinda yayi ba, da kuma abinda yayi wa hjy, nan tace yabari idan ta huce yaje ya roketa gafara” Bakura yace, in sha Allahu”.

Sati bakura daya, koda gaida hjy yayi bata amsawa, cikin side ďin ma gaba daya ta hanasa shiga, dole yasa yakoma rayuwa daga shi sai zynah”.

_*wannan shi ake kira ga koshi ga kwanan yunwa, duk daďi abu idan babu kwanciyar hankali, ba daďin sa zakaji ba*_

Gani ba zai iya zama mahaifiyarsa tana fushi dashi ba, zuwa yayi A.Y.A, gidan hjy *Ashe* ya zayyana mata komai, ďan babu abinda ya boye bata”.

Hjy Ashe tayi mamakin bakura daya iya aikata haka, sai dai a wani ban gaare kuma, taji daďi sosai dayayi tunani zuwa sanar da ita,  faďa tayi masa sosai haďe da faďi masa bai kyauta ba”.

Duk fadar da tayi masa bakura bai musu ba, domin ya amsa laifinsa, godiya sosai yayi mata sannan sukayi sallama tace zatazo gidan ta sami hjy”.

Bakura yaki sanar wa daddy sane, ba dan sabida komai ba, duk mutumin da baya tare da iyalansa, idan za’a kirasa a sanar dashi abinda ke a gida, hankalinsa sai yafi naku ku da kuke gidan tashin. Da lilin da yasa bakura bai sanar wa daddy ba kenan”.

Washe gari saiga hjy Ashe tazo, hjy khursum da murnanta ta tari hjy Ashe, kai tsaye bedroom suka nufa, waya ta dauka ta kira bakura, tace yazo ya sameta a ďakin hjy”.

Mikewa yayi haďe da daukar jallabiyarsa yasa, ina zuwa kawai yace wa zynah dake kwance”.

Kai tsaye ďakin hjy ya nufa, da sallama ya shiga, hjy Ashe ce ta amsa masa, har kasa ya duka gwiwa bibiyu ya gaida ta, bayan su gaisa hjy Ashe tace bakura ya memeta abinda yazo ya faďi mata”.

Nan bakura yasake faďin irin abinda yazo ya faďi mata”

Sannan hjy Ashe ta juya kallonta zuwa ga hjy Khursum tace kinji ko,yanzu tunda ya amsa laifinsa kiyi hakuri ki yafe masa”.

Shiruu hjy Khursum tayi tana kallonsu, ba tare da tace uffan ba, har zuwa tsawon minti goma zuwa ashirin, sannan tace yanzu sabida Allah abinda yaronga yayi ya kyauta kenan?”.

Ya rana wacce zaiyi wa ciki sai er’aiki? to a daďin me? Nan ta fashe da kuka tana faďin Allah ya gani kuma shima sheda ne, daga ni har mahaifinka bamu bata yin zina ba, shine kai zakaje ka aikata haka ko? To wlhy bari kaji, bazan taba amsar er’shege a matsayin jikata ba”.

Bakura yanaso ya sanar dasu kamar ba shege bane, amma kuma yana tsoron yadda hjy zata dauki maganar, hakan ma yaya aka kare, balle taji maganar aure” Can dai wata zuciya tace, Muhammed fito ka faďi gaskiya, kawai zaifi maka,domin boye-boye bazata amfana maka komai ba, balle ma a irin wannan lokaci”.

Cikin rawar baki yace bafa shege bane, aure mukayi”””…

Bakin hjy Khursum har yana rawa, tace auuauuauure fa kace?”

Shiru bakura yayi, kansa na kasa”.

Ba tare da sun ankara ba, daga bakura har Hjy Ashe tsalle hjy Khursum tayi sai kan bakura hannu tasa ta shakosa, itama hjy Ashe da sauri t tayi kansu tana kokarin cire wa hjy Khursum hannu a wiyar bakura, babu yadda hjy Ashe batayi da hjy Khursum akan ta sakar wa bakura wiya amma taki, sai faman cewa takeyi bari na kashesa na huta da gani abin takaici da bakin ciki”.

Kururuwan sune yasa su Yah-na da Am’abuwa suka gashi ďakin a guje, gani abinda ke faruwa ne, yasa su fashewa da kuka, suna kokarin cire wa hjy hannu a wiyar bakura”.

Da’kar suka cire mata hannu a wiyar bakura, duk a lokacin tana zaune a kanta, gani haka yasa ta koma mutsilinsa,duk inda tasamu mutsila kawai takeyi, tanayi tana babatu”.

D’akar suka samu ta sauka, tana sauka bakura ya tashi zaune, gyara rigan dake jikinsa yayi ya koma a duka a gefe, hjy Ashe tace su Yah-na su fita su basu gu”.

Nan bakura yaci gaba da bawa hjy Khursum hakuri, ta yafe masa, hada baki sukai suna bata hakuri, har ta hakura amma da sharaďi”.

Ashe tace, shawaďin me?”
Saidai ya rabu da Amina, idan kuma yace ba zai rabu da ita ba, ita kuma a maysayinta ta mahaifiyarsa bazata yafe masa ba”.

Babu irin hakirin da hjy Ashe bata bawa hjy Khursum ba, amma taki hakuri, daga kaeshe dai  cewa tayi bakura ya basu gun, bakura yana fita hjy Ashe ta gyara zama sannan tace Khursum”.

Itama juyowa tayi suna kallo juna, tace keki godewa Allah da har Allah yabashi hankalin da tunanin yin haka, ni nawa yaronfa? So nawa nake kama *Malah* da yaran aikina, idan baki sani ba to yau zan sanar dake, duk yaron da zan dauka aiki, wlhy ba sabida Allah nake sallamarsu ba, malah ke addabansu”.

Daga karke iya abu dana dauka a karshen nan, tana bacc cikin dare malah ya fada mata, Allah ya taimakeni bai riga ya shigeta ba nazo”.

Ki duba dagani har alhj bbnsu wani irin gatane, bamu nunawa yaran nan ba, kinfi kowa nasanin irin en’matan dake garin nan, amma dan jarabar duniya su rasa wanda zasuyi irin wannan har kan dasu sai yaran aikin?”

Himm Ashe kenan, ni abinda yafi bani mamaki da yaran nan kwata-kwata guda nawa suke, to yanzu fa ji abinda bakura ya ďibi, ni abinda ma yafi bani takaici, ace er’aiki”.

Er’aiki ba mutum bace?”
Haba Ashe, kamar ni ace er’aikin gidantace kuma ta koma sirikata?”

Nidai koma menene, inaso bakura yaci arzikina ki yafe masa, kuma ki bashi key’s ďin shago dana motarsa, duk da dai babu daďi, amma inda haka malah yayi ai daya fi, akan kullum ya rika faďa wa yaran jama’a, ke banda ma Allah yasa ba gida daya muke da kishiyoyina ba, kema kisan sai fata ya gagareni, sabida gori”.

Himm Ashe kenan, keta kishita kike, yanzu sabida Allah idan kawayena sukaji wannan labari mai zance dasu? er’aikifa?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button