ZYNAH Hausa Novel

Kodai gani kake kamar shirri nayi mata?”
Ni bance haka ba, amma lamarinne abin dubawa ne”.
Yan har kokwanton abinda sadiya zatayi kakeyi? Bayan kafi kowa sanin tun daga lokacin da Amina tabar gidan nan, sadiya ta janye jikinta bata shiga harkan kowa, to wlhy bari kaji, yadda Amina tabar gidan nan, sadiya bataki kowa ma yabar gidan ba, niba hatta kai da kanki, kuma bari kaji idan har bazaka dauki mataki akan hakan ba, ni zan dauka, domin inaji ina gani bazan zauna a kasheni ba”.
Gsni yadda ta birkice mada yasa malam shehu cewa yanzu me kikeso ayi?”
Nidai banaso a karota a gidan, domi har ga Allah tausayi take bani, idan ka koreta a gidan da wanne zataji? Ga rashin miji ga kuma rashin yarinya, girki kawai zata daina yi, tunda ta nanne take niman halakamu, idan muyi sai takawo kwanu asa mata ita da yara, idan ma magani zatasa, wannan kuma kanta zatayi wa?”.
Koda girki ya zagayo kan sadiya, tana idar da sallar la’asar ta share gindin murhu ta gyara ko’ina”.
Tana cikin kwashe sharan kenan taga rakiya tazo tana haďa icce”.
Da mamaki tace rakiya yaya haka kuma?”
Ba tare data fasa abinda takeyi ba, kuma bata ďaga ba, tace jeki ki tambayi malam da kike zamansa, amma nida amsar tambayar a nan”.
Bakin kofa ta koma ta zauna tana kallo ikon Allah, bayan isha lokacin malam yanacin abinci rakiya dake zaune kusa dashi tana yi masa fifita, sadiya tazo ta duka a gefe, bayan ta gaishesa tace dan Allah malam magana nakeso muyi dakai”.
Faďi ina jinki”.
Shiruuuuu tayi kamar bazata magana ba, amma kuma da taga baida niyyar tashi, dole yasa tayi maganar “.
Yau nice da girki, kodai mantuwa kayi?”
Ba mantuwa nayi ba, ina sane, nayi haka, kuma daga koda bakizo kin tambayi dalili ba, ni zanzo da kaina, daga yau bazaki kara dora sanwa a gidan ba, rakiya ce zata rika yin abinci, idan tayi zata zuba maki keda yaranki”.
Ido kawai sadiya tabi malam dashi, har yakare magana”.
Har ta buďe maki zatayi magana, malam shehu ya dakatar da ita, da banason jin komai, idan kuma ba haka ba, nida kece a gidan nan”.
Sadiya na kwallo ta mike zuwa ďaki, kuka sadiya tayi sosai, akan irin hukincin da malam shehu ya yanke a kanta batare da tasan dalili ba”.
Ita kuwa rakiya tun daga lokacin ta fito da sabon salo, wani lokaci koda malam bai kwanta da ita ba, idan har malam zai shiga ďakinta jansa da hira takeyi,wanda saiya dauki lokacin, bayan wasu awanni ko mintoci sai kaga ta fita da buta taje wanka, dan dai kawai ta cusa wa sadiya bakin ciki”.
Tun abin yana damu sadiya har tazo ta saba, sabida, duk da ba girki takeyi ba, amma malam shehu baya bari girkinta ya wuce ba tare daya bata hakkinta ba”.
*~~~~~~ ~~~~~~~*
_*JABI*_
Bayan wata biyu daddy ya dawo daga Germany, duk suna zaune a falo suna hira, cikin wasa da dariya, me dauka da jin dadin gani mahaifinsu, duk cikinsu babu wanda yayi tunanin sanar wa daddy abinda ake ciki”.
Da safe bayan bayan goma, duk suka shigo ďakinsa gaida sa, kamar yadda suka saba, bayan su gama gaisuwa, har su mike hjy ta dakatar da bakura, su sauran suka fita”.
Gwiwa bibiyu bakura ya duka a gaban iyayensa”.
Hjy ta meda dubanta ga alhj dake zaune cikin girmamawa ta kira sunan sa, da alhj”.
Amsawa yayi da na’am, yana kallonta”.
Kallo da yake mata ne, yasa hjy dukan ta kanta kasa, shiru tayi ta rasa ta ina zata fara masa bayani”.
Gani tayi shiru yasa alhj cewa ita sauratanki”.
Nan ta fara kame-kame, haďe da wasa da yatsun hannunta, alhj yace kiyi magana mana Khursum”.
Sannan ta fara da, da farko dai kafi na fara magana, zan fara da baka hakuri, sabida nasan duk kokarin da nakeyi akan yaran nan ba gani kakeyi ba, haka ma bai faru ba, yaya aka kare balle kuma ga wannan abinda ya faru”.
