HAUSA NOVELZYNAH Hausa Novel

ZYNAH Hausa Novel

Idan er’aiki menene to, kada ki mance rayuwar nan, ba kamar gida ba, kowa harkan gabansa yakeyi, idan ma su sani menene? Kice daga gida maiduguri aka auro ta”.

Nan dai hjy Ashe tata tausar hjy Khursum har ta hakura ta bada key’s ďin shago dana mota da kuma sharaďin Amina zatabar gida, sannan ta tafi”.

Bakura godiya yayiwa Ashe sosai, washe gari tare suka fita da zynah, gidan kanďe ya kawota, yana bayan kwana biyu zaizo ya dauketa, ita kanta zynah ďin yace kada ta faďi wa kanďe abinda ake ciki”.

Tun daga ranar da zynah tabar gida hjy ta shirya da bakura, komai yayi kai tsaye kamar yadda ya saba dah!”.

Bayan kwana biyu yasa aka nima masa gidan haya a cikin sulejan, wata unguwa da ake kira *A.P.C* quarters, ba wasu kaya ya zuba ba, sabida yasan na ďan zaman nata na ďan lokaci ne”.

Katifa kawai sukasa sai abinda baza’a rasa ba, bayan kwana biyu da tare warsu, yasa kanďe ta samo masa er’aiki, sabida tarinka taya zynah hira, itama zynah ďin waya ya bata, yace duk abinda takeso ya kirasa, yaso bata babba waya,coda chat ne, sai suyi, matsala daya ce, ba karatu tayi ba,dole yasa ya barta da karami”.

Yanzu kam hankali bakura yaďan kwanta, ba kamar dah ba,mafi yawanci lokaci koda ya sallami hjy da sunar zaije shago ba nan yake zuwa ba, gum zynah yake zuwa, susha soyayyar su, balle dama bakura irin mazan nanne masu yawan bukata”.

Ko kuma kuruciya ne, kesa shi haka oho” Domin a yadda yakejin kansa yanzu babu wanda ya kaisa jin dadi duniya”.

Ďan yasa yanzu yake sheke ayarsa da zynah, gashi zynah tada abu daya, koda kwana zaiyi a kanta bata magana, domin itama abinda takeso ne”.

Hjy tayi gudun garane ta faďi ma sago, domin yanzu irin da sukeyi, sai Allah, amma kuma, inda a cikin gida suke dole su rage wani abu, ďan ma har yanzu zynah bata gama kilewa ba, wani abin bakura ke koya mata, gani harda rashin boko ke cutarta, yasa bakura duk lokacin daya tare da ita, yana kokarin koya mata A.B.C.D, bayan ta iya, sannan ya fara koya mata two letter world three letter, da shike mai kwakwalwace, har ta iya, yanzu kam ta fara iya rubuta sunanta da nashi”.

Wani lokaci kuma idan anzo karatun, mancewa akeyi da shi a kama soyayya”.

Kullum na barawo, rana daya ta me kaya, abinda sa ido irin ta hjy, bayan bakura ya sallameta akan zaije kasuwa, yana zuwa bayan yaran shago su buďe shagon, tunda bakura yabar kasuwa, kai tsaye suleja ya nufo, gun zynah, be koma akan lokaci ba, domin duk lokacin daya tsicci kansa tare da zynah, mancr komai yakeyi”.

Bayan azahar hjy ta shirya zuwa kasuwa, tun a bakin kofa ta fara zargin bakura baya shago, bata gasganta ba saida ta shiga ciki, ganita yasa duk yaran shagon suka mike, sukazo suka gaisheta a ladabce,bayan su gaisa ne, hjy take tambayar ina bakura?”

Magana ďin shago yace, tun safe daya shigo, ya sake fita bai dawo ba har yanzu, take hjy ta juya harshe tana faďin wlhy idan har ysnzu suna tare da shegiyar yarinyar nan ne, saina bata masa rai”.

Yau da gobe ya wuci wasan yaro, ashe yaron shagon yaji abinda hjy ke faďi “.

Hjy na juyawa yace, yau ne kawai ya fara haka ko yau ne kawai?”

Daya tuno irin alkhairin da bakura keyi bamu yasa shi rufa masa asiri, yace yau ne kawai hjy”.

Ba tare data tanka masa wayar ta ta ciro daga cikin jaka ta fara kiransa, bakura yana gani kiran hjy yaji gabansa ya faďi, hjy tayi kira har sau uku amma bakura bai daga wayar ba”.

Lokacin da bakura yaga kiran hjy, lokacin yana kan network yana sending messages ne ya hanasa daga wayar”.

Tsaki kawai hjy tayi, haďe da juyawa, cikin bacin rai tabar gurin”.