Da sauri alhj ya dakatar da ita,da cewa dakata, nine nace maki bana gani kokarin da kikeyi akan yaran nan? Kome kike nufi, kinga Khursum idan zakiyi magana kawai kiyi idan kuma bakida abin faďi to dan Allah ki tashi ki bani gun, tun kafin raina ya baci”.
Matsalar mata kenan, kana nisa ana kawarka amma kuma kana dawowa sai an bata maka rai, sabida Allah daga dawowar jiya-jiya mutum ki bata masa rai”.
A lokacin ne ta fara magana, dama wata matsalace ta taso, wannan yaron nan, wlhy yaje ya””..
Daga nan kuma ta kuma yin shiru, ta kasa karisawa”.
Bakura dake duke, jin yayi hanji cikinsa yayi wani irin kara, gabansa yayi mummunar faďuwa”.
Alhj ya ďubi bakura dake duke yace, bakura lafiya, wani abune ka aikata da har ake juyayin faďi min?”
Shiru bakura yayi, saima matsawa gefe da yayi”.
Nan dai hjy ta cire tsoron da takeji ta zaiyana wa alhj abinda bakura yayi”.
Shiruuuuu alhj yayi na ďan wasu mintoci, ido kawai ya zuba wa bakura”.
Bakura dake duke, wani irin kunya ce ta kama sa, domin ji yayi kamar kasa ya buďe ya shige, sabida kunya”.
Alhj yafi minti goma a haka sannan yace, yanzu sabida Allah abinda kayi ka kyauta mana kenan, haba-haba-haba bakura ina tarbiyanka da ilimi suke da har zakaje ka aikata irin wannan aika aika, amma kasan idan har mukayi fushi dakai bazaga dai-dai ba a rayuwar ka ko?”
Yanzu duk ďawainiyar da mukayi dakai tun kana ciki, irin sakayyar daya dace damu kenan ko? Inaso kasani duk girman da zakayi,bakafi karfin idan kayi laifi mu hukutaka ba ko?”
Yanzu abinda Allah wannan irin abin da aikata dame yayi kama? Ďan shege a gidana? Haba bakura, wlhy kwata-kwata banji dadi ba”.
Tunda daddy ya fara magana bakura baice komai ba, har saida daddy ya kare magana sannan bakura ya fara bashi hakuri, haďe da niman gafararsu, sannan kuma ya amsa laifinsa”.
Bakura yasan babu abinda keta wa daddy da hankali irin yaga kukan yaransa, hakan yasa bakura yayi amfani da wannan damar ya shaho kan daddy, kuka sosai bakura keyi, yana kuka yana rike da kafar daddy “.
Gani haka yasa daddy sa hannu ya dagosa, saida daddy ya kara yi masa faďa sosai da kuma ja masa kunnin kada ya kara, domin wlhy idan yakara, koransa zaiyi a gidan”.
Bakura yace yaji kuma ya amince, sannan daddy yace yanzu ina yarinyar take?”
Baďe bakin bakura yace hjy ce ta koreta daga gidan, yasa na medata inda aka daura mana aure”..
Aure fa kace?”.
Bakura yace eh”.
Nan daddy yace ya faďi masa gaskiya, tsakaninsa da Allah, yadda aka fara tun farko, domin bayaso a shegonta masa daya daga cikin zuri’asa”.
Nan bakura ya kwashi komai ya faďi wa daddy, sannan yace idan ma yana gani kaman karya yayi yazo suje inda aka daura auren”.
Daddy yace, da kasan aure kakeso, meyasa baka sanar dani ba?”
Shiru bakura yayi”
Daddy yace, ya shirya da la’asar ya kaisa gidan kanďe ďin”.
To kawai bakura yace, bayan bakura ya fita alhj ya faďa hjy Khursum da faďa domin yafi gani laifinta akan bakura, sabida me zata rika fita ta bar gida daga shi sai yarinyar aiki, bayan tasan idan mace da najimi suna tare na ukusu shine sheďan”.
Batayi musu ba, itama ta amsa laifinta, tunda tasan hanayi haka”.
Shima kansa bakura ďin haka ya farune, tun ranar da hjy dasu Yah-na sukaje gidan hjy Ashe, kuma tunda suka fita basu dawo ba sai dare”.
Bayan alhj ya numfasa, sannan ya take ce masa, tunda har bakura ya iya aikata masu haka, yanzu fushi da faďa ba nasu bane, tunda har ya iya shirya wa ransa abinda ransa keso, sabida haka bai isa ya hanasu abinda suma suke soba, dan haka yanzu wani aure zasuyi mata”.