Yana sauka yaje yayi wanka, yau be daďe ba kamar sauran ranaku, yana zuwa shago suka sanar mata da zuwan hjy”.

Shiruuu kawai bakura yayi yana tunanin ta ina zai fara?”

Bayan ya koma gida, yana shiga, kai tsaye falon su hjy ya nufa, lokacin suna zaune dukkansu falo, gani yadda hjy ta daure fuska yasa, yasa bakura zuwa kusa da ita ya zauna, bayan ya gaisheta fuska a daure tace, bayan shago ina kake zuwa?”

Ina ko zanje hjy bayan, shigo? Yau ma da kikazo baki sameni ba, motatane nakai gyara, sabida kwana biyun nan naji birkin motar tana rawa, yau ma wlhy dan Allah ya kiyayene” sannan kuma lokacin da kika kirani ina masallaci ina sallah, sann wayata tana slent, yasa banji kiranki ba, amma dan Allah kiyi  hakuri insha Allahu hakan bazai sake faruwa ba”.

tsakani dah da uwa sai Allah, nan hjy ta ije fushin da takeyi”.

Daga nan bakura yaci daga da gashinsa, ciki kuwa yananan yana girma, yanzu haka cikin zynah wata hudu kenan”.

*~~~~~      ~~~~~~*
*KUNCI*

Me hali baya fasa halinsa,bayan rakiya ta zubar wa zainab da wacce cikin, sai gashi taje ta sake wani,

Wannan karon ma, haka sukaje inda aka basu magana suka zuwar da wacce, cikin dare rakiya ta dauki magani batawa zainab, a cewarta kafin safe, cikin ya fita, tunda zainab tasha magani jini yake zuba mata, har asubs, rakiya bataso kowa ya sani ba, amma gani zainab nayi kamar zata mutum, yasata kiran sadiya, tazo ta taimaka mata”.

Gani irin jini dake zubowa daga jikin zainab yasa sadiya fahimtar abinda ake ciki, amma kama bakinta tayi tai shiru, tunda basu faďi mata ba, ita kuma tayi alkawarin bazata tambayesu ba”.

Hankalin malam shehu ya tashi matuka, sabida yadda yaga jini ke kwararowa daga jikin zainab”.

Babu irin tambayar da baiwa rakiya ba, amma taki faďi masa, cewa kawai takeyi, yayi hakuri ya kwantar da hankali, bataso ya yanke hukunci cikin fushi, kuma koma menene ya bari har zainab ta samu lafiya sannan sai ta faďi masa”.

Ana sanar asuba,  rakiya da sadiya suka dauki zainab zuwa asibiti, da’kar da taimakon Allah aka samu ragowar cikin ya fita, kwanata biyu, kuma duk sadiya ke kwana da ita, sannan aka sallamesu”.

Bayan kwana biyu lokacin girki ya dawo hannu rakiya, cikin dare, rakiya ta tashi zaune, tagumi tayi tayi shiruu kamar me tunanin, juyawar da malam shehu zaiyi yaji bata kusa dashi, da sauri ya mike ya zauna”.

Gani yadda tayi tagumi yasa malam shehu tambayar lafiya”.

Kai kawai ta kaďe haďe da cewa babu komai, da kar malam shehu ya lallabeta, kukan mana ficci tasa mata, tana faďin, naji zan faďi maka amma dan Allah inaso kayi min alkawarin koda na faďi maka, bazaka dauki kowani mataki a kaiba, sabida tariga ta rokeni, dana rufa mata asiri, na yafe mata, kuma kada nabari koji wannan maganar”.

Kaga idan har kata da zance, ya nuna ban rufa mata asirin ba kenan, kamar yadda nayi mata alkawari”.

Nan malam shehu yace yaji kuma ya amince, ba zai tada maganar ba”.

Nan rakiya ta kwashe karya ta shrya wa malam, har kukanta winwinwin, akan zuban jini da tayi, sariya ce, ta zuba mata guba a cikin abinci, ina fitowa bayi yana tana zubawa, koda nayi mata magana sai tace nayi hakuri na yafe mata, sannan kuma na rufa mata asiri kada na bari kaji maganar”.

Yadda take kuka sai taban tausayi, sabida yasa nace mata insha Allahu bazakaji maganar ba, to kuskuren da nayi, a lokacin ban dauki abincin na zubar ba,  sabida yadda naga tayi nadama, na dauka har cikin zuciyarta ne, ashe ba haku bane, kawai muna kwance cikin dare, naji yarinya na kukan ciki, kafin nawi wani yunkuri sai ga jini”.

Malam shehu dake zaune yace, anya kuwa, sadiya zata iya aikata hakan?.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